Chapter 16
Chapter 16
shiga wani kebantaccan jirgin da ya kasance na mussaman dashi da iyalinsa. Kamar yanda mane ma labarai ke bin diddinginsa nima haka ban dauke idona ba har sai dana tabbatar da cewa sun shiga jirgin sannan na janye idona, gumin dake goshina na sharce kafin na sauke wata irin ajiyar zuciya, gaskiya na jinjinawa wannan mutumin da ace duk haka masu hali suke da sun ji dadi, ya zama koda yaushe a fadi alkairinka kafin a fadi sharrinka. *Wannan kenan* ***** Takwas na dare suka kawo wutar nepa cikin unguwar wanda jama'ar dake zaune a cikinta suka cire tsammanin samun wutar sakamakon faruwar matsalar data janyo shud'ewar wattani rabonsu da samun wutar lantarki. Unguwar ta rikice da ihu! ba yara ba manya mata na cikin gida ma ihu! suke kananun yara sun fito waje sai ihu suke da fadin." *NEPA!!.* Baba Asabe dake zaune a tsakiyar rumfa tana daura man gyada irin wanda take siyarwa, tafi kowa farin ciki da samuwar wutar dalilin sana'ar ta, bata samun lokacin daure-daure sai da daddare, fuskarta da fara'a tace." Allah ya taimake mu, jama'a mai za'ayi da duhu ko a kabari Allah yayi mana tsari dashi." Saliha data fito daga uwar daki tace." Ameen dai ai Baba na fi kowa farin ciki kinga na huta wahalar kai waya ta gurin chaji." Tana maganar tana kokarin sanya wayar hannunta a chaji. Tace." Aikuwa ai yaran nan sun cutar damu wallahi ace saboda tsabar mugunta da bushewar zuciya mutum abu ba shi ya aje ba kayan gwamnati amma sai abi dare a sace ko tsoro ba sayi watarana injin wutar ya tashi dasu, kai Allah dai ya shiryi yaran yanzu." Ta amsa da "Ameen tana kokarin kunna Tv tace." Baba kin manta ai ba wannan ne na farko ba kusan sau uku 'barayi na bin dare su sace abubuwan dake da muhimmanci a transformer amma dai wannan karan naji ana cewa anyi kwamiti akwai kuma 'yan bijilanti da zasu sanya ido sosai." Tana cigaba da abinda yake gabanta tace." Ai hakan shine abinda ya dace suyi dama can rashin hadin kai ne na cikin unguwa." Shahida ce ta katse maganar da suke. rumfar ta shigo hannunta rike da plate da abinci a ciki. Can gefe ta zauna babu walwala a fuskarta, kallo guda kayi mata zaka fahimci cewar akwai abinda ke damunta. Ta kalleta da fadin." Akwai miya amma me yasa zaki sanya manja a cikin abinci, kina so wani ya shigo yaga kina cin fara da manja ya fita ya zage ni ko? dama kwana biyu naga sai nukufurci kike wai shin me akayi miki ne."? Hawaye suka fara gudana a saman fuskarta. kawai sai ta ajiye cokalin ta kifa kanta tsakanin gwiwarta tana rusa kuka." Ta bude baki kawai tana kallonta gabanta in banda faduwa babu abinda yake, rikon maraya akwai matsala babba. Saliha taja tsaki da fadin." Baba don Allah ki kyaleta ke kike rarrashinta shiyasa ai take duk iskancin da takeso idan bata bukatar zama a gidan ba sai ta hada kayanta ta tafi gidan ubanta ba." Duk da tana da matsalar kunne hakan bai hana ta jin irin kausasan maganganun da Salihan keyi a kanta ba, ta rasa me yasa Saliha bata kaunarta, tun suna yara take nuna mata kiyayya, bayan mahaifinta shine yasha nono ya bawa mahaifiyarta, amma kiyayya karara take nuna mata. Baban tace." Saliha wace irin magana ce wannan? ba na san tashin hankali da neman fitina, saboda kina ganin tana da matsalar kunne shine kike cin mutumcinta a fakaice, kin fi kowa sanin halinta, duk sanda kike kure hakurinta