Chapter 21
Chapter 21
nasa keyi a gari, ko shakka ba ya yi daga can gurin sana'ar tasa ne aka wulakanta shi irin wannan, in banda zubda mutumci da son duniya mai za'ayi da sanar cha-cha! jahili shine ya d'auke ta sana'a har yake fankama da ita, gidansa ya shiga da tunanin yanda zai tunkari ma'kocin nasa da maganar zuwan Saminu Abbatuwa sannan kuma dole ne ya nuna masa kuskuran abinda ya ke aikatawa wannan shine zaman amana a tsakaninsu. Fitowar ta kenan daga d'aki da buta a hannunta za ta kama ruwa. ya shigo gidan kamar wani 'barawo sai sand'a yake, shi kansa kunyar kansa yake tunda ya fara sanar ca-ca! bai ta'ba wulakanta irin yau ba. Ta kalleshi da mamaki a tare da ita ta ce." Mai zan gani ni Talatu?" Bai saurare ta ba ya nufi dakinsa da saurin gaske, ba ya so tayi kwakwazo har 'ya'yansa su tashi a bacci su san abinda yake faruwa. Ta ja mutsiyacin tsaki da fadin." Allah ya shirye ka Jamilu wallahi na yi nadamar auranka." ranta a 'ba ce ta shiga bandakin tana tur! da halin mijin nata. Wa she gari ya tashi zuciyarsa a 'kuntacce fargabarsa kada Saminu ya zo ya ritsa shi a gidan sai sauri yake fita. "Wai ana sallama da mai gidan." Wani ne yaro ne yake magana a gidan. Gabansa ya fad'i! wai shin ya zai yi da wannan mutumin ne? Luf yayi a d'akin bai ce komai ba yana jin lokacin da Talatu ke fadi'n." Ka ce gashi nan zuwa." Ya nemi gefan gado ya zauna yana tunanin k'aryar da zai girbawa mutumin. Ta shigo babu sallama ballanatana gaisuwa, ta ce." Ka ji ana sallama da kai a waje ko?" Ya kalle da dan firgici a tare da shi ya ce." Na ji zan fita na same shi." Ta ja dogon tsaki ta fita tana surutai, gabadaya Talatu ta raina shi, bashi da wata 'kima a idonta. Kayan sa ya sanya ya fita yana cin kunu! sai dai yanayin yanda ya samu Saminun ya firgitashi, mutumin bai ta'ba bashi tsoro ba irin yau ba! amma sai ya jajurce yayi ta ma za! hannu ya mika masa da fadin." Malam Saminu barka da asubah." Ba tare da ya amsa ba ya ce." Hujaj haka mu kayi da kai ?" Yayi shuru bai ce masa komai ba. Ya girgiza kansa yana hura 'katoton hancinsa ya ce." Lallai yau zan nuna maka asalin waye ni." Cike da burga da rashin gaskiya ya d'aga masa hannu da fadin." Ka ga Saminu ba fa za ka zo har k'ofar gidana ka fada min bakar magana ba, mai akayi akai dubu dari uku da hamsin da har za ka ishe ni da sallama wallahi na fi k'arfin haka." Ya fusata! yana numfarfashi! fuskarsa na mai'ko ido cike da kwantsa ya ce." Kai har kana da bakin wata magana anan gurin wallahi idan ba kayi wasa ba zan dau'ke ka na damfara ka da 'kasa! ni ba'a rai na min hankali." Jin abinda ya ce yasa ya d'an tsorata amma bai nuna masa a zahiri ba, ya ce.'' Na so mu fahimci jun.......Ya katse shi da fadin." Jiya na zo da daddare ban same ka sai na barwa mak'ocinka sallahu saboda haka bani da lokacin sauraran maganarka a yanzu." Wayarsa ya fito da ita "Eh gani a kofar gidansa ku 'karaso." Ya kashe wayar ya mayar da ita aljihu! Malam Habu ya fito da shirin tafiya kasuwa ya ga abinda ke shirin faruwa 'Yan sanda sun zagaye Hujaj d'aya na k'okarin d'aura masa ankwa a hannu. "Subahanallahi." Wannan kalmar ya furta yana kallonsa, kafin ya ce." Haba Saminu har an kai ga haka kuma? kayi