Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 32

Chapter 32

Majanuni Book 1 Complete Hausa Novel 1,205 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

zaki iya amincewa mu rayu a inuwa d'aya." Hannu tasa ta rufe fuskarta kunyarsa ce ta rufe ta. Ya raunata murya da fadin." Ko kina ganin nayi miki tsufa ne? ko kuma kina gudun kada 'yan uwanki da 'kawayenki su yi miki dariya."? Hannunta ta cire tana girgiza kai ta ce." A'a wallahi bana shakka kuma bana jin kunyar mutane su gan ni tare da kai! so na gaskiya nake maka, kuma wallahi zan iya rayuwar aure da kai a cikin kowane hali, ina rokon Allah ya tabbatar da alkairi a tsakaninmu." Ya amsa cike da walwala da farin ciki. Ya ce." To yanzu ya za a yi nayi magana da mahaifinki domin jibi nake so na koma bakin aiki na." Shuru tayi tana Nazari! Ya ce." Shahida akwai matsala ko?" Kanta ta d'aga murya a sanyaye ta ce." Mahaifi na yana cikin matsananciyar damuwa da rashin lafiya! gashi bama jituwa da juna kullum cikin yi min tsawa! yake tunkararsa da wannan maganar zai yi wuya domin bashi da fahimta, ita ma Baba Asabe tana da tata matsalar. Ya ce." Ko zan iya sanin matsalar.?" Shuru tayi tana jin nauyin fad'a masa! dole duk d'an halak yayi kishin iyayansa. Ya ce." Ki daina shakkar fada min damuwarki Shahida ni dake mun riga mun zama d'aya." Shuru tayi ta kasa magana. Ya d'anyi murmushi da fadin." Ki fad'a min kada kiji komai, ni mai rufa miki asiri ne a kowane yanayi." A sanyaye ta fara bashi labarin abinda yake faruwa. Shuru yayi na minti uku kafin ya ce." Ina ganin wannan ba a abun damuwa bane insha Allahu, ni zan yi iyakar bakin 'kokari na akan al'amarin ina da alfarma sosai a gurin maigida na zai nemi alfarma a gurinsa insha Allah ba za ku tozarta ba." Ta ce.'' Kudin fa suna da yawa." yayi murmushi da fadin." Ba zai gagara ba insha Allahu rabbi.'' Ta dinga kallonsa ta na tunanin yanda za ayi har a samu a biya wannan kudi masu yawa, to amma tunda ya ce Allah ya gama magana. Har 'kofar gida ya rakata suna tafe suna hira ta fahimtar juna sosai ta saki jikinta dashi, ta kuma samu sassauci a kan fargaba da tashin hankalin da take ciki. Sai dai har yanzu tana mamakin sauyawarsa. Cike da farin ciki biyu ta shiga gidan. Sai kawai ta riske su a tsaitsaye a tsakar gidan har da kawu Musa a cikinsu, da alama akwai maganar da suke. Gabanta ne ya fadi! ganin fuskokinsu babu walwala ko kad'an! Kafin ma tayi magana ya rufe ta da fada! ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba. Sai kawai ta fashe da kuka ta durkushe a gurin tana shashshe'ka! Baba Asabe ta ce." Ka kyale ta haka tunda dai Allah yasa ta dawo lafiya shikkenan magana sai ta wuce." Ya ce." Idan gidan uban nata take so ta koma ai sai ki had'a mata kayan ta, amma idan ba haka ba mai zai sanya ta dinga wahalar damu, kawai ina zaman zamana an taso ni a tsaye 'karfe goma na dare idan ba shashashan uba ba waye zai bar 'yar sa tana gantali a hanya irin haka." Ta ce." Na ce ya isa haka don Allah kada mak'ota su ji abinda yake faruwa, tunda dai ta dawo magana sai ta mutu." 