Chapter 38
Chapter 38
Vip jakka daya katin airtel za ku turo min dashi ta lambata. Allah ya yassare* Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/K7QH4idftZS5fSw7m2Rueb *MAJANUNI!* (The Unknown Rich Man) NA *BINTA UMAR ABBALE🍒* MANAZARTA WRITES ASSO.. _____ *AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE🌳* _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ 45&46 "Wai ana sallama da Shahida." Yaron ya fad'a yana wasa da garegaran dake hannunsa. Saliha dake zaune a tsakar gidan tana kula da masu shige da fice domin sayan abinci ta hararin yaron tana shirin magana sai ga Shahidan ta fito daga daki. Sai tayi shuru tana yi mata wani mugun kallo. Yaron ya ce." Yawwa Shahida ki zo ana kiran ki a waje." Da dan 'karfi yayi maganar. saboda ya san lalurarta. Da sauri ta ce." Ka je ka ce gani nan zuwa." Yaron ya juya ya fita cike da wasa a tare dashi. Dama tayi wankata tsaf ta shirya cikin atamfah mai sauki kudin, sai kawai ta fesa turare mai dadin 'kamshi ta sa hijabi a jikinta, ta fito cike da farin ciki a tare da ita. Saliha ta bi ta da harara da fadin." Shashasha! mara hankali kawai." Yana tsaye a soron gidan ya shirya babu laifi doguwar jallabiya ce a jikinsa ruwan madara amma ta kod'e sosai, da ba'kar hula mai raga-raga a kansa, kafarsa sanye da takalmi d'an madina kore sai hannunsa dake makale da carbi mai madannai! yayi mata kyau sosai, ta tsuguna har 'kasa tana gaishe shi. Ya amsa yana mata wani irin duba mai tattare da abubuwa da yawa. Cikin nutsuwa ya ce." Ki tashi mana." Ta mi'ke tsaye tana murmushi, a hankali ta ce." Yau kafi koda yaushe kyau." Murmushin farin ciki yayi ya ce." Na gode sosai Gimbiyata." Tana wasa da yatsun hannunta ta ce." Baba Asabe ta je unguwa ya za ayi kenan?" Ya ce." Hakan ba matsala ba ce idan babu damuwa sai mu je can gidan naku nayi magana da mahaifinki." Ta ce." Shikkenan hakan yayi." Suna fitowa kofar gidan. adaidaita sahu yana sauke Baba Asabe da 'katon buhun shinkafarta. Ta fito da kudi ta bawa direban da fadin." Don Allah ka taimaka ka shigar min dashi gida." Ya ce."To babu matsala Baba." Tana juyowa ta gan su a tsaye. Gabanta yayi mummunar fad'uwa! Wani irin kallo take musu fuskarta babu annuri ko kadan. A sanyaye ta ce."Baba sannu da zuwa." A dakile ta amsa tana kokarin shiga gidan, ya zube gwiwa a 'kasa yana gaishe ta. wuce shi tayi ba tare da ta amsa gaisuwarsa ba. Sosai ya ji babu dad'i amma sai ya danne! ya tashi tsaye yana buge rigarsa! Shahida kuwa idonta sun ciko da ruwan hawaye ta ji ciwon wulakancin da tayi masa. "Kayi hakuri don Allah." Ta fada tana kokarin mayar da hawayen dake kokarin kwace mata. Ya ce." Babu komai kada ki damu. zubar hawayenki shine damuwa ta, saboda haka kiyi kokarin hana su zuba." Ta daure tana kokarin mayar da hawayen ta ce." Bari na je na sanar da ita." Ya ce." To babu matsala. Gidan ta shiga ta same su suna mayar da magana. Baban tana cewa." Ai mutumin nan yana da kirki sosai wallahi shine ya bada umarnin cewa a sallami dattijai irinmu saboda raunin da muke dashi, da ba don haka ba da tuni ina can cikin 'kila wa 'kala." Saliha ta ce." Ai ya taimaka wallahi ban yi tsammanin zaki samu ba." Tana kokarin magana Shahidan ta katseta ta hanyar fadin." Baba wannan fa ba rayuwa ba ce, tunda ubangiji ya girmama dan adam babu wanda ya isa ya wulakanta shi, a matsayinki na mai hankali bai kamata kiyi masa haka ba, ban ji dadi ba wallahi." ta kai karshen maganar cikin rawar murya. Ta ce." Rashin kunya za kiyi min Shahida?" Ta girgiza kai "A'a ni ba nufi na kenan ba, kawai kuskuran ki nake nuna miki." Ta ce." Ai ba tun yau ki ka saba nuna min kusukura na ba Shahida ki cigaba da yi min abinda ranki yake so. Ta share hawayen da ya soma fita ta ce." Allah ya baki hakuri! dama zan fada miki ne cewa. Za muje can gurin Babana tare dashi." Ba tare da ta kalle ta ba ta ce." Sai kun dawo." Ga mamakinta sai ta ga ta juya ta fita. Suka kalli juna ita da Saliha ta ce." Gatse fa nayi mata." Saliha ta ce." Don girman Allah Baba ki kyale 'yar iskar yarinyar nan da mahaukacin mutumin nan jiki magayi." Baban ta shiga girgiza kanta tana tu'ajibun al'amarin. Gidan duhu sosai! babu haske. dukkaninsu suna rumfa a zaune yunwa na sasakarsu! yau Talatu dai ta ranste tace kowa ya ci aljihunsa! domin ta gaji yawon cin bashi gashi babu mai ko anini a cikinsu, tunda ba sana'a suke ba, bahaushe ya ce duk lalacewar mutum yana da rana. Talatu tana iyakar bakin ko'kari a kansu, yau dai ta gaji! 'kokari take ma ta biya bashin da ta ci a baya wanda kullum ta Allah ake mata sallama ba dare ba rana. Motsin shigowarta gidan ya sa Hadiza tayi saurin kunna fitilar wayarta tana fadin." Waye?" Ta ce." Ni ce Shahida." Talatu tayi karaf ta ce" Wa ce Shahida kuma. ba dai kurmar yarinyar nan ba, domin na ji kamar muryarta." Hadiza ta ja tsaki mai tsayi ta tashi ta shiga daki ta kwanta. tunanin yanda za a yi ta samu abinci kawai take, tana ganin saurayinta kawai zata kira a waya ta fad'a masa halin da take ciki. A wulakance ta kalle ta kafin ta ce." Ke kuma daga ina da wannan daran?" "Da ga gida nake." tafada a takaice. Ta ce." Ayyo! to ina fatan dai lafiya?" "Gurin Babanmu na zo tare da wanda zan aura za su yi magana." Gabanta ya yanke ya fad'i! ta ce" Waye wanda zaki aura din? wane sakarai! asararran ne mara mafad'i." Jamila
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50