Chapter 11
Chapter 11
taje ta shedawa Huwaila cewa Eh tabbas da gaske yake zai auri Mariya domin ma yanzu ma shirye-shiryen kawo kudin aure yake. Farin ciki ya lullubeta aikuwa ba taja dogon lokaci ba taje ta shedawa Huwaila halin da ake ciki Huwaila cike da farin ciki ta yafa mayafi domin zuwa ta shedawa Baba Asabe abinda yake wakana. Baba Asabe addua kawai tayi ta barwa Allah amma daga can 'bangaran 'yan uwan Malam Almu an dan samu matsala domin sun so su hana faruwar al'amarin mussaman da sukayi binkice suka tabbatar da munanan halin Jamilu wanda ya zama abun gudu ga ko wane managarcin mutum. Jamilu yana ganin haka sai ya shiga musu facaka da kudi lokaci guda ya toshe musu baki. Kuma ba'aja dogon lokaci ba akayi komai a ka gama. amarya ta tare a gidanta dake unguwar ja'in. Jamilu ya ga fa'idar auran Mariya domin daga sanda aka daura auransa da ita k'ofofin samu suka bude daga gareshi Allah ya albarkaci kasuwancinsa, a maimakon ya nutsu ya yi abinda zai taimaki rayuwarsa ai sai kawai ya hau shiririta da shirme, burni yake sosai ya sayi sabuwar mota kana kuma duk bayan wata biyu yake fitar da tufafinsa ya zuba wasu takalma da huluna gami da agogona kamar hauka a dakinsa, turare kam be yarda da mai arha ba mai tsada yake fesawa, Mariya tana ganin ikon Allah domin duk irin shawarar da take bashi baya dauka idan ta matsanta masa sai ya rufeta da fada da fadin kudinta ne ko nasa! Haka ta naji tana kallo ta zuba masa ido sai dai labarin duk abinda yake aikatawa a gari yana dawowa kunnanta tana da labarin yanda yake kashewa matan bariki kudi. Sosai al'amarin yake cin ranta gashi har sunyi shekara da aure amma babu labarin haihuwa ta fahimci kuma shi sam abun bai dameshi ba harkar gabansa kawai yake. Ta sameshi da maganar tana so ita dashi suje asibiti a dubasu domin a tabbatar musu da lafiyarsu. Yayi funfurus! ya ce shi babu inda za shi lafiyarsa lau don haka kada ta 'kara yi masa maganar zuwa asibiti. A ranar taci kuka ta koshi kuma yanzu ta fara nadamar auranta dashi dama wannan badakalar mahaifiyarta take guje mata, yanzu da kunya ta tunkareta da maganar domin kuwa tun farko itace ta za'bi auransa dole tayi hakurin zama da mugun halinsa. Haka ta cigaba da hakuri yau fari goma baki don ma dai yana kokari ta fannin ci da sha daba don haka ba da ba zata ganu ba. Tana kokarin warware matsalarta sai wata ta matsalar ta shigo domin kuwa mijin nata aure ya rakito ashe tuntuni har an kai kudi dasa rana bata sani ba sai ana saura kwana biyu daurin aure yazo ya ajiye mata leda viva da kayan fadar kishiya a ciki. A ranar kwanan kuka tayi ta kudiri aniyar gari na waye wa zata tafi gidansu domin kuwa ba zata iya ganin wannan ba'kin cikin ba. Yana d'akinsa yana shirin fita kasuwa ta fita daga gidan, koda ya fito yaga bata nan be wani damu ba dama yayi tsammanin faruwar haka, aure zai yi babu wanda ya isa ya hana shi. Baba Asabe ta rufe idonta tace sam! bata yarda ba don haka tayi maza ta tashi ta koma dakinta ai duk wanda ya sayi rariya ya san zata zubda ruwa don haka ita bata da gurin kwana. Haka nan tana ji tana gani ta koma gidan Jamilu koda ya dawo ya sameta a gidan, a maimakon ya rarrasheta ai sai ya tsiri gaba da ita ya dai nai mata magana har aka daura auran baya kulata. Ta sake shiga halin ni 'yasu ta