'Kwafa! yayi da girgiza kai ya kalle ta da fadin." Ni zan tafi gida sai da safe." Ta ce." To Allah ya tashe mu lafiya" Ya kama hanya ya fita da takaicin abin a cikin ransa. Saliha kuwa bayan fitarsa tsaki ta ja ta shige daki tana surutai! Ya rage da ita sai Baba Asabe a tsakar gidan. Ta ce." Ai sai ki tashi kuma kukan da kike bashi da amfani domin sai da na ce miki kada kiyi dare duba da yanayin garin da kuma lalurarki idan shi Jamilun bashi da hankali to mu muna dashi" Cikin b'acin rai na yanda suke cin fuskar mahaifinta ta ce." Baba ku daina daukar alhakinsa haka don Allah." Sai ta ri'ke baki da mamaki a tare da ita ta ce." 'Karya akayi masa kenan?" Girgiza kai tayi ta ce." Tuntuni na dawo fa babu ruwan Babanmu shine ma ya ce na tashi na tafi kada dare yayi min." Ta ce." To a ina kika tsaya har goma na dare." Kai tsaye ta ce.'' Ina tare da Baban Baba." Gabanta yayi mummunan fad'uwa!" Baki na rawa ta ce'' Baban-Baba kuma?" Ta amsa da "Eh." tana kokarin tashi tsaye. Ta cigaba da cewa." Ya zo ne saboda ni, kuma mun tattauna maganganu masu muhimmanci! wallahi Baba baki ga yanda rayuwarsa ta sauya ba dama na ce miki ba mahaukaci bane." Baba Asabe jikinta yayi sanyi sosai kawai ta dinga kallonta ta gaza cewa komai, mamaki da al-ajabin al'amarin kawai take. A daran ranar dai da 'kyar Baba ta iya rintsawa tsabar fargaba da tashin hankalin da take ciki na al'amarin yarinyar da wannan mutumin da take zargin wani abu a kansa. Mamakin ta ya kara tsananta lokacin da Shahidan take sheda mata irin maganar da suka tattauna dashi. wato Maganar aure da kuma taimakawa mahaifinta da zai yi." Ta kalle ta da fadin." Shahida anya kina da hankali kuwa.? Kafin tayi magana Saliha ta kyalkyale da dariya da fadin." Ras! take tsabar iskanci ne wallahi! amma Baba ki kyale ta kawai jiki magayi ta je ta aure shi jikinta zai gaya mata." Baban ta girgiza kai da fadin." A'a Saliha ba za ayi haka da ni ba, domin yarinyar nan amana ce a hannuna ban bari ta an aura mata Saminu abbatuwa ba to kuwa ba zan bari ta auri mahaukaci ba." A hankali suke maganar dan kada ta ji." Ta kalle su ranta a masifar 'bace ta ce." Baba na san duk kokarin ki kada nasha wahala a rayuwa! wallahi nayi imani da Allah mutumin nan ba zai azabtar dani ba, yana sona ina sonsa mai zai sanya ki dinga mugun tunani akan al'amarin, ni dai mutukar kina so ki ga farin ciki na to ki amince da abinda nake so kuma ki bini da addu'a. Sai kawai tayi shuru tana kallonta gabadaya jikinta ya mutu ta rasa yanda za tayi ta kamo bakin zaran. *MAJANUNI!* (The Unknown Rich Man) NA *BINTA UMAR ABBALE🍒* MANAZARTA WRITES ASSO.. _____ WANDA BAI JI BARI BA...! 39&40 To ko da ya sanya gidan nasa a kasuwa bata canza zani ba. Domin kuwa duk dillalin da yazo domin ya duba gidan ba ya yi masa 'kima ta mutunci. duba da yanayin unguwar ta gargajiya ce. bayan haka kuma gidan irin ginin taka haye ne irin ginin 'yan kanci! duk fulastar ta zaizaye! ramuka ciki da wajan gidan, sannan kuma duka d'akuna uku ne sai tsakar gida madaidaici da kicin da band'aki. Wannan dalilin yasa gidan bai yi wani daraja ba. sai wanda yazo daga k'arshe ne ma yayi wa gidan 'kima ta mutunci ya saya miliyan daya da dubu dari biyu, amma duka na bayan sun taya ne a wula'kance! Ganin ba yanda zai yi ne ya sanya ya sallama gidan a hakan, idan ya so sai ya biya bashin miliyan d'aya tare da alkawarin cika sauran a cikin 'yan kwanaki kad'an domin akwai wasu kudi da

Table of Contents

Chapters

50 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});