Chapter 14
Chapter 14
gobe kici abinci, sannan magana ta karshe da zanyi miki shine ki iya bakinki akan zama na da Mariya kuma ki zauna lafiya da ita domin itace mahadin arziki na." Ba tace komai ba tasa hannu ta dauki kudin da ya jefa mata tana jin wani irin bakin ciki a cikin ranta. Bai bi ta tanka ba ballanantana ya duba halin da take ciki dakinsa ya shiga ya sayo k'ofar ya kashingida yana hutawa kafin dare yayi ya nufi in da yafi wayo. **** Hujaj shige da fice ya cigaba dayi tsakanin gidansu Mariya da kuma zauran malaminsa wanda yake sake tabbatar masa da cewa lallai yayi kokarin ganin Mariya ta dawo gidanshi mutukar yana so arzikinsa ya yalwata, aikuwa ya tashi hankalinsa, sai da yaga tabbutuwar auran kisan wutan da abokinsa sannan hankalinsa ya kwanta. Alhaji Sha'aibu yayi murmushi tare da godewa Allah, babu shakka dami ya tsinta a kala, babu yanda za'ayi Allah ya azurta shi da mace kamar Mariya ya rabu da ita, auransa da ita mutuwa ce kawai zata raba, dama can yana jin abokin nasa ne, bai auri Mariya dan ya sake ta ba. 'Bangaran Mariya kuwa hankalinta ya kwanta, a yanzu ne ta san tayi aure domin kulawar duniya Alhaji Sha'aibu nayi mata tare da 'yarta wacce suke kira da Shahida, ita kanta Baba Asabe sai yanzu hankalinta ya kwanta ganin yanda Alhaji Sha'aibun yake kulawa da 'yarta wannan shine babban burinta ace 'yarta tayi dace da miji nagari. Mariya tayi shar abunta tayi kyau da kiba haka nan Shahida tayi wayo rayuwarsu sukeyi mai tsafta dukkaninsu sun amince da juna babu nufin auran kisan wuta a zuciyarsu. Yana can sake da baki yana ta lissafin wa'adi (kwanaki) ya cika Abokin nasa ya cika masa alkawari kamar yanda yayi daukar masa. Bonono rufe kofa da barawo kenan. Lokacin da Hujaj ke lissafin wa'adi ita kuma Mariya ta samu ciki da Alhaji Sha'aibu. Shahida nada wata takwas a duniya Ganin yanda cikin yake wahalar da ita ne yasa Baba Asabe tazo ta dauki Shahidan ta tafi da ita can gidanta domin kula da ita, aikuwa cikin ikon Allah yarinyar tayi lafiya ta manta da nono, Baba Asabe ta cigaba da kula da ita tare da bata magungunan gargajiya. *** Sau uku kenan yana masa maganar cikar wa'adin amma yana shakulatun 'bangaro dashi, yau ne karshe dole ne ya saki Mariya ko yaso ko yaki. Koda ya isa kasuwar bai zauna a shagonsa ba, kai tsaye shagon abokin nasa ya nufa, fuskar nan tasa a murtuke. Alhaji Sha'aibu na ganinsa sai gabansa ya fadi, ya san dai labarin gizo baya wuce na koki. Babu walwala suka gaisa da juna. Ya kalleshi da fadin." Alhaji Sha'aibu ban ta'ba tsammanin cewa za kaci amanata ba wallahi yanzu haka mu kayi da kai? wata biyar fa mukayi da kai cewa za ka sakar min matata amma duba wata takwas kullum idan nayi maka magana sai kayi shuru ko kuma ka dinga raragefe, Alhaji Sha'aibu kai kanka kasan cewar yarinyar nan itace kashin arziki na mai zai sanya kayi min haka."? Hular dake saman kansa ya cire ya ajiye gefensa ya kalleshi da fadin." Alhaji Jamilu ni fa ba jahili bane ina da ilimin addini daidai gwargwado dama can ban auri Mariya dan na sake ta ba, kuma duk kudin da na baka kayi mata hidima wallahi saboda tsananin son da nake mata ne, bana bukatar komai a gurinka, 'Yarka Shahida kuma zan cigaba da daukar nauyin ta domin duk abinda Mariya ta haifa ina sonsa, babban Albishir din da zanyi maka shine Mariya na dauke da juna biyu ni ne kuma ubansa." Wani irin gumi ya dinga yanko masa! a take wuyan rigarsa ya jike jagab! bakinsa yana rawa yace." Alhaji Sha'aibu cin amanar da za kayi min kenan? sharadi mukayi da kai cewa babu mu'amular aure a tsakaninka da ita, amma me yasa za kayi min haka." Shuru yayi masa domin duk maganar da zai fada masa ya riga yayi masa bayani duk abinda zai biyo baya mai sauk'i ne. Ya girgiza kai bala'in bakin ciki kamar ya kasheshi ido jawur! ya kalleshi da fadin." Alhaji Sha'aibu idan ka san wata baka san wata ba ka mance waye Jamilu ko."