Chapter 41
Chapter 41
ban so kiyi wannan rayuwar ba, na so ki auri miji nutsatstse mai hankali d'an gari mafi kusa dani wanda zai kula min dake da lalurarki, amma hakan bai samu ba, sai wannan kaddara to ina rokon Allah yasa ta zama alheri." Sosai suka rungume juna suna ta kuka! Saliha ta dinga kyalkyala musu dariya tana yi musu vedio, da 'kyar suka rabu da juna kowanne zuciyarsa babu dadi, mussaman Baba Asabe da har yanzu abin bai kwanta mata a rai ba. Ita kuwa Shahida kukan rabuwa da ita kawai take, amma a cikin zuciyarta ba ta tunanin komai face alheri domin ba ta tsammanin cewa masoyin nata zai cutar da ita. **** To tun a mota ta sha jinin jikinta gabad'aya sai tayi sanyi jikinta ya mutu! ta dinga kallonsa a fakaice! tana jin wani irin tsoro a cikin zuciyarta. Gabad'aya kamar tunda aka hallice shi bai ta'ba dariya ba, fuskarsa murtuk! sam ya ma'ki yarda ya kalle ta ballanatana ta samu sararin yi masa wata magana, tun bayan da ya d'auko ta daga gaban mahaifinta ya rikid'e! ya zama mara farin ciki ko a motar ma bai yarda ta zauna a kusa dashi ba, cewa yayi taje can ta zauna cikin mata 'yan uwanta. Ta dinga tunane-tunane marasa kyau a cikin zuciyarta! amma ba ta bari abinda take rayawa a ranta yayi tasiri ba, kawai sai dinga nanata innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! Tunda take bata ta'ba doguwar tafiya irin wannan ba shiyasa gabad'aya! jikinta ya mutu! ta gaji sosai! sai addua take Allah ya sa su sauka lafiya! ko ta samu ta mi'ke k'afafunta! Matar dake kusa da ita ta bata pure water "Kar'bi ruwa 'yan mata naga kamar kin gaji." Ba ta ji maganarta ba kawai dai ta ga tana mi'ko mata ruwa. Da sauri tasa hannu ta kar'ba ta bud'e baki za tayi magana, ya juyo daga mazauninsa wata muguwar harara ya daka mata fuskarsa a mugun had'e! Sai tayi saurin sunkuyar da kanta gabanta na wani irin fad'uwa ta mayarwa da matar ruwan da sauri! jikinta sai rawa yake. Matar ta bi ta da kallon mamaki! sai kuma ta ta'be bakinta ta ajiye ruwanta da fadin."Kin yi wa kan ki." A galabaice suka isa abuja! yanda ta fahimta kamar tafi kowa galabaita watakila saboda rashin sabo ne. Ya riga ta fita daga motar yana tsaye yana jiranta ta fito. a gajiye likis ta fito, nan ta ga yanda ya sa bakin gilashi a idonsa tare da rufe kansa da bakar hular sanyi. ta dan tsaya a gefansa tana bin tashar da kallo! ga rana ta k'wallare! jama'a kowa na gabatar da abinda yake gabansa. Hannunta ya ri'ke! ya jata suka nufi wata rumfar kwano gurin wata mai sayar da abinci bayerabiya. cikin harshen turanci suka gaisa kafin ya shedawa matar cewa ga ajiyar yarinya ya kawo mata ta bata abincin da zai isheta anjima zai turo a d'auke ta, wanda zai zo ya d'auke ta sunansa Sule." Ta Amsa da "to kafin kalle ta da fad'in." Zo ki zauna." tana nuna mata wata kujera. Gabanta ya dinga duka yana daka! hawaye suka ciko idonta! ita dai ba ta ji abinda suke cewa ba amma ta fahimci kamar barin ta zai yi a gurin ganin yanda matar ke kallonta tana nuna mata gurin zama. Ta ri'ke hannunsa tana girgiza masa kai! wasu zafafan! hawaye suka kufce mata. Saurin d'auke kansa yayi ya cire hannunsa daga nata ya kalli matar da fad'in." Tana da matsalar kunne ba sosai take ji ba." Da kansa ya ja hannunta ya kai ta ya ajiye a kan kujera, fuska a murtuke ya ce" Zan je wani guri ne shiyasa na kawo ki anan na ajiye amma zan turo a dauke ki kada ki damu." Bai jira tace wani abu ba yayi saurin barin gurin ko waiwayenta be yi ba. Duk kyawun abincin bai bata sha'awa ba, gabadaya ma ba ta cikin nutsuwarta, tsoro da fargaba sunyi mata dabaibaiyi, tunani ma ta rasa wane kala za tayi, sa'i da lokaci ta ke share hawaye tana bin tashar da kallo da nazarin wace rayuwa za ta fuskanta a nan gaba. Ekeke matar dake sayar da abincin kenan, ta kalleta a karon da ba zai lissafu ba, domin tun tana lallabata ta ci abincin har ta gaji ta zuba mata ido! sai dai haka kawai take tausaya mata idan ta tuna cewa kurma ce ba ta ji sosai, ta yi tunanin abubuwa da yawa akan yarinyar, ta tunanin mutumin yayi kawalcinta ne domin ya dinga biyan buk'atarsa! Sai daf da magariba Sule ya je domin d'aukarta! Ko kusa ko alama bai gane ta ba ballantana yayi tunanin wani abu, ko da yake can baya da ya je binkice lokacin da abin ya faru duhun dare ya shigo da kuma cikowa ta mutane shine dalili. Su ka gaisa da Ekeke kafin ya sheda mata shine Sule ya zo tafiya da yarinyar." Ta ce." To kud'in abinci dubu biyu sai kudin jira dubu uku, duk da ba taci abincin ba ita wannan ba damuwarta bane. Sule bai ja doguwar magana ba ya ciri kudinta ya bata. Jiki a sanyaye take binsa tana ta addua a cikin zuciyarta. ba ta 'kara firgita ba sai da ta ga shirgegiyar motar da ya bude mata wai ta shiga. Ai sai hawaye suka fara zuba kuka sosai take! tana waiwaye a gurin, ta tsorata don gani take kamar sa ce za ayi." Yayi -yayi da ita ta shiga amma fafur! ta' ki shiga sai kuka take tana nema ta tara musu mutane a gurin. Wayarsa ya fito da ita ya kira maigidan nasa ya sheda masa halin da ake ciki. Ya ce ya bata wayar su yi magana. Nan ma da kyar ta karbi wayar jikinta sai rawa yake. Da muryar da ya aro yayi mata magana da k'arfi yanda za ta ji. "Shahida ki shiga mota Sule zai kawo ki gidan da nake aiki wato gidan maigidana kamar yanda nayi miki bayani a can baya. zamu zauna a gidan ne a wani sashe da aka ba mu, ina nan ina jiran zuwanki." Hankalinta ya kwanta jin muryarsa, a sanyaye ta ce." To." ta mika masa wayar tana godiya a cikin ranta domin wallahi tayi tunanin Sule sace ta zai yi. *Normal group #500 Vip group 1k via 0542382124..Binta umar gtbank. idan kati za a turo sai ayi mini magana ta WhatsApp 07084653262...Mutanan Nijar za ku turo dala dari katin airtel. Vip gruop jakka daya.* Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/K7QH4idftZS5fSw7m2Rueb *MAJANUNI!* (The Unknown Rich Man) NA *BINTA UMAR ABBALE🍒* MANAZARTA WRITES ASSO.. _____ *AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE🌳* _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50