to zan kyaleki da it........Ta katse ta da fadin." Ki kyaleta Baba ta cigaba da maganganu a kaina jikinta ne zai yi tsami yanzu yanzu." cikin dashewar murya take magana. Baban tace." Magana dai ta wuce ke Saliha babu ruwanki da ita ki kama girmanki." Tsaki taja ta gyara wayar ta dake chaji ta tashi ta bar gurin tana kunkuni." Duk suka bi ta da kallon mamaki, Saliha sam bata da tarbiya wai a hakan ma gwara Shahidan tunda ita duk rintsi tana jin maganar kakar tasu. Gurin yayi shuru sai tv dake aiki. Kallonta tayi tana juya abincin har yanzu ta gagara saka loma daya a bakinta, da d'an 'karfi tayi maganar." Shahida sanja min tasha ki kai NTA KANO na saurari labarai." Ajiyar zuciya ta sauke ta rarrafa ta isa gurin Tv fa fara kokarin sanja tashar Tv ce irin ta da sai shuuuuuu! take mutane ma basa fita sosai, a haka suke kallon. Dai-dai lokacin da ta kai tashar NTA din yayi daidai da lokacin da aka haskoshi a filin jirgi yana gaisawa da mutane tare da cikakken bayani a kansa amma kuma da turaci ne. Murya ta karo ita da Baba Asaben suka kurawa Tv ido suna ganinshi haza-haza domin tv ba clear saboda rashin Area mai kyau. Baba Asabe tace." Shahida wannan mutumin ne mai taimakon mutane ko.? A sanyaye ta daga kai da fadin." Shine wai suna bayani a kanshi zai je aikin hajji da tare kakarsa da kuma 'yarsa tilo guda daya." Karaf tace." To bashi da mata aure ne.? Itama tace." To ina zan sani Baba nima na dan tsinci wasu abubuwan ne ba komai na fahimta a kanshi ba, amma dai gaskiya ba zai rasa matar aure ba tunda ga budurwar 'yarsa nan." Tace." Eh gaskiya kam amma kuma surutai marasa kyau suna yawo a kanshi jama'a da bin diddigi da ganin kwaf da yawa mutane nayi masa zargin auri saki wai a kalla ya auri mata sama da goma ya saki saboda yana da kudi." Ta kalleta da fadin." Baba ki iya bakinki wallahi, na lura mutane ke kawo miki gulma iri-iri kada aji wannan maganar daga bakinki babu ruwanki." 'Yar dariya tayi tace." Yo 'yar nan ai maganar duniya bata 'buya, ko na fada ko ban fada ba, idan halinsa ne, Allah zai tona masa asiri watarana." Tace." Eh duk da haka dai babu ruwanki wannan al'amari domin na san ki da magana watakila wasu na iya zuwa siyan abinci ki basu labarin da baki da tabbas akai, daga haka kuma sai al'amari ya lalace! sunanki yayi ta yawo gari." Uffan ba tace ba, saboda ta san duk maganganun Shahidan akan hanya suke, sai kawai ta cigaba da abinda ke gabanta. abincin take cusawa a bakinta tana had'iye wa da 'kyar! ita kadai ta san abinda ke damun ranta, kwana uku bata sanya shi a idonta ba, taje bakin kasuwar ya kai sau biyar bata ganin gilmawarsa, sai dai tarin tarkacensa a karkashin tsohowar motar da yake kwana, ko yana ina oho! wasu zafafan hawaye suka zubo mata a kumatu, tayi saurin gogewa! tana satar kallon in da take zaune, hada ido sukayi sai tayi saurin sunkuyar da kanta tana juya sauran abincin da ya rage da cokalin hannunta. Ta ture bokitin man gyadan da ta gama daurawa, a nutse take kallonta kafin ta d'an bud'e murya yanda za taji tace." Shahida idan baki fada min damuwarki ba waye zaki fad'awa? duk halin da kike ciki na fahimta kwana biyu kamar baki da lafiya, shin ko dai wani abu yana damunki ne."? Tasa hannu ta goge hawaye dake ta gudana a saman fuskarta, murya na rawa
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50