Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 28

Chapter 28

Majanuni Book 1 Complete Hausa Novel 1,210 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

din ya nufa, lokacin ya fita yawon Malamai burinsa kawai a daure bakin Saminu sannan ya wulakanta a duniya kamar yanda ya wulakantashi. Sai Malam Habu ne ya kar'bi mukkulin ba tare da ya bi ba'asin komai ba ya bude gidan, yasa yara suka dinga kwashe kayan suna shiga dasu. A gari ya ji cewa Saminu ya dawo da mukkuli har iyalinsa sun koma ciki, sai ya sake gazgata karfin aikin malamin da ya taimaka masa, domin duk a ganinsa aikin malamin ne yayi tasiri. 'Bangaran Baba Asabe kuwa da kyar ta wayi gari, domin tunda Lurwanu mai kanti ya sheda mata cewa Hujaj ya tafi da Shahida hankalinta ya tashi mutu'ka! har tayi niyyar zuwa gidan suyi wacce za suyi Kawu Musa ya hana ta yace a rabu dashi su ga iya gudun ruwansa. Kasa hakuri tayi washe garin ranar da yamma ta shirya ba tare da tayi shawara da kowa ba ta nufi gidan, domin bata tsammanin zata zubawa mutumin ido yayi abinda ya keso a kan marainiyar Allah, dole sai tayi masa karakare! sannan za su daidaita. _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/K7QH4idftZS5fSw7m2Rueb *Ku yi joining domin samun damar karanta littafi na daya* *MAJANUNI!* (The Unknown Rich Man) NA *BINTA UMAR ABBALE🍒* MANAZARTA WRITES ASSO.. _____ Pege 37&38 'Kamshi turaran ta ne ya tabbatar masa zuwan ta gurin. Cikin nutsuwa ya d'ago kansa daga barin karanta jaridar da ke hannunsa. 'Bata fuskarsa ya yi yana yi mata wani irin kallo na tuhuma. Lallausan murmushi ta yi masa ba tare da tace komai ba ta fara kokarin zama a kujerar dake fuskantar sa. Cikin tsawa! ya dakatar da ita daga abinda take shirin yi. "Ka da ki sake ki zauna anan gurin.'' Ya fada yana zare mata gabad'aya idanuwansa yanda ya tsani mutuwarsa haka ya tsane ta Fatima tayi masa illah a rayuwarsa. Da hannu ya nuna mata hanya da fadin." Fita ki bani gurin tun kafin ranki ya 'baci." Ta girgiza kai still da murmushin a fuskarta ta ce." Ai ko babu komai ka tsaya ka saurare ni domin kaji da abinda nake tafe, idan ban ci albarkacin Shukura ba sai na ci arzikin zumuncin dake tsakaninmu domin dai ni ba zan yi gaba da kai ba." Tsaki ya ja ya koma ya zauna tare da cigaba da karanta jaridar dake hannunsa. Gurin yayi shiru na minti biyar kafin ta sauke zazzafar ajiyar zuciya ta kalle shi wani irin bala'in son sa na ratsa dukkan sassanan jikinta, ita ce tayi wauta a wancan lokacin, gashi yanzu ya yi mata nisa tayi-tayi ta shawo kansa ta kasa, saboda babu wacce ya tsana sama da ita.'' "Maganar Shukura nake tafe da ita." Ta yi maganar idonta a kansa. Shuru bai d'ago kansa ba ballananta ya bata amsa. sai ta d'ora da fadin." Aiki na samo mata a babban kotun birnin tarraya ina fata ba zaka watsa min 'kasa a ido ba." Babu walwala a fuskarsa ya ce." Babu wani aiki da Shukura za tayi, buri na na ga na aurar da ita ga wanda ya da ce, saboda haka wannan maganar ki ajiye ta a gefe.'' "Me kake nufi kenan.? ta fada d'a b'acin rai a tare da ita. Ya ce." Ban amince da kud'irin ki ba." Sai ta fusata! "Amma dai ka san ba kai kad'ai ka ke da iko da ita ba ko? "Yes na sa ni da ni da ke muka haife ta amma abinda nake so shi za a yi idan kuma akwai matakin da zaki d'auka bisimillah." Fuska a tur'be ta mi'ke tsaye! "Shikkenan tunda haka ka ce zan nuna maka nawa ikon a kanta." Fuuu! ta bar gurin ranta a mugun b'ace! Dogon tsaki! ya ja ya bita da mummunan kallo har sai da ta fita daga gurin. Ya d'auke kansa yana jan ajiyar zuciya tare da tuno kuttun 'bakin cikin da ta k'unsa masa a can baya. ******* Da azama ta shiga d'akin sai dai me? tuntube tayi da ita a raku'be jikin dirowar gado ta hada kanta da gwiwa tana wani irin kuka mai tsuma zuciya! Gabanta na fad'uwa ta ambaci sunanta a sanyaye ta ce." Shahida ba zaki fada min abinda ke damunki ba ko? kullum sai ki 'buya a daki kina kuka idan maganar Saminu ce ai ta mutu ki daina damun kanki mutu'kar ina raye ba zan bari mahaifinki yayi miki auran dole ba." Jin yanda take tausar ta da kalamai masu sanyi ya sanya ta sassauta kukan da take yi ta sa hannu ta goge hawayen dake gudana a fuskarta ta ce." Baba ba zaki iya magan ce min matsala ta ba, watakila ma idan na fad'a miki damuwa ta ki kira ni mahaukaciya, shiyasa na gwammace damuwar da nake ciki ta zama ajali na." Maganar ta doke ta sosai! kafafuwanta su kayi sanyi sai ta nemi guri ta zauna tare da fadin." Shahida wace irin damuwa ce wannan ? wacce har ki ke ikirarin ta zama ajalin ki, kada dai a kan mahaukacin mutumin nan ki ke nema ki kashe kanki?" Jin abinda Baban ta ce yasa ta 'kunshe bakinta da tafin hannunta domin ta hana kukan dake k'okarin kufce mata fita. Ta dinga girgiza kanta zafafan hawaye na sharara a fuskarta, murya a sar'ke da yanayin harshenta ta ce." Ki daina kiran sa da wannan sunan domin bai cancanta ba wallahi shi din ba mahaukaci bane kuma zan iya sadaukar da farin ciki na akan sa." Jikinta ya 'kara yin la'asar jin furucin da yarinyar ta yi. ya kamata ta daina tsawwala wa domin ba ta san abinda Allah ya lullu'be ba amma babu shakka al'amarin yana bata tsoro mutu'ka! Ta ce.'' To na ji na daina kiran sa da mahaukaci ko za ki iya fad'a min abinda ya same shi domin tabbas ruwa baya tsami banza

Table of Contents

Chapters

50 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});