Chapter 24
Chapter 24
lahira sai Allah yayi muku hisabi." Ko gezau! ya ce." Ni dai na gama yanke hukunci wannan yarinya ba ta da miji sai wanda na za'ba mata a matsayi na na ubanta yana da kyau a bani hakkina wannan shine magana ta daku ta karshe ku zauna a shirye daga nan zuwa sati biyu komai zai guda na.'' Shuru kawai tayi tana kallonsa hawayen tausayin yarinyar na tsare a saman fuskarta tunda take a duniya bata ta'ba ganin maciyin mutunci irinsa ba, shekara da shekaru yake 'kunsa mata 'bakin ciki har yanzu ta rasa maganinsa. Shi kuwa rigarsa ya buge! ya fita daga gidan cike da cin alwashi akan abunda ya niyyata. Saliha na kife kwanuka a kwando ta ce." Wai Baba ina ruwanki ne! don Allah ki kyale shi yayi iko da 'yarsa mutumin nan bai da mutunci wallahi saura kiris na d'ura masa ashar saboda takaici! Tana goge hawaye ta ce." Saliha har yanzu kuruciya na damunki baki san duniya ba amma mutumin da yake k'okarin hada aure da Shahida bai cancanta ba." Ta ce." To ai gwara shi akan wancan mahaukacin na bakin titi, kamar yanda ya fadi hakane yarinyar nakasashshiya ce da wuya ta samu mijin aure dole sai mara galihu." Girgiza kanta kawai ta ke hawaye na zuba a saman fuskarta, saboda kawai yarinyar na da matsalar kunne shikkenan ba ta da wani farin ciki da jin dadi a duniya ba za a duba cancanta da abinda ya da ce ba, to ita muddin tana numfashi ba zata bari ayi mata auran tozarci ba. Tana fitowa daga kantin Lurwanu ta hango shi ya fito daga gidan. Gabanta yayi mummunar fad'uwa! sam ganinsa ba alkairi bane mussaman yanda ta hango tsantsar tashin hankali a fuskarsa. Babu damar guduwa tunda ya riga ya gan ta, fuska a tur'bune ya k'arasa in da take. sai ta sunkuyar da kanta cikin rawar murya take gaishe shi. bai amsa ba kawai ya rike hannunta ya ja ta sukayi gaba. Jan ta yake tana bin sa har suka fita bakin titi bai ce mata komai ba gabanta sai fad'uwa yake tana kiran Innalillahi wa'ina ilahi raji'un! Suna tsaye a bakin titin suna neman abun hawa Baban -Baba ya 'karaso gurin dugujaja! ya tsaya gefen ta. Hujaj din ya razana kad'an! yana kallonsa ita kam ba ta tsoro ta da ganinsa ba, sai ma wani irin kallo da take masa hawaye na sauka a kumatunta tafi jin tausayinsa akan kanta." Kallo guda ya yi masa ya sha jinin jikinsa idan ba mahaifinta ba to wani shak'i'ki ne a gurin ta saboda yanayin kammani da ya gani a fuskokinsu. Da yake mutum ne mai kyauta sai yasa hannu cikin aljihu ya d'auko dari biyu ya bashi domin shi duk a tunaninsa abinda yake bukata kenan.'' Girgiza kansa ya yi kafin ya ce." Ina zaka kai min mata ta?" Maganar ta dinga yi masa amsa kuwwa! a kunne "Ina zaka kai min matata? ya sake maimaita maganar, itama ta tsorata da jin furucinsa hawayen idonta ya bushe ta dinga kallonsa gabanta na dukan uku-uku! "Kai ba na son hauka! kar'bi nan ka matsa ka bani guri." abinda ya fad'a masa kenan ya sake mi'ka masa gudar dari biyun. 