ko'ina babu sassauci sai ta mayar da hankalinta gurin ibadah da ro'kon sauk:i daga rabbis-samawati. Jamilu da amaryarsa suka dinga sheka amarci ayi wanka tare aci abinci a tare sannan kullum da daddare idan ya dawo daga kasuwa ya sata a gaban mota su tafi su zaga gari ko ranar girkinta ko ba ranar girkinta ba. Amarya Hafsa ta dinga jiji da kai a gidan tana zubar da habaici ita ga matar da akeso, ita kuwa Mariya ta tattara komai ta barwa Allah ta zuba musu ido. Aikuwa tafiyar ba tayi nisa ba amarya ta samu ciki, yana fahimtar haka sai yaje ya samo mata maganin zubar da ciki ya tsaya a kanta sai da tasha. A daran ranan cikin ya zube. Taci kuka ta koshi domin ita taso ta haihu ko don tayi wa Mariya gadara da hujja. Koda ya fahimci amaryarsa tana da saurin da'ukar ciki sai ya daina kusantarta kai tsaye sai yasa kwaroron roba(condem) sannan yake auratayya da ita, Hafsa amarya ranta ya b'aci mutuka sai ta daina amincewa dashi, aikuwa be ji kunyar ci mata mutunci ba domin tsakar gida ya fito ya dinga zazzaga mata tujara da fadin." Dama lalurace tasa ya aureta ba wani gamsar dashi take ba ta dubi matarsa Mariya cikakkiyar macace me zai yi da ita idan ba kaddara ba. Hafsa ta dinga kuka tana mamakin halin d:a namiji. Ita kuwa Mariya ba tayi mamaki ba domin ta san abunda yafi haka zai iya aikatawa ita tafi kowa sanin halinsa Tun daga ranar ya mak'ale mata ya dinga rarrashinta da kalamai masu dadi har da fadin kaddarace ta sa shi aure amma me zaiyi da wata bayan yana da ita. Ita dai jinsa kawai take ta san ba komai yakewa dadin baki ba sai ni'imar da Allah yayi mata duk daran duniya baya iya hakuri sai ya kusanceta. Tsayin wata biyar haka rayuwar take tafiya Jamilu ya watsar da amaryarsa kamar bashi ya ajiyeta ba, sai kawai ta tunkareshi domin taji matsayinta, ya kalleta sama da kasa kafin yaja mugun tsaki ya ce."Wallahi ban san dalilin da yasa na aureki ba dubeki don Allah guntuwa dake hanci k'ato in banda farar fata baki da komai." Hafsa ta fusata! ta daga masa hannu da fadin." Kaga ya isa haka ka fada min matsayina a gidanka dama ai kafin na aureka sai da aka fada min halinka amma tsautsayi yasa na aureka. Ya sosa gemunsa yana mata wani irin kallo ya ce."Kwad'ayin abun duniya ne yasa kika aure ni ai tun kafin naje neman auranki na gane ke din mayyar kudi ce shiyasa na rud'eki dasu kuma na samu nasara, saboda haka yanzu baki da wani amfani a gurina kije na sakeki saki biyu." Hawaye suka k'wace mata ta ce."Sai Allah ya saka min wallahi kuma abunda kayi min sai anyi wa 'yarka." Ko a jikinsa ya rubuta mata saki a takarda ya bata harda kudi dubu biyar akan takardar, a fusace! ta watsa masa kudinsa ta fita daga d'akin tana kukan bakin ciki. *TAFIYAR TANA DA TSAYI😃* Ku karanta littafin a sannu a hankali, amma kada ku manta na fada muku cewa nayi amfani da salo biyu gurin rubuta littafin, sai a nan gaba za ku fahimta *BINTA UMAR ABBALE* Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/K7QH4idftZS5fSw7m2Rueb Ku yi Join domin samun damar karanta littafi na daya *MAJANUNI!* (The Unknown Rich Man) NA *BINTA UMAR ABBALE🍒* MANAZARTA WRITES ASSO.. _____ *13&14* Ya hujaj! bayan ya rabu da amaryarsa da wata uku sai ya hango wata 'yar dumur-dumur! mai cikar kirji
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50