Chapter 17
Chapter 17
tace." Baba zuciya tana tausayin wannan mutumin na bakin kasuwa wallahi haka kawai nake tausaya masa, kullum dashi nake kwana dashi nake tashi a raina yau kwana uku kenan babu labarinsa sai dai tarkacensa a karkashin motar da yake kwanciya.'' Baba Asabe ta tsira mata ido cike da tsantsar mamaki tace." Baban- baba kike nufi.? Kai ta daga. Mamaki ya cika ta tace." Ke kuma meye damuwarki da mahaukaci Shahida kada fa garin tausayinki ki jefa kanki a wata musifa watakila ma ba mutum bane, aljani ne domun babu wanda ya san daga wace duniya ya fito." Gabanta na faduwa tace." Wallahi mutum ne kamar kowa kuma ba mahaukaci bane, tunda yana sallah kuma baya doke-doke watakila damuwa ce ta mayar dashi haka." Baba tace." To ai shikkenan yanzu wane irin taimako za'ayi masa." Wani dadi ya ratsa zuciyarta, cike da farin ciki tace." Ki sanya masa kwano na abinci tun daga safe har dare, tunda Allah ya baki yanda za kiyi wallahi zaki samu lada." Tace." To shikkenan zanyi yanda kikeso amma kada na kara ganin kin shiga damuwa a kansa, kuma kiyi kaffa-kaffa dashi tunda na lura baki da hankali." Tana 'yar dariya tace." Baba kenan, Baban-baba ba zai cutar dani ba nayi imani da hakan, tunda na jima ina bashi sadaka kuma bai ta'ba yunkurin kawo min duka ba, sai dai yace ya gode." Shuru kawai tayi mata ba wai dan bata da abun cewa ba, tsabar takaici ne ya isheta, yanzu yarinyar ta zama hukuma sai da rarrashi! za tayi kokarin ganin tayi mata duk abinda ta ke so. *BINTU* Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/K7QH4idftZS5fSw7m2Rueb *Ma su tambayar farkon littafin suyi joining domin samun damar karana na d'aya A yi hakuri a daina bi na pravite Na gode.* *MAJANUNI!* (The Unknown Rich Man) NA *BINTA UMAR ABBALE🍒* MANAZARTA WRITES ASSO.. _____ *19&20* Duk da Baba Asabe ta amince da abinda ta ke so hakan bai sanya ta kwantar da hankalinta ba, kullum cikin damuwa take duk saboda rashin sanin takameman gurin da mahaukacin ya sauya da zama, don ita duk a tunaninta tsokanar da yara ke masa ya sanya ya bar gurin, a rana ta kan je bakin kasuwar sau uku ko fiye da haka tayi ta dube-dube ko Allah zai sanya ta gan shi, babu shi babu dalilinsa sai tarin tarkacensa dake k'ar'kashin matacciyar mota (a kori kura) da yake kwanciya a 'karkashinta. Da azumin arfa a bakinta daf da za'a sha ruwa ta faki ido ta fita daga gidan kai tsaye bakin kasuwar ta nufa. Baba Asabe ta fito daga kicin da muburgi a hannunta, Saliha ce kad'ai a zaune a tsakar gidan tana had'a musu lemo, tace." Ina Shahida ita kuma sai tazo ta soya mana awara kada asha ruwa mu rasa abunda za musa a bakin salati." Tabe bakinta tayi ta ce." Yanzu ta fita." Cike da mamaki ta ce." Ta fita kamar yaya ina taje?" Ta ce." To ni kya tambaye ni, nima ban sani ba, na san dai sa'i da lokaci tana fakar idonki ta fita." Baba Asabe bata kawo mummunan abu a ranta ba, tafi tunanin cewa Shahidan bakin kasuwa take zuwa gurin mahaukacin data d'auki son duniya ta d'ora masa. A fili ta ce." Allah yasa ya tafi kenan ba zai dawo ba domin kuwa na fara zargin mutumin nan idan ba aljani bane to babu shakka maye ne." Ta d'aga labulan d'aki ta shiga tana cigaba da maganar da alama al'amarin yana damunta. Yau ma ba sa'a domin kuwa gurin zaman nashi ma dabbobi (awakai) ne a