'Kin 'karba ya yi maganar dai ita ya sake maimaitawa "Ina zaka kai min mata ta?" Cikin fad'uwar gaba ya ce." Don Ubanki waye wannan maukacin! meye hadin ki dashi.? Da yake da 'karfi ya yi maganar yasa da sauri ta ce." Ba mahaukaci bane sunansa Baban-Baba a 'karkashin waccan motar yake kwana Baba Asabe tana bashi abinci." Ya ce." Okey shiyasa kuka k'ulla soyayya a tsakaninku.? ido ta tsura masa tana auna maganarsa. Ya buga mata muguwar tsawa! da fadin." Ba zaki bani amsa ba.? ta ce." Ba soyayya muke ba Allah ne kawai ya hada jininmu nake tausayin........Ya wanke fuskarta da wani azababen mari! yana huci! ya ce." Ni zaki mayar mutumin banza ko? wannan d'an iskan mutumin ban yarda dashi ba kina tausayinsa shi zai iya cutar dake saboda haka aure zanyi miki, kai kuma ka saurare ni da kyau." Ya tsura masa idanunsa dake cike da tsantsar b'acin ran marin da yayi wa yarinya ya ji ciwon hakan har cikin ransa. Cikin isa ya cigaba da cewa." Wannan yarinyar tafi 'karfinka ba zan baka auranta ba domin ba ka da komai! mahaukaci kawai." yana kai k'arshen maganar ya ja hannunta suka shiga motar da ta tsaya a gabansu. Ya jima a tsaye a bakin titin yana nazari da tunani akan al'amarin, can kuma na ga ya tsallaka titin ya bi wata hanya ya mi'ke...... ***** "Ranka ya dad'e ina sauraranka. d'aya daga cikin yaransa ke wannan maganar yayin da yake tsugune a gabansa. Ya ajiye jaridar dake hanunsa a nutse ya ce." Sule kai ne kasan gari sosai kasan wata unguwa Ja'in a cikin garin nan.?" Yayi jim na minti biyu kafin ya ce." Eh ranka ya dade ina dai jin sunan unguwar amma ban ta'ba shigar ta ba amma wani lokaci muna bi ta hanyar tare da kai idan za muje babbban kamfanin ka na sumunti dake sharad'a." Ya ce." To ai ta kwana gidan sau'ki tunda ka san hanyar wani aiki za kayi min akan wani mutumi ina so kayi min binkice sosai a kansa. Ya ce." To ranka ya dad'e babu damuwa ya sunan mutumin?" shuru yayi na minti biyu, sunansa Jamilu idan bai manta ba domin can da dadewa ya taba bugun cikin yarinyar ta fada masa sunansa da kuma unguwar da yake zaune. "Sunansa Jamilu amma akwai wani suna da jama'a ke kiransa ya kwanta min a rai amma hakan ba zai zama matsala tunda mutumin sananne ne a cikin unguwar binkice a kansa ba zai yi wahala ba." Ya ce." To babu damuwa ranka ya dade insha Allah zanyi k'okari sanin wanene mutumin domin kawo maka cikakken labari a kansa." Ya ce." To Allah ya taimaka ina tsumayinka daga nan zuwa gobe da safe. Ya mike da fadin." Insha Allah ranka ya dade .'' da sauri ya nufi parking spece ya fito da mota domin cika umarnin maigidan nasa. Na jima ina kallonsa ina hango nagarta da dattijantaka a tare dashi, cikakken mutum ne kamili a zahiri da bad'ini domin yanda yake tafiyar da rayuwarsa a nutse shine zai tabbatar maka da cewa ya san abinda yake. *Binta tana mik'a sak'on gaisuwa ga ilahirin masoyanta💯❤🔥* Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/K7QH4idftZS5fSw7m2Rueb *Ku yi joinig domin samun damar karanta littafi na d'aya* *MAJANUNI!* (The Unknown Rich Man) NA *BINTA UMAR ABBALE🍒* MANAZARTA WRITES ASSO.. _____ _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50