Chapter 20
Chapter 20
tana da yanda za tayi akansa da tuni ta samar masa nutsuwa da makwanci mai kyau. Can gurin mai siyar da wainar geron ta nufa. A ka ci sa'a wainar bata k'are ba. to koda ta sayi wainar a maimakon ta nufi gida kai tsaye gurinsa ta koma domin ba ta tsammanin za ta iya sanya wani abu a cikinta mutukar ba tabbatar da cewa shi din yaci wani abu ba. daf dashi ta tsuguna da ledar wainar a hannunta, cikin yanayin tsoro ta kirayi sunansa, ya bude ido yana kallonta, ta ce." Ga waina za ka ci ko.? ya bi hannunta da kallo lokacin da take mi'ka masa ledar wainar. Ta fara k'ok'arin kwance ledar tana fadin." Ga ta nan da zafi ka ci bari na je gida na kawo maka kunu ka had'a." Kallonta kawai yake bai sa hannu ya kar'bi wainar ba. Ta marairaice fuska kamar za tayi kuka ta ce." Don Allah ka ci wallahi tausayi kake ba ni.'' Tsigar jikinsa ce ta tashi jin abinda tace. Ya tsira mata idanuwansa yana jin wani irin tausayinta, ya lura da yarinyar ta na sonshi sosai kuma duk abinda ta fad'a gaskiya ne. Hannu yasa ya 'karbi wainar a takaice ya ce." Na gode." A hankali ya yi maganar shi yasa ba ji ba, amma ta fahimci godiya yake mata. Ta mi'ke da fadin." Bari na je na dawo." Bai ce mata komai ba, ta tsallaka titin ya bita da kallo yana ayyana abubuwa da yawa a kanta. Cikin farin ciki ta shiga gidan, lokacin har sun fara aikace-akaice abincin siyarwa Baban tana yanka kabewa ita kuma Saliha na gyara alayyahu. Da farin ciki a tare da ita tace." Baba akwai kunun ko?" Ta ce." Eh saura naki a kadai gashi can a jug." Tace." Baba yau dai na ga Baban -Baba a bakin titi wallahi dadi ya rufe ni.' Ta harareta da fadin." Matsalarki ce wannan Shahida ni abinda nakeso ki zo ki daka min gyadar miya domin yanzu zan hura wuta na dora miya." Tace." Shikkenan yanzu zan zo nayi." Ba ta sake magana ba, kawai sai gani su kayi ta shiga daki minti biyu ta fito da kwano a hannunta, ta dauki jug din kunun ta kama hanya ta fita. Saliha tace." Wallahi Baba idan ta dawo da kwanukan kada kiyi amfani dasu domin ba kowa za ta kai wa ba sai wannan mahaukacin.' Tace." Saliha ya zanyi da Shahida, na yi magana cibi ya zama 'kari, na zuba mata ido kawai amma ya zama dole idan mahaifinki yazo mu tattauna dashi domin ina wani tunani a kan yarinyar." Tana 'yar dariya ta ce." Wallahi lafiyarta lau tsabar iskanci ne wai ita mai tausayi watarana sai taje ya buga mata dutse idan haukan nasa ya motsa." Ta girgiza kai da fadin." Allah ya rufa asiri. "Wannan naman sallah ne na kawo maka, wannan kuma kunu ne in sha Allahu da rana ma zan kawo maka abinci." Ya kalleta kafin ya kalli abubuwan da ke gabansa, hannu yasa ya bud'e kwanon naman babu abinda yayi suyar tayi kyau sosai sai k'amshi yake. Rufe wa yayi kafin ya bude jug din kunun shima da zafinsa sai kamshin lemon tsami yake, sosai kunun ya bashi sha'awa, amma bai nuna a fuskarsa ba. Sunkuyar da kansa yayi ba tare da yace mata komai ba. A sanyaye ta ce." Sannu ko baka da lafiya ne?" Ya d'aga mata kai alamun ."Eh." gabad'aya jikinta ya mutu kamar za tayi kuka ta ce." Zazzabi ko ciwon kai.? Ganin tana shirin fashewa da kuka yasa ya sassauta fuskarsa ya ce." Babu ko d'aya jikina ne yake ciwo." Ta sauke ajiyar zuciya da fadin." Sannu Allah ya sawwa'ke amma ka daina