kwance a gurin duk sunyi masa kashi ga ruwan saman da akayi jiya ya jika masa wasu kayan nasa, babu shi a gurin sai dabbobin da suka maye gurbinsa. Wasu zafafan hawaye suka ciko idonta, ko'ina mutumin nan ya shiga? "Watakila ya mutu a wani guri." Zuciyarta ce ke raya mata hakan. Ta girgiza kai gabanta na wani irin fad'uwa! "Insha Allahu bai mutu ba." Ta furta hakan a fili. Da sauri tasa hannu ta goge hawayen da ya zubo ta kira wani yaro da hannunta. Yaro yazo ya tsaya gabanta da ledar kankana da lemo a hannunsa da alama aikensa akayi kuma da azumi a bakinsa yana sauri ya isa gida yace." Gani." A sanyaye tace." Don Allah ko kasan inda Baban-baba ya koma da zama?" Cike da rashin fahimta yace." Waye Baban-baba?" Ta nuna masa tsohuwar motar da fadin." Mutumin dake zama a waccan motar." Ya kalli gurin da take nuna masa ya juyo da tsoro a tare dashi ya ce." Ni ma ban sani ba.'' bai jira jin abinda za tace ba yayi saurin barin gurin yana waiwayenta. Ba ta ha'kura ba ta sake tarar wani yaron tana tambayarsa, yaron irin marasa kunyar nan ne, kawai sai ya fashe da dariya yana gwada irin maganarta ta kurame! "habbbaba! ya nu na ta da yatsa yana kyalkyala dariya ta bishi da kallo tausayin kanta da kanta ya lullubeta, wai shin ita din abar tausayi ce ko kuma Baban-baba? Hawaye masu zafin gaske suka ciko idonta, tayi namijin k'okarin hanasu zuba, da saurin gaske ta bar gurin tana addua a zuciyarta. Koda ta koma gidan ma 'bacin rai ne! don fad'a ta riska, Baba Asabe ta inda take shiga ba ta nan take fita ba har da cewa idan ba tayi a hankali ba to za ta kai ta asibitin dawanau a duba kwakwalwarta, to itama a lokacin da Baban ke fadin hakan ba taji haushi ba domin ta fara zargin kanta anya kuwa bata samu matsalar kwakwalwa ba. Washe gari aka tashi da sallah, jama'a nata walwala da farin ciki mussaman wanda Allah ya hore wa abin layya ciki har da Baba Asabe domin babban (rago) na dubu sittin ta saya tayi layya dashi, wadatar zucci ne da ita tare da 'ko'karin faranta ran jikokinta dake gabanta. Uku ga sallah ta shirya tsaf fuskarta babu walwala ta fito daga d'aki da hijab dinta a hannuta. Baban ta kalleta da fadin." Kin shirya kenan? ai da nace Saliha ta shirya kuje tar.....Salihan ta katse ta da fadin." Ni babu in da zani bacci zanyi na huta, sannan kuma da yamma Kamalu zai zo muje gidan yayarsa ziyara." Kamalu shine saurayinta wanda akayi musu baiko. Baban ta ce." Ayyo! to shikkenan Shahida kinji abinda ta ce." Babu damuwa a tare da ita ta ce." Babu komai.'' Hanyar fita ta nufa da fadin." Sai na dawo." Ta ce." Ki gaishe su ba dan halinsu ba, maganar naman sallah kuwa ba zan ce ki tafi musu dashi ba dalili na fi kowa sanin waye Jamilu da burgar tsiya yanzu idan baki take ba yana nan ya kayar da manyan shanu yana neman suna a unguwa." Bata tsaya taji 'karshen maganar ba tayi saurin fita daga gidan, a ranta tana jin haushin irin cin mutuncin da Baban ke wa mahaifinta. Ilai kuwa tana shiga gidan taga zahiri domin kaca-kaca ta samesu suna ta aikin suyar nama tare da daka dambu a k'aton turmi Hadiza ce mai wannan aikin. Can gefe kuma ganda ce tare da kan sah! da rago a babbake akan buhu an shanya k'udaje sai tashi suke a gurin da wari mara dadi. Jamila ce kawai ta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50