? Murmushi yayi da fadin." Alhaji Jamilu duk in da zamuje fa nafika gaskiya idan hukuma za kaje ka sanar dasu, to kanka zaka tonawa asiri watakila ma alkali ya daure ka, saboda haka hakuri kawai da dangana za kayi." Yaji kamar ya dora hannu aka ya kurma ihu! saboda takaici babu shakka Alhaji Sha'aibu yayi masa bazata. 'Kwafa yayi tare da girgiza kansa ya kama hanya ya fita daga shagon yana sa'be babbar riga, duk ya zauce ya fice daga hayyacinsa, kasa zaman kasuwar yayi ya nufi zauran malaminsa duk ya zube masa abinda ya faru, Arrama ya buga kasa ya zana ya kuma zanawa ya kalleshi da fadin." Ka rabu dashi kawai na duba naga zamansa da yarinyar na 'kan'kanin lokaci ne, yanzu ka kwantar da bankalinka ka zuba masa ido kawai ka cigaba da harkokinka, akwai wasu layu da zan baka wanda zaka samu kwalba mai murfi kasa a ciki, ka jefa cikin tsohowar rijiya, sannan akwai turaran da zan baka kullum kafin ka turara jikinka sai ka kalli gabas yamma kudu arewa ka kira *Arziki har abadah! talauci kada yazo inda kake."* sai ka turara jikinka da hannayenka, ina mai tabbatar maka da cewar kai da talauci har abadah." Hujaj yayi farin ciki sosai da irin taimakon da yake samu daga gurin malaminsa, sosai yayi masa alkairi kana sukayi sallama, ya nufi gida hankalinsa a kwance yana da tabbacin cewa duk abinda malaminsa ya fada masa zai tabbata. Wannan shine abinda ya faru. Hujaj ya dauke hankalinsa gabadaya daka kan Mariya ya cigaba da fagauniyar yawan malamai domin samun sa'a ta duniya arziki kawai ko ta halin yaya. Bangaran Talatu kuwa kamar ta zuba ruwa a kasa tasha saboda farin ciki dama babban burin ta Mariya tayi nesa da ita, duk abinda yake faruwa tana da labari kuma idan taje gurin malaminta yana sake tabbatar mata da magana, wannan dalilin yasa ta kara gazgata al'amirin malamin nata, ya iya aiki kamar yankan wuka. Cikin wannan halin ta samu ciki domin sai da ta shiga ta fita ta janyo da hankalinsa kanta, kuma bata yarda ya kusance ta da k'waroron roba(conderm) **** Mariya na cigaba da samun kulawa da mijinta da kuma mahaifiyarta, cikin ikon Allah cikinta ya shiga watan haihuwarsa, sai kuma lalura tayi yawa , yau da lafiya gobe babu, ta kai ta kawo har sai asibiti suka bata gado domin kula da ita da abinda ke cikinta, Allahu akbar ashe abokin tafiya ne, daran juma'a nakuda ta tashi, kafin asubah, ta haihu 'ya mace sai da babu rai! mahaifa kuma tayi gardama likitoci suka rufu akanta domin ceto rayuwarta, duk abinda Allah ya kaddara babu makawa, suna tsaka da taimaka mata mahaifar tayi sama, a take ta dinga wani irin nishi! idonta na rufewa da wata irin jijjiga, da kalmar shahada Allah ya dauki rayuwarta. Sun shiga rudu mai tsanani mussaman mijinta da mahaifiyarta, bangaran Jamilu kuwa ko a jikinsa domin yanayin sa ma ya nuna kamar yana farin ciki da mutuwarta, domin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50