Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 4

Chapter 4

Majanuni Book 1 Complete Hausa Novel 1,213 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Na gama zama dake ki tafi duk inda za kije mara mutunci." "Baba kiyi hakuri tsautsayine kin san dai tunda kike aike na banta'ba zubar miki da kudi ba wannan ma kaddara ce." Tace." Ban san kaddara ba na fada miki na gama zama dake ki tafi can gidan Ubanki duk abinda za su yi miki dama tausayi yasa nake rike dake to tunda kin zama munafuka zama na dake ya 'kare Kije duk abinda Talatu za tayi miki ba zai dameni ba. Ta durkushe a gurin tana kuka da rokonta tayi hakuri tayi kunnan uwar shegu da ita kicin ta shige ta barta a gurin, ta kalli Saliha da fadin." Ki sanya baki tayi hakuri kinji." Ko kallonta ba tayi ba ta cigaba da abinda take, A fusace! ta fito daga kicin din ta nufi dakin sai gata ta fito da bulala a hannunta ta riga ta san idan tazo babu abinda zai hana ta doke ta. dan haka da gudu ta ruga a guje ta fita daga gidan tana jin lokacin da ta sanya sakata ta koma ciki tana surutai. Babu yanda ta iya haka ta kama hanya domin tafiya gidan mahaifinta dake can Ja'in Tafiyar 'kafa za ta yi tunda babu kud'i a hannunta gashi akwai tazara mai tsayi tsakanin Gadar salga da Ja'in. Koda ta fito bakin titin hankalinta na gurin zamansa, babu shi a gurin sai tarin tarkacensa , sai ta tsinci kainta da kasa tafiya har sai da ya dawo da ledar biredi a hannunsa taga ya shige karkashin motar ya zauna. Ajiyar zuciya ta sauke cikin zuciyata Tace."Watakila wani ne ya tausaya masa ya siya masa biredin. Sai da taje Sabon titi na gidan 'kankara a kasa kafin ta samu wani d'an kirki ya taimaka mata ya rage mata hanya. *MAJANUNI!* (The Unknown Rich Man) NA *BINTA UMAR ABBALE🍒* MANAZARTA WRITES ASSO.. ____ Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/K7QH4idftZS5fSw7m2Rueb Kuyi join domin samun damar karanta littafi na d'aya. _Gaisuwa ta karamci zuwa ga iyaye na biyu._💯 *FATIMA MUSA (MOMY NIJAR)* Tare da *USAINA ABDUL-MALIK KAITA (HAJIYA BABBA)* *5&6* Ta zo shiga gidan kenan ta yi karo da 'karamar k'anwarsu Walida tana d'auke da markad'an awara a kanta. kallon juna su ka yi sai kawai yarinyar taja tsaki ta wuce ba tare da tayi mata magana ba. Idan da sabo ta riga ta saba da irin wannan wulakanci da 'kas'kancin da 'yan uwanta suke mata duk da cewa itace babba a cikinsu amma mutum d'aya ce take ganin girmanta. Gabanta na fad'uwa tayi sallama cikin gidan. Talatu tana kicin ta baza kwanuka tana rabon abinci yayin da Hadiza babbar 'yarta ke yanka musu salak da tumatur. ita kuma Jamila tana shanya kayan makarantarta akan igiya. Itace ta amsa sallamar fuska a sake tace."Auntymu kece ki ke tafe da wannan ranar.?" Hadiza ta kalleta a watse ta mayar da kanta kasa tana cigaba da gyara salak din dake gabanta. Jamila tace."Talatu ga fa Aunty Shahida tazo." Ba tare da ta juyo ba tace."To Ubanta zan yi mata kome?" Jamila ta girgiza kanta ba tace komai ba taja hannunta suka shiga daki tana 'kokarin kawar da 'bacin ran dake damunta, ta tsani halin ko in kulan da mahaifiyarsu take mata a ganinta Shahida abar tausayi ce duba da maraicin da take ciki bayan haka kuma akwai nakasu na rashin ji a tattare da ita, babban damuwa yanda mahaifinsu yayi shakulatun 'bangaro da lamarinta da kuma lalurarta a matsayinsa na mahaifinta baya taimaka mata da komai