hakuri ku fahimci juna mana.'' Ya ce." Malam Habu na dawo daga rakiyar wannan mara mutuncin bashi da gaskiya mugun mak'aryaci ne, saboda haka hukuma ce zata raba ni dashi." Hujaj ransa idan yayi dubu ya 'baci sai gumi yake ya gaza furta komai bai ta'ba tsammanin mutumin zai masa haka ba. Ya kalli yanda jama'a suka fara taruwa a gurin suna kallonsu abinda ya tsana kenan zubewar mutumci mutane na kallonsa da k'ima da mutunci amma Saminu ya ci masa mutunci a gari. Hayaniya tasa Jamila fitowa kofar gidan, can ta hange su sun tasa k'eyarsa domin tafiya ofis da shi, da sauri ta koma gidan tana shedawa Talatu abinda ke faruwa, ko a jikinta ta cigaba da sabgoginta a fili ta ce.'' Shi ya janyo wa kansa cin mutumci saboda haka babu abinda ya shafe ni shi ya siya." Yaran suka zauna jugum!-jugum! duk lalacewar sa, ba za su canza shi a matsayi a ubansu ba. Wai a kace labarin duniya ba ya 'buya har gida labari ya same ta, da yake sana'arta ta jama'a ce, duk wanda ya zauna sai ya jajanta mata wasu kuwa munafurci ne ya ke sanya su maganar. Shahida kam d'aki ta shiga ta ci kukanta ta k'oshi, ta rasa yanda za tayi da rayuwarta kunyar fitowa take saboda irin kallon da mutane ke mata dole sai sun nuna ta da tambayar Baba Asabe ita ce 'yar Hujaj wanda bai san ma shine mahaifinta ba to a ranar ya sani. *** "Ranka ya dad'e iyakar ha'kuri nayi kawai abinda na ke so ku sanya shi ya biya ni kudi na domin akwai hidima a tare dani." Officer ya ce." Saminu kaje ku yi sulhu a tsakaninku mu za mu shiga cikin al'amarin mutukar bai cika alkawarin da ya dauka ba, tunda dai ya ce yasa gidansa a kasuwa yana jira a bashi kudin a karshen wata to zamu zuba ido lokacin ya cika, idan ya sa'ba alkawari za mu shigar da 'kara kuto." Fuskar nan a murtuke! ya ce." Ranka ya dad'e aure na ke so nayi a wannan lokacin nima ina da uzuri gaskiyar magana kenan wannan mutumin ma'karyaci ne na daina yarda da maganarsa." Ya kalleshi da fadin." Saminu ni ne fa nayi alkawari cewa 'karshen wata ana bani kudin gidana zan biya ka kudin ka amma cin mutuncin da kake min ya isa haka muna gaban hukuma anyi komai a rubuce da kuma sharad'i ka kwantar da hankalinka zamu rabu lafiya insha Allahu." Ya d'an sassauta amma bai saki fuskarsa ba tana tanan kamar hadarin dake dab da zubda ruwa, ya kalli Officer din da fadin." Na amince da hakan amma ayi komai a rubuce da sanya hannuku sannan kuma a fada min ranar da zai bani kudi na domin nima na shiryawa hidimar dake gabana." Officer din ya kalleshi da fadin." Hujaj kaji bayanin Saminu yana bukatar sanin rana da kuma kwanan watan da zaka biya shi hakkinsa." Yayi jim yana nazari wannan maganar kawai dai ya shata ne ya fad'a amma babu wani dilalli da su ka yi cinikin gida dashi kawai ya fadi hakan ne saboda ya kubtar da kansa yana kuma hasashen kafin zuwan lokacin sa'a ta fad'o kansa a gurin sana'ar tasu. Ya ce." ashirin da takwas ga watan uku ya kama ranar lalata kenan insha Allahu zan biya Saminu kud'insa." Officer ya rubuta ya sanya hannu, ya mika masa shima ya sa hannu. Ya kalli Saminun dake tsaye ya sa k'aton ciki a gaba, ya ce."Kai ma kasa hannu akan wannan yarjejeniyar ni ne
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50