Chapter 31
Chapter 31
dala dari Vip jakka daya, katin airtel za ku tura min da shi ta wannan number 07084653262 Allah ya ba mu sa'a da rabo mai amfani. _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/K7QH4idftZS5fSw7m2Rueb *MAJANUNI!* (The Unknown Rich Man) NA *BINTA UMAR ABBALE🍒* MANAZARTA WRITES ASSO.. _____ Pege 41&42 Cike da fuffuka! irin ta rashin gaskiya ya nuna ta da yatsa da fadin." Kada ki yi min maganar banza da wofi mana; don uwaki ni za ki zauna kina tsarawa magana, ke din guda nawa kike? me ki ka sani a rayuwa da har zaki zo kina kawo min 'kabli da ba'adi, to wannan shine gargadi na dake na karshe! kada wani abu ya sake faruwa ki zo kina min wasu zantuka ranki sai yayi mummunan 'baci! wallahi." A sanyaye ta ce." Kayi hakuri Baba." tsawa! ya daka mata ya nuna mata hanyar fita da fadin." Fita ki bani guri shashasha kawai." Da sauri ta fito tana share hawaye! Talatu ta ja tsaki da fadin." Aikin banza yarinya kina wahalar da hawayenki a wofi wannan mahaifin naku ai ya riga yayi nisa domin ba zai ta'ba gane hanya ba, don haka kowacce ta nemi madafa don duk wanda ya dogara da Jamilu 'bacin rai ne zai kashe shi." Hadiza ta ce." Talatu duk lalacewarsa ubanmu ne babu yanda za mu yi dole mu shiga damuwa." Ta ce." To ai sai ku yi karo karo ku biya masa bashin da ake bin sa shashashai kawai ana nusar da su suna baud'ewa." To in ban da rigima irin ta Talatu ya za su yi ? za su je su rufe shi da duka ne? ai ya riga ya gama yi musu illah! a rayuwarsu dole kuma su yi hakuri su cigaba da yi masa addu'a domin ba a canzawa towo suna. A na kiran sallar isha'i mai adaidaita sahu ya sauke ta a bakin titi. Kud'insa ta bashi ta fara kokarin tsallaka titin da nufin shiga layinsu, dan gabadaya Hankalinta yayi gida ganin garin yayi duhu, gashi babu wani cikkaken haske akan titin. tana kokarin tsallakawa kawai ta ji ana jan gefen hijab d'in ta. A razane! ta juyo sai tayi saurin ja da baya tana kallonsa gabanta na wani irin fad'uwa! Yana nan yanda yake sai dai an samu sauyin tufafi a jikinsa, amma fuskarsa tana nan cike da 'kasumba sumar kansa duk a cukurkud'e! Yana sanye da tazarce na shadda bulu sai dai ta kod'e sosai tayi haske sai wani takalmi sosa a kafarsa shima ya sud'e! amma babu datti a tare dashi. Murmushi kawai yake mata yayin da yake mata wani irin kallo. Ita kuwa gabanta sai bugawa! yake tana kallonsa tana so ta tabbatar da cewa shine ko kuma aljani ne domin al'amarin ya 'bata tsoro mutuka! Maganarsa ta dawo da ita hayyacin ta. "Shahida ni ne Baban-baba kina mamakin gani na ko?" da d'an k'arfi yayi maganar saboda ya san lalurar ta. Zazzafar ajiyar zuciya ta sauke har yanzu da ragowar tsoro a tare da ita ta ce.'' Baban Baba kai ne da gaske ko dai idona ne yake min gizo." Ya sake matsowa kusa da ita a nutse ya ce." Ni ne dai masoyinki na san kin yi kewata ko? nima ina can hankali na yana kan ki." Wasu hawaye masu zafi suka 'kwace mata ta ce." Alhamdulillahi Allah Na gode maka daka 'kar bi addu'a ta." Yana murmushi ya ce." Ai d'azu akan idona kuka fito tare da wata abokiyar ki sai na ga fuskokinku cike da damuwa! ganin haka ya sa jiki na yayi sanyi na ce lallai akwai abinda yake faruwa, wannan dalilin ya sa na ce sai na zauna na jira dawowarki kafin na tafi." Sunkuyar da kanta tayi tana wasa da yatsun hannunta. Ya dan sake matsowa daf da ita da fad'in." Ko ba zaki iya fad'a min damuwarki ba?" Ta kalle shi tana girgiza kai. Ya tausasa murya da fadin." Ina sauraranki ki sanar dani abinda yake faruwa domin ganin ki cikin damuwa da tashin hankali ya sanya ni cikin wani hali." Ita dai a tsorace take dashi dan sai waiwayen bayanta take. Shima ya fahimci hakan ya ce." Kina jin tsoro na ko? Zuciyarta ta karye sai kawai hawaye suka shiga gangarowa ta sanya hannu tana sharewa wasu na biyo baya! sai jan majina take. Wani irin ciwo zuciyarsa take masa. tuntuni ya tsani zubar hawayen ta ita ce ba ta fahimci hakan ba. Ya rasa yanda zai yi a gurin yana jin kamar ya rungume ta ya rarrashe ta, sai dai ya daure ya shirya kalaman rarrashi ya fara kwantar mata da hankali har ya samu ta daina kukan. Ta kalle shi; nan ta fahimci cewa yana cikin damuwa da kukanta, sai ta sassauta fuskarta ta d'an yi kasa da kanta ta ce." Ka fara fad'a min ya akayi rayuwarka ta sauya ? wani almajiri dai ya tabbatar min da cewa an tashe ka daga gurin da kake rayuwa to tun daga lokacin ba a 'kara ganin ka ba. shin dama kai din ba mahaukaci bane?" Murmushi yayi, ya ce." Ni ba mahaukaci ba ne Shahida." Da sauri ta kalle shi tana mamakin furucinsa, koda yake ba abun mamaki bane a gurinta tunda dama can ita ba ta yi masa wannan kallon. Ya cigaba da cewa " Rayuwa ce ta mayar dani haka amma yanzu alhamdulillhi na gode Allah tunda ya mayar min da alkairi ya had'a ni da uban gida wanda ya dauke ni aiki a garin abuja, ina masa gadin gidansa ni nake kula da masu shiga da fita! wannan shine ya sauya min rayuwata na dawo cikkaken mutum kamar kowa tunda bani da fargabar ci da sha da kuma gurin kwanciya komai ya d'auke min, nutsuwa ta zo min ban yi tunanin kowa ba sai ke domin ina ganin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50