Chapter 37
Chapter 37
farin ciki. Babu yabo babu fallasa ta shimfida masa tabarma ya cire takalminsa ya zauna a nutse ya ke gaisata, ta amsa babu walwala a tare da ita domin dai har yanzu zuciyarta ba tayi na'am dashi ba kawai dai ta hakura ne saboda samun farin cikin yarinyar. Ita kuwa Saliha a fakaice take kallonsa tana k'unshe dariya, hular kansa da takalminsa soso da ya cire a gefanta su takewa dariya. wanda duk abinda take yana kallonta kuma yana mamakinta a zuciyarsa. Kawu Musa shi yake masa tambayoyi, cikin nutsuwa yake bashi amsa daidai da tambayar da yayi masa. Kawu Musa ya ce." To Allah ya tabbatar da alheri a cikin al'amarin. tunda ka riga kayi magana da mahaifin yarinyar ai shikkenan, dama shike iko da 'yarsa, tunda ya baka mu kuma za mu zama masu addua da fatan alheri, amma mun baka amana ka rike ta da kyau, marainiya ce bayan haka kuma ka duba lalurarta. Ya ce." Nayi alkawarin haka insha Allahu. Baba Asabe ta ce." Da zai yiwu sai ka kama haya a cikin unguwa ka ajiye ta a kusa, idan yaso ka dinga zuwa daga can abujan. Ya ce" Hakan ba zai yiwu ba Baba, ni dai buri na ku yarda dani, ku amince cewa zan rik'e amanarku, ni kuma nayi alkawari insha Allahu idan ban rik'e ba Allah ya hukunta ni". Ta ce." To ai shikkenan Allah ya sa mu dace amin." Gabadaya suka amsa da "Ameen ameen." Da zai tafi ya ajiye mata dari biyar, ta ce."A'a zo ka dauki kudinka bawan Allah ka 'kara guziri, kai da za kayi tafiya" Yayi sauri yasa takalmansa ya kama hanyar fita Shahidan ta bi bayansa da sauri. 'Yar 'karamar waya tacno ya bata ya ce ta ri'ke zai dinga turo mata sak'on gaisuwa, saboda ya san lalurarta, ta kar'ba ta na godiya sai murmushi take ganin yanda aka samu daidaito ta kowane b'angare! a yanzu burinta bai wuce ace sun mallaki juna ba. **** "Eh ni ne Alhaji Sammani mai leshi kasuwar wambai.'' Ya fad'a yana gyara wayar a kunnansa. Daga daya 'bangar ya ce." Ma sha Allah. dama na kira ne akan maganarka da Abokinka Jamilu Hujaj." Ya ce." Eh hakane to ina sauraranka, Allah yasa alheri ne. Murmushi yayi a nutse ya ce." Alheri ne insha Allahu." Yayi shuru na second daya kafin ya ce." Nawa ne sauran kud'in naka ne?" Cike da karsashi da kwarin gwiwa ya ce." Ba saura bane ai domin a miliyan biyu da rabi an bada miliyan daya ka ga kuwa ya wuce saura." Ya ce." 'Kwarai kuwa, yanzu idan na fahimta cewa kudinka da suka rage a hannun abokinka Miliyan daya da rabi kenan?" Ya ce." 'Kwarai kuwa." ya fada yana gyara tsayuwarsa a cikin shagon. Ya ce" Babu matsala ka tura min account number zan sa maka insha Allahu." Mamaki ya rufe shi! ya bud'e baki kenan zai yi magana sai ya ji wayar ta tsinke! ya dinga kallon fuskarsa wayar yana mamakin in da Alhaji Jamilu ya samu wannan hanyar, shin waye wannan mutumin? amma bari ya tura account din ya gani, domin bai gama amincewa da maganar mutumin ba, ya na so ya tabbatar ne kawai. Ko minti biyar bai yi da tura account d'in ba ya ji alert kudi sun shigo, yana dubawa ya ga kud'insa cif miliyan biyu da rabi! Cikin tsantsar mamaki! ya nemi guri ya zauna jikinsa sai kyarma yake dama Jamilu ya sha sheda masa cewa shi ba 'karamin mutum bane. Text ne ya shigo wayarsa ya bude yana dubawa. Sai jikinsa ya 'kara mutuwa karanta abinda yake k'unshe. _"Ga kud'inka nan Alhaji, ka mayar masa da miliyan dayan da ya baka Allah ya kiyaye faruwar hakan anan gaba."