kwanciya cikin lema dubi abin shimfidar ka a jike ga 'kazanta da kashin awakai dole lalura ta kama ka." Shuru yayi bai ce komai ba. Tace." Ka sha kunun sai na tafi na siyo maka magan........Ya buga mata tsawa! a burkice yace."Ke! tashi ki bani guri bana so kin dame ni da surutu." Ta tsorota ta mi'ke tsaye tana kallonsa, gabad'aya idanunsa sun jirkice! ya d'auki robar ruwan paro ya jefa mata, wanda ya janyo hankalin yara gurin. Aikuwa suka fara ihu! "Baban-baba mahaukaci! Baban Baba mai annakiya." wasu suka fara tsintar duwatsu suna jifansa tare da tofa masa yawu, sai su ruga a guje suna dariya. 'Karkashin motar ya shige ya takure jikinsa guri daya yana makyarkyata! Ita kuwa zuciyarta a 'kuntacce ta bar gurin wani k'atoton abu ya tokare mata a wuya tana shiga gidan kai tsaye daki ta nufa ta kwanta saman gado tare da fashewa da wani irin kuka! Kuka taci ta koshi ta fito idanunta jawur! babu wanda ya tambaye ta abinda ya sa ta kuka aikin gabansu kawai suke, murya a dashe tace."Baba ina gyadar take.? Da hannu ta nuna mata. ta cigaba da aikin gabanta zuciyarta cike da kunci da takaicin halin da yarinyar take 'kokarin jefa kanta. **** "Wai ana sallama da maigidan." muryar wani yaro kenan, yayin da aka aiko shi ya yi sallama da Hujaj. Jamila ce ta fito da fadin." Ba ya nan.'' yaron ya juya ya fita, minti biyu ya dawo da fadin." Wai idan ya dawo a fada masa cewa Saminu abbatuwa yana nemansa." Ta ce." To za'a fada masa. Da ya dawo gidan Talatu ta sheda masa cewa wani yazo nemansa mai suna Saminu Abbatuwa, ko gezau bai yi ba ballanatana ya razana, cin bashi dai ba akansa aka fara ba, kuma sai yana dashi zai biya. Hankalinsa a kwance ya cire babbar rigar jikinsa ya rataye, ya kashingida yana tunanin yanda za'ayi kudi su shigo masa, kwana biyu kamar wanda a kayi wa baki gurin sana'ar tasu haka yake dawowa babu ko sisi a aljihunsa, hakan kuma baya ha na shi gobe ya koma da wata kadarar tasa domin samun nasara tare da nin ka abinda ya bayar. *BINTU* Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/K7QH4idftZS5fSw7m2Rueb *Ma su tambayar farkon littafin su yi joining domin samun damar karanta na daya* *MAJANUNI!* (The Unknown Rich Man) NA *BINTA UMAR ABBALE🍒* MANAZARTA WRITES ASSO.. _____ *27&28* Ha'ki'ka duk wanda ya sayi rariya ya san za ta zubda ruwa, zahiri kuma wanda ya hau motar kwad'ayi to babu shakka za ta sauke shi a tashar dana sa ni, Hujaj cikin rashin k'ima da rashin arziki ya nufi gidansa da gashi sai singlet da gajeran wando domin ko da sanya tufafin jikinsa don ganin kamar zai samu nasara, sai gashi cikin hukuncin Allah an k'wamushe shi, bashi ga tsuntsu bashi ga tarko haka ya nufi gidansa cikin rashin kuzari da rashin 'kwarin gwiwa, in da Allah ya rufa masa asiri ma dare ya tsala babu wanda ya ga ne shi a hanya sai da ya zo shiga gidan ne su ka yi arangama da mak'ocinsa mai suna Malam Habu yana nannad'e tabarma zai shiga gidansa, da sauri Hujaj din yayi nufin shiga gidan, ya ji Malam Habu din yana magana amma saboda kunya bai saurare shi ba, ya yi saurin banko kofar gidan ya sa sakata ya kulle kana ya ja tsaki da fadin munafiki kawai. Malam Habu ya girgiza kai ransa a 'bace da irin zubda mutuncin da ma'kocin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50