gabad'aya ya sakarwa kakarta wacce ta haifi uwarta ragamar rayuwarta, bai san ci da sha da sutturarta ba, Uwa uba karatunta duk be san wannan ba, ta wannan fanni dole a jinjinawa Baba Asabe domin ita d'in maca ce mai kamar maza duk da nauyin ba akanta yake ba amma ta d'auka tana iyakacin 'bakin 'ko:karinta akan yarinyar. Tsaf Talatu ta gama rabon abinci amma babu rabon Shahida a ciki duk da cewar lokacin da ta zo gidan bata gama rabon abincin ba idan da ta yi niyyar sanya mata kwano zata san yanda tayi ta fitar mata da rabonta amma k'emagadas! tayi mirsisi ta rabe abincin kaf ta kira kowa ya d'auki nasa. Jamila a sanyaye ta nufi dakin da nata kason a hannunta. Kamar ta san niyyarta sai ta kira sunanta, taja ta tsaya tana kallonta, fuska a tsuke tace." Ki ka shiga da abincin nan ku ka ci tare sai na tsine miki albarka." Dama sarar ta kenan daga zarar 'ya'yanta sunyi mata laifi sai tace zata tsine musu. A marairaice tace."To yanzu ita Shahidan haka zata zauna Talatu kada fa ki manta itama tana da hakki a gidan nan tunda duk ubanmu d'aya." Ta ciko hannu da shinkafa 'yar manja wacce taji salak da yaji ta watsa a bakinta tana taunawa ta ce." Kafin ki san haka na rigaki sani ban yi niyyar bata abincin ba shiyasa nayi rabo babu ita idan kuma ki kayi wasa wannan na hannun naki zan k'wace na bawa almajirai kema kiyi asara." Hadiza ta kalleta da fadin." Banza mara kishin uwarta shin har kin manta labarin da Talatu ta ba mu a lokacin da suka zauna tare da mahaifiyarta yanda ta azabtar da ita amma shine saboda rashin kamun kai kike tausayin abinda ta tafi ta bari ai wallahi ni da wannan kurmar yarinyar har abadah." Jamila ta girgiza kanta da fadin." Ke Hadiza jahilci ne yake damunki wallahi ni ina ruwana da irin zaman da su ka yi kawai 'yar uwata na sani saboda duk rintsi ba'a sanjawa towo suna Shahida 'yar uwarmu ce dole ko mun 'ki ko mun so." Hadiza ta fusata! ta hau d'ura mata ashar wai ta kira ta da jahila. 'Kokarin tashi take taje inda take tsaye ta doke ta uwar ta hana ta. Sallama ya yi cikin gidan yana sanye da manya kaya sabuwar shadda mai uban surfani, kansa sanye da hula zanna bukar idan ka ganshi sai ka dau'ka wani hamsha'kin mai kud'i ne nan kuwa tsabar 'karya ce da fafar tsiya Jamilu kenan wanda abokansa suke kiransa da Ya hajuj! tsabar 'karya da nuna shi wani ne. ya sanya sunanshi ya 'bata a ko'ina ake kiransa da Hujaj! Ya kallesu da fuskar shannu "Menene na ganku a tsaye ke Jamila ya akayi?" Da sauri tace." Baba ka ga Aunty Shahida ce tazo shine Talatu ta raba abinci babu ita wai don na d'auki nawa zamu ci tare shine fa suka had'u suke zagina. Ya gyara zaman babbar rigarshi da fadin." Ina Shahidan take? Tace."Tana daki a zaune.'' Tsaki yaja da fadin." Shige ki je kuci abincin tare." da sauri ta shige dakin. Talatu ta kalleshi da fadin.'' Yau kuma? ba tare da yace mata komai ba ya bude dakinsa ya shiga ya turo k'ofa. Kasan kafet ya zauna ya cire babbar rigar jikinsa, hannu yasa cikin aljihu ya shiga fito da kudi daure da kyaure bandir biyar ne ya zube a gabansa yana wani irin murmushi babu shakka yau kura tayi nama ya tashi da Sa'a ko da yake dama sana'ar tasu ta gaji haka yau kai gobe wanin ka da yake shi akwai nasibi duk ranar da suka buga wasa baya fad'uwa, wasan yau yafi na kullum domin

Table of Contents

Chapters

50 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});