Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 29

Chapter 29

Majanuni Book 1 Complete Hausa Novel 1,208 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Shahida baki ta'ba shiga damuwa ta kwana da kwanaki ba irin wannan ko shakka ba nayi akansa ne." Hanci taja tana jin wani irin rashin dadi a tare da ita ta ce." Yau tsayin kwana goma kenan ban sanya shi a idona ba tun bayan korar da akayi masa daga mazauninsa shikkenan ban sake ganinsa ba, ko na je bakin kasuwar haka zan dawo gida gabad'aya ma mutane sun watsar da kayan sa a bola sai filin gurin tunda mai motar ya d'auke abar sa." Wani irin sanyi ta ji a zuciyar ta amma ba ta nuna a zahiri ba, sai ta shiga girgiza kai cikin alhini da damuwa ta ce." Ayya! Allah sarki shi yasa ashe kwana biyu na ga ba kya kai masa abinci ashe abinda ya faru kenan amma na tausayawa mutumin nan wallahi." Zuciyar ta ta 'kara yin rauni! kukan da take dannewa ya kufce! ta ce." Ni yanzu ban san ya zanyi ba zuciyata tana so ta gan shi ban san a wane hali yake ciki ba, ya kamata a taimaka masa." Kallon tausayi takewa yarinyar domin kuwa Allah ya jarabce ta da soyayya a in da bai da ce ba sai dai addua kawai. Ta ce." Ki share hawayen ki ki daina kuka insha Allahu zan taya ki da addua kuma zan sanya ayi miki saukar al'kur'ani a kan lamari idan da rabon zaku sake had'uwa sai Allah ya had'a ku a wani guri na daban." Hannunta ta ri'ke da fadin." Na gode Baba Allah ya saka miki da alkairi, insha Allahu nima zan dage da addu'a Allah ya bayyana mana shi cikin nutsuwa da kwanciyar hankali." ******* "Alhaji Sammani mai leshi wani d'an kasuwa ne wanda ya kasance abokin hurd'ar Hujaj ta 'boye! shima yana caca kuma yana samun alkairai sosai yana kasuwancin ne kawai domin kawar da hankalin jama'a daga kansa. Tarin kud'ad'an da yake bin Hujaj ba za su lissafu ba, domin dai Hujaj! gabad'aya duniya ta juya masa baya komai nasa ya tsaya cak! sai buge-buge! yake yana yawon malamai k'auyuka da zaurukan malamai ba irin wanda bai je ba domin a duba masa me yake faruwa da rayuwar sa. Kimanin miliyan biyu da rabi Alhaji Sammani yake bin sa, kuma a wannan lokacin ya bu'kaci da ya bashi kud'insa domin yin wata bu'kata! Ya rasa ina zai tsoma rayuwarsa ya yi nan yayi can fagau-fagau! ya zama wani shashasha! har ya fara surutai a hanya, shawarar da ya yanke shine sanya gidansa a kasuwa domin ya biya bashin kudin da ake bin sa! Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/K7QH4idftZS5fSw7m2Rueb *Ma su tambayar farkon littafin su yi joining domin samun damar karanta na daya* *MAJANUNI!* (The Unknown Rich Man) NA *BINTA UMAR ABBALE🍒* MANAZARTA WRITES ASSO.. _____ *Mutane masu karamci da mutunci ina godiya da adduarku tare da 'kwarin gwiwa💯❤‍🔥* _*JAMILA YUSHA'U*_ _*FAUZIYYA MU'AWIYYA*_ Tun a farkon fari muke tare. ina ro'kon Allah ya had'a fuskokinmu da alheri🙏🏻 *35&36* Lokacin da ta isa gidan baya nan, amma kuma daf yake da dawowa domin ya yi shiri na mussaman na zuwa mahad'arsu. Babu yabo babu fallasa Talatu ta karbe ta. suka gaisa sama-sama kafin ta bar ta zaune a gurun. Jamila ta shigo gidan hannunta rik'e da 'bakar ledar dake dauke da kayan miya gwalagwaji. ganin ta yasa ta washe baki da fadin." Baba ke ce a gidanmu?" Ta saki fuska da fadin." Ni ce Jamila ai na jima da zuwa ina zaune ina jiran