Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 3

Chapter 3

Majanuni Book 1 Complete Hausa Novel 1,214 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

kaina na duba kudina yau koni ko shi duk haukansa wallahi na fi shi sai ya fito min da kudina 'barawo kawai " Tsaye ya mike tare da zaro kudi daga aljihunsa ya mika mata da fadin." To ni dai ga kudinki zan shiga gida na huta zuwa yamma zan shigo domin naji a'ina aka kwana.'' Kudin ta kar'ba tasa cikin lalitar dake d'aure a kugunta da sauri ta shiga daki ta fito yafe da mayafi. Saliha ta kalleta da fadin." Baba kada kije ki tunkari mahaukacin mutumin nan kada garin neman gira a rasa ido ni dai na fada miki. "Sai naje d'in ba zan lamunci wannan al'amarin ba domin kuwa ban yarda da asara ba." Tana 'kare maganarta cikin zafin nama ta kama hanyar fita da kud'irin zuwa yiwa Baban Baba A tare a tare. Tunda ta hango ta gabanta yake faduwa sunkuyar da kai tayi har ta k'araso inda take, "Don ubanki abinda ki kayi min kenan? ta fad'a tana kokarin kai mata duka! tasa hannu ta kare tana kallonta da idanuwanta da suka taru da ruwan hawaye. cikin masifa ta ce."Tashi muje gurin mahaukacin daya sace min kudina." Cikin k'okarin kare kanta ta bude baki za tayi magana.......ta buga mata tsawa! wacce ta sanya babu shiri ta mike tabi bayanta tana me cigaba da aibata ubanta wanda bai san abinda yake faruwa ba. Har suka isa bakin titin tana surutai! jama'arta sai tambayarta suke abinda ke faruwa tana tafe tana basu amsa wasu dariya kawai suke su wuce wasu kuwa bin bayanta suke domin kashe kwarkwatar idonsu. Yana tsaye da wata jarka a hannunsa da alama gurin yake so ya bari, katamau! ta rike hannunta suka 'karasa gurin da yake. Tsira musu ido yayi yana kallo. ta kalleshi da niyyar yi masa tijara! dafin idanuwansa ya sanya jikinta mutuwa sai ta gaza furta komai kawai tayi 'kasa da kanta. Kallon yarinyar ya yi suka hada ido da ido, sai tayi gaggawar saukar da nata idon sakamakon mutuwa da jikinta ya yi a cikin k'wayar idonshi akwai wani sirri wanda shi kanshi bai san yana dashi ba. Can 'kasan ma'koshi ya ce." Menene ko za ku duba kudin ne?" Kai kawai ta iya d'agawa har yanzu kanta na kasa ta kasa kallonshi, Baba Asabe tayi namijin kokari gurin Fad'in." Kaga Malam dakata! ba mu yarda da cewa kai mahaukaci bane kazo cikin wannan unguwa ne da mummunar manufa don haka kud'ina dubu arba'in da hudu daka sace wallahi sai ka fito dasu ko kuma ka kwana a police station." Ya zuba mata kyawawan idanuwansa masu cike da kwarjini. Dalladi dake bayansu a tsaye yace."Uwar towo wannan magana ki barta kawai ko kin ta'ba ganin anyi sharia da mahaukaci ni na tabbata da cewa Baban-baba ba zai sace miki kudi ba, to yayi me da su? mutumin da ba shi da hankali idan kuma baki yarda ba sai ki dauki mataki amma ina mai tabbatar miki da cewa wahala zaki sha domin kuwa duk inda za ki je babu wanda zai saurareki. Ta girgiza kai nifa ba zan yarda ba wallahi." Yace."Shikkenan sai kiyi abinda za kiyi." Gurin ya bari bayan ya gama maganarsa, sai kawai ta hankad'a yarinyar kusa dashi da fad'in "Maza shiga k'arkashin motar ki duba min kud'ina idan zai kashe ki da duka bai dameni ba." Ba tare da wata fargaba ba ta shige k'arkashin motar ta fara dube-dube duk da tasan kudin basa gurin. Kallonsa tayi da fad'in." 