_ Hannu na rawa ya fara kokarin kiran wayar sai dai sai kash a kashe take, ya kira ya kai sau bakwai bata shiga ba, sai ya hakura ya fara laluben lambar abokin nasa domin fada masa halin da ake ciki. " Na san da hakan, domin kafin a tura maka kudink'a sai da aka sheda min, Yau ka tabbatar da cewa ni din ba 'karamin mutum bane ko?" ya fada cike da izzah da ginshera! Alhaji Sammani ya ce." Wai don Allah ina ka samo wannan mutumin domin daga jin muryarsa bai yi kama da abokanan hurd'ar mu ba." Murmushi yayi kafin ya ce." Haihuwa ce tayi min rana saboda haka mu bar maganar kawai, kai kayi nufin tozarta ni Allah bai nufa, sai ka tura min abinda yayi saura nawa dake hannunka, daga haka ala'karmu ta yanke." Ya na gama maganarsa ya kashe wayar yana jan tsaki, account number ya tura masa yana jiran ya ji alert. Cike da kwarin gwiwa ya fito daga d'akinsa! ya bankad'a labulan dakin yana kiran sunanta. Ba ta amsa ba sai ido kawai da ta zuba masa. Ya ja mugun tsaki kafin ya ce." Na yarda ke ce ki ka karya ni, ba tun yau ba malamina ke sheda min hakan, rabon wad'annan yaran nake zaune dake, amma ki sani, Mariya ta fiye min ke duk da bata raye ina alfahari da ita, domin ta haifa min yarinyar da ta share min hawaye, ba zan ga ji da sheda miki cewa ke da yaranki baku da amfani a guri na ba." Yana gama maganarsa ya saki labulan ya kama hanya yayi ficewarsa zuciyarsa fes! gabadaya duk wani damuwa da lalure-lalure da yake sun tafi sakamakon shigowar kud'i, a maimakon ya je ya mayar wa da dillali kudin ya bashi takardar gidansa, kawai sai ya cigaba da fantamawa da kud'in, ya gwammace ya zauna a matsayin d'an haya a gidan, domin zuwa yayi ya bashi kudin hayar shekara biyu dubu dari biyu da ashirin, yasa abinda ya rage a aljihunsa ya cigaba da buga barikinsa. Baba Asabe tayi-tayi dashi kan cewa a je ayi binkice a can garin nasu amma fafur! ya'ki a lokacin har ya so yayi mata rashin kunya! Kawu Musa ya ce kawai ta kyaleshi kamar yanda ya fad'a mata cewa uwarsa da ubansa ne kawai za su fad'a masa magana ya ji akan wannan al'amari to tunda basa raye babu wanda ya isa domin dai yarinya 'yarsa ce shi yake da iko da ita! Baba Asabe har kuka tayi saboda tsabar 'bacin rai tana jin takaicin abinda mutumin yake mata, wato ita ta gama yi masa wahala yana nuna mata iko. kawai sai ta barwa Allah al'amarin, ta tsananta da addua. 'Bangaran masoyan kuwa sun sha'ku sosai ta waya domin kalaman soyayya suke aikawa da junansu babu dare babu rana. Ranar juma'a 20/3/2021 aka d'aura auran, babu laifi d'aurin auran ya tara mutane, amma duk yawancinsu mutanan Hujaj din ne, sai wakilan ango guda biyu da suka bada sadaki, kuma suka kar'bi auran bisa yarjewar addinin musulunci. *Littafi na daya yana daf da 'karewa, ina fatan masoya za ku goya mini baya gurin sayan littafi na biyu domin cigaba da tafiyar tare. hanyar da za a biya kudin mai sauki ce Normal group #500 Vip group posting sau biyu a rana 1k za a tura kudin ta wannan asusun. 0542382124...Binta umar gtbank. idan kati za a tura sai ayi mini magana ta WhatsApp 07084653262. mutanan Nijar za ku tura dala dari
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50