dawowar babanku." Ta ce." Aikuwa yana kan hanya domin lokacin dawowarsa yayi." Talatu ta fito daga kicin ranta a 'bace ta harare ta da fadin." Sarkin shishshigi da cusa kai a maimakon ki kawo min aiken da nayi miki shine ki ka tsaya kina neman suna ko.?' A sanyaye ta ce." Ki yi hakuri." Tsaki taja da karfi ta fizgi ledar dake hannunta aikuwa ta ya ge kayan miyan suka watse a gurin, sai kawai ta hau d'ura mata ashar! ranta a a b'ace ta yi saurin barin gurin tana turr!! da halin mahaifiyarsu sam bata da d'abia mai kyau. Shahida ta fito tsakar gidan da alamun bacci a idonta, Jamila ce da ta shiga dakin ta tashe ta daga baccin tana sheda mata zuwan Baba Asaben. Ganinta yasa zuciyarta karyewa sai kawai ta zube a jikinta ta fashe da wani irin kuka mai sosa zuciya. Jin kuka ya cika gidan ya sanya tayi gaggawar Fitowa daga kicin da ludayin miya a hannunta nan ta iske Baban na rarrashinta da fadin." Tayi shuru ta share hawayen ta mutukar tana raye babu mahalukin da ya isa yayi mata auran dole. Karaf ta bude baki ta ce." Wannan fa ba hurumin ki bane Baba kina nema ki wuce gona da iri a akan wannan yarinyar." Ta daga mata hannu da fadin." Saurara haka kada kiyi min rashin kunya ba gurin ki na zo ba gurin mijinki na zo kuma shi nake zaman jira saboda haka kada ki kuskura ki kara wata magana a cikin wannan al'amari." Ta ja dogon tsaki tana surutai kasa-kasa ta juya ta shige kicin domin cigaba da aikin dake gabanta. A gaggauce ya shigo gidan. sai kawai yayi tozali da ita a zaune tare da yarinyar a kusa da ita, kallo daya yayi mata ya san da abinda ta zo. A tsaye ba tare da ya risina ba ya gaishe ta. itama fuska a daure ta amsa, da sauri ya nufi hanyar dakinsa sai ta dakatar dashi ya tsaya tare da soka hannuwansa a cikin aljihun rigarsa. Ta ce." Ba wani abu ne ya kawo ni gidan ka ba sai wannan yarinyar domin na zo ne na tafi da ita saboda ba zan ta'ba yarda ka cutar da ita ba." Ya ce." Kin taba ganin uban da ya cutar da abinda ya haifa?" Ta ce." Sau nawa kuma sai dai idan ba a sa son zuciya ba." Ya girgiza kai da fadin "Shikkenan Baba ni ba naso mu dinga jayayya da juna, zan baku dama da lokaci dake da yarinyar domin ni ba mutumin banza bane nayi nufin yi wa 'ya ta aure kin hana to wannan ce dama ta 'karshe a gare ku sati uku kacal ya rage bikin Hadiza kuma so nake na had'asu duka na auran, a cikin wannan satikan nakeso Shahida ta tsayar da miji idan ba ta tsayar ba wallahi tallahi zan had'a ta aure da duk wanda nayi ra'ayi. Cike da alhani da jajantawa yarinyar Tace." Wai shin Jamilu kai wane irin uba ne mara tausayi da jin kai? shin baka ganin halin da yarinyar nan take ciki ne, bata da koshin lafiya wane namiji ne a wannan zamanin zai iya da lalurarta" Ya ce." Tunaninki daban da nawa, ni a ganina duk wannan ba matsala ba ce kuma wanda zan bawa auranta zan sheda masa matsalarta cewa kurma ce to sai kuma me? tana da duk abinda da namiji yake bukata a jikin mace matsalar rashin ji ba zai ha na komai ba, saboda haka wannan shine hukuncin dana yanke." yana kai karshen maganarsa yayi gaggawar bude dakinsa ya shiga. Jiki a sanyaye suka koma gida, duk da cewa ba duka taji komai ba amma ta tsinci wasu maganganun, hawaye kawai take sharewa ta

Table of Contents

Chapters

50 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});