Chapter 42
Chapter 42
yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ 51&52 Girman gidan da tsaruwarsa ya firgitata sosai, sai ta 'kara shiga rud'ani zuciyarta ta cigaba da yi mata tunane-tunane marasa kyau! wani 'bangaran na zuciyarta na nuna mata cewa Baban- Baba mutumin arziki ne ba zai cutar da ita ba. Tafiya mai tsayi su kayi a cikin gidan domin kwalta ce a shimfid'e har sai da suka kusa kai wa karshen gidan, sannan taga yayi parking, sai ta dinga kalle-kalle a gurin, tsit! sai shuke-shuke da kukan tsintsayen dake sauka a kan ciyayi gabanta ya cigaba da fad'uwa, cikin zuciyarta take ta nanata innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! ya bud'e mata 'kofar motar, alama yayi mata ta fito da hannunsa. 'Kin fitowa tayi ido jawur! take kallonsa kafin ta bud'e baki cikin yanayin maganarta tace." Ina ne nan din.? Ya ce." Gurin da zaki zauna ne maigida ne ya ce a kawo ki nan" Sai ta kasa fahimtar inda maganarsa ta dosa. kawai dai ta zuba masa ido tana ayyanawa abubuwa da yawa aran ta. Cikin wayo da dubara ya ce." Ai yana ciki yana jiranki kamar yanda ya fad'a miki a waya." shima ya fadi maganar ne kawai! ba tare da ya san abinda ke faruwa ba. Jin abinda ya ce yasa ta d'an ji 'kwari a jikinta, ta fito daga motar, yayi mata jagora zuwa wani ke'bantaccen sashe, ya bude mata ta shiga da bisimillah a bakinta! tare da jin fad'uwa gaba a tare da ita. Tana shiga ya mayar da k'ofar ya rufe da key. ya bar gurin da saurin gaske. Shuru falon babu alamun motsi! sai dai tsaf ko'ina a tsare babu datti a ko'ina. Falo ne mai girma da kujeru masu kyau da labulaye! sai dak'in bacci guda biyu da kicin da bandaki duk a falon. a hankali ta zauna kan kujera mai cin mutum d'aya tana sake nazarin falon, gefe guda kuma zuciyarta sai bugawa take, shin ko daga ina mijin nata zai fito oho! "Yallabai komai ya kammala, yarinyar tana wannan sashen daka umarce ni dana ajiye ta." Sule ne ke wannan maganar lokacin da yake zaune a gabansa. Ya cire farin gilashin dake sakaye a idonsa ya kalleshi sosai kafin ya ce."Matata ce Shahida." Da sauri Sule ya kalle shi da dumbun mamaki a tare dashi ya ce." Matarka Yallabai?" Yayi murmushi da fadin."Kwarai kuwa a jiya nan aka daura min aure da ita, itace yarinyar mutumin nan da nasa kayi min binkice a kansa." Sule ya dinga jinjina al'amarin ya ce." Wallahi Yallabai ban gane komai ba, ita kanta yarinyar ban gane ta ba, sai dai nayi ta mamakin dalilin da yasa ka 'kebance ta a gidanka, sai na ce to ko da wani abu ne wanda kake shiryawa." Ya ce." K'warai kuwa Sule kai din yaro na ne amintacce wanda na yarda dashi, nasan cewa ba zaka mance wahalhalun da nasha a can baya ba, auren farko ban yi dace ba, na biyu ma haka, wannan dalilin yasa gabad'aya nake tsoron duk wata 'ya mace saboda kaidi da sharrinsu, da yawa 'yan uwa da abokanan arziki suna fad'in ai ba duka suke da mugun hali ba, bahaushe yace wanda maciji ya sara idan ya ga bakin tsumma dole ya razana! a cikin zuciyata na cire aure gabad'aya daga raina! sabida samun zaman lafiya na, daga baya surutai na jama'a yayi yawa a kaina cewa ba girma na bane na zauna babu aure! wannan dalilin yasa na janye kudirina, auran wannan yarinyar nayi shi ne da manufofi da yawa. saboda haka kai kad'ai ne a gidan nan kasan wannan yarinyar matata ce, akwai wani shiri da nake akan lamarin duk don na gwada ta, da tarbiyarta." numfashi ya sauke kafin ya cigaba da cewa." Matata ce, amma za ta zauna a matsayin matarka na d'an wani lokaci, ina nufin ko da wani daga cikin iyali na zai tambaye ka sai ka amsa da cewar matarka ce, shikkenan, amma babu ruwanka da zuwa sashen, sai dai idan ni na aike ka gurinta." Sule ya sauke zazzafar ajiyar zuciya, a sanyaye ya ce." To shikkenan Alhaji Allah ya sa a dace da tagari, ina yi maka fatan alheri ubangiji Allah yasa anyi kenan." Ya amsa da "Ameen ya rabbil-alamina Sule za ka iya tafiya sai na neme ka." Godiya yayi sosai kafin ya tashi ya tafi cike da mamaki a tare dashi, ko da yake bai ga laifin maigidan nasa ba, duba da cewa a can baya mata sun wahalar dashi don yayi hakan ba laifi bane. Kuka taci sosai! ganin duhu dare ya shigo gashi babu haske a falon, ko'ina yayi duhu! sai labulan tagogin dake falon ta janye haske ya shigo, hakan yasa iskar sanyi ta dinga shigowa, jikinta ya dinga kyarma! da sauri ta takure jikinta akan kujera tsoro na sake kanainaye ta, bud'e tagogin da tayi sai idanunta ya dinga yi mata gizo ta dinga ganin gilmawar abubuwa da yawa. da sauri ta je ta sauke labulayen ta koma ta zauna, babu abinda ya fi damunta irin sallar magariba da isha'i! ga yunwar da take mugun sasakarta! Jin motsi kamar ana ta'ba 'kofa ya sa gabanta ya tsananta fad'uwa! ta tsirawa kofar ido! duk da bata da tabbacin ganin fuskarsa saboda duhu amma a jikinta take jin shine zai shigo. Ya shigo da sallama ciki-ciki. ba ta ji ba amma ta ga inuwarsa. Tsaye ta mi'ke! har yanzu jikinta bai dawo daidai ba. Ya kunna hasken 'karamar wayarsa, nan ya hangeta a tsaye ta tsura masa ido, lokaci guda ya fahimci firgici da tsoro a tare da ita. Sunanta ya kira babu walwala a fuskarsa. Ta amsa cikin rawar murya. Ya ce." Zo ki kar'bi wannan ledojin kayanki ne a ciki." A sanyaye ta 'karasa kusa dashi tasa hannu ta kar'bi manyan ledejojin dake hanunsa. Bayansa ta bi ganin ya nufi d'aya daga cikin d'akunan dake falon. Ya juyo ya kalleta, babu yabo babu fallasa ya ce." Nan d'akina ne kuma ina bukatar sirri! ki d'auki wancan dakin ya zama naki." ya fada yana nuna mata d'aya dakin. Yana gama maganarsa ya bud'e ya shiga ya barta a tsaye da ledoji a hannu. Ta jima a tsaye a bakin kofar dakin tana tunane-tunane! daga bisani ta fara laluben hanya tunda ya shige dakinsa da hasken sai falon ya dawo inda yake duhu sosa! ta nemi kan kujera ta zauna ba tare da tayi tunanin shiga dakin ba, saboda tsoro take ji tana ganin gwara
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50