'Yan sanda zan dauko maka yanzu ai gamu ga police station haukanka na 'karya ne" Cikin sauri ta bar gurin. Yana tsaye ya rungume kirjinsa da hannuwansa idanuwansa a kanta a lokacin da take karkashin tsohowar motar tana dube-dube. Jikinta ya jik'e da gumi ta fito daga 'kasan motar da 'karfi tace."Baba banga 'kudin b........Had'a ido sukayi yana kallonta jiki a sanyaye tace."Babu kudin a gurin." Kai ya gyad'a mata. sai ta matsa ta bashi guri ganin yana kokarin ture ta, ya shiga ya zauna tare da rungume gwiwarsa still idanuwansa na tsaye a kanta. Baba Asabe Cike da kwarin gwiwa ta isa station din duk ta zayyane musu abinda yake faruwa. Koda sukaji abinda take tafe dashi sai suka shashantar da maganar saboda sun riga sun san sharia da mahaukaci sai wanda ya shirya bayan haka kuma duk tsayin watannin da mahaukacin yayi a unguwar ba'a ta'ba kawo musu shi da sunan ya aikata mummunan aiki ba. saboda haka sai suka sallameta tare da kafa mata hujja da cewa ko don gaba ta daina cewa za ta yi sharia da mahaukaci domin kuwa al'kalami ya sauka daga kan duk wani mai matsalar k'wakwalwa. Jiki a sanyaye ta fito daga station din ranta duk a bace! tana tafe tana zancan zucci da irin hukuncin da za tayi wa yarinyar. Ita kuwa Shahida tana nan tsaye a gurin gabanta sai faduwa yake ta san halin Baba Asabe akan kudi babu shakka yau sai buzunta. A jikinta take jin yana kallonta amma tsabar fargaba ta kasa juyawa ta kalleshi ta fahimci a cikin haukan nasa harda kallo a ciki to idan ba haka ba menene abin kallo a tare da ita. Ya jima yana kallonta kafin ya sauke zazzafar ajiyar zuciya hannunshi yasa ya ja gefan hijab dinta. Cikin wani irin yanayi ta juya suka hada ido. muryarsa ya daga sosai da fadin." Wacece ita?" Zuciyarta ta karye hawayen da take ta tattalinsu suka su'bce. A raunane tace."Kakata ce." "Ina iyayenki?" ya fad'a still idonsa na kanta, kai ta sunkuyar jin tana shirin fashewa da kuka, ya sake maimaita maganarsa. Murya na rawa ta ce." Mahaifiyata ta mutu Babana kuma yana can unguwar Ja'in da matarsa da sauran 'yan uwana." Zama ya yi ba tare da ya sake magana ba. A sace ta d'an Kalleshi da gefen idonta, al'amarinshi akwai abun mamaki a ciki maganarsa cikin nutsuwa babu alamun ta'bin hankali a ciki ko dai akwai wani abu da yake 'boyewa ne? gashi ba yaro bane da shekarunsa yanda take ganinsa ma kamar zai yi shekarun mahaifinta, Kallonsa ta sake yi taga ya rungume gwiwarsa da hannuwa biyu yana girgiza kansa can kuma sai taga yana 'yar dariya. Cikin faduwar gaba Ta ce." Baban-Baba kana jin yunwa ko?" Ba tare da ya kalleta ba ya daga kanshi. Ta ce." Yanzu a ina zaka samu abinci?" Ya kalleta na second biyu kafin ya kauda kansa. Wata maganar take shirin yi masa ta hango Baba Asabe ta tsallaka titi, ya kalleta cikin tsawa yace."Ki tafi ki bani guri." da sauri taja gefe tana kallonsa, ya dauki iccen dake gabansa yana nuna ta dashi. "Na ce dake ki tafi ki bani guri ko ba kya ji ne? Saurin barin gurin tayi tana waiwayensa. Sai girgiza kansa yake tare da wasa da iccen dake hannunsa, Hawayen tausayinsa ta goge tana tunanin a inda zai samu abinci ya ci watakila kan bola zai je ya yi tone-tone ya samu lalataccen abinci ya ci tunda mafi akasari da haka mahaukata 'yan uwansa suke kawar da yunwar da ta damesu. A soran gidan ta samu ghana masgo kayanta kaf a ciki. Ta dinga jin masifarta daga gidan Saliha na taya ta. Jiki a sanyaye ta shiga da sallama a bakinta, ta kalleta da fadin."

Table of Contents

Chapters

50 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});