Chapter 1
Chapter 1
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/K7QH4idftZS5fSw7m2Rueb *MAJANUNI!* _(The Unknown Rich Man)_ Na *BINTA UMAR ABBALE🍒* MANAZARTA WRITES ASSO.. _____ Dukkan yabo da godiya su tabbata ga Ubangiji mad'aukakin sarki. Tsira da aminci su 'kara tabbata ga fiyayyan hallita Annabi Muhammadu S.A.W *MAJANUNI* 'Kir'kirarran labari ne wanda ba'ayi don a ci zarafin wani ko wata ba. duk wanda ya ga ya yi dai-dai da rayuwarsa to a rashin sani ne. TSOKACI: Kasancewar Ubangiji ya halliceka da ji da ga ni tare da wadatacciyar lafiya, to kada hakan ya sanya ka d'auki kanka daban da sauran wanda aka hallita da wata larura makamanciyar wannan, Ubangiji ba yanda baya zartar da ikonsa, kuma yanda ya so haka shi yake faruwa. tabbas bawa baya shiryawa kansa rayuwa face wacce ya riski kansa a ciki. *_Da 'ko'kari da jajurcewarki wannan Littafi ya fita. Hasinatu (AUTAR MANYA💯) Binta tana godiya, rabbi ya tabbatar da zumuncinmu har gaban abada._* *Am Back Again* Allah ka bamu sa'a da rabo mai amfani. *1&2* *KANO STATE* *GADAR SALGA* Unguwa ce mai zaman kanta wacce take daura da kasuwar kurmi tsohowar kasuwa mai d'umbun tarihi a jahar *KANO.* Cikin rukunin gidajen yaku bayi na cikin unguwar. Matashiyar budurwa 'yar kimanin shekaru goma sha tara Zuwa ashirin zaune a kan kujera 'yar tsuguno da tarin wanke-wanke a gabanta tana wankewa tare da kifewa a cikin wani babban kwando. wanke-wanken take tun k'arfi da alamar sauri a tare da ita. Cikin rashin kintsi! Saliha Ta iso inda take, ba tare da tunanin komai ba ta kurma mata wani irin ihu! a cikin kunnuwanta! A Zabure! ta juyo har farantin dake hannunta yana fad:uwa a kasan gurin, idanuwanta sukayi rau-rau kamar zata fashe da kuka ta fara magana cikin yanayin na 'bacin rai! tare da yanayin hallitar da Allah yayi mata tace."Saliha menene haka."? Cike da rashin mutunci tace." Yo idan ba haka akayi miki ba ai ba za kiji magana ba, yaushe zan dinga wahalar da kaina gurin kiran sunanki ai ihu! kawai shi ya cancanta ayi miki tunda kunnuwanki a toshe! suke." Girgiza kanta kawai tayi tare da mayar da kanta 'kasa tana cigaba da wanke-wanken dake gabanta. A fusace! tace."Au! Shahida mahaukaciya kika mayar dani ina miki magana kinyi min banza to bari naje na shedawa wacce ta aiko ni kiran ki. Hanci ta shak'a ta sanya hannuna ta goge gumin goshinta cikin yanayin magana irin ta kurame! tace."Saliha kina dai ganin wanke-wanken nake ko." Saliha ta watsa mata harara da fadin." To ba zaki bar wanke-wanken ba ki tashi ki je kiran da take miki ba." A hankali ta ajiye sosan dake hannunta ta mike tsaye hanya ta nuna mata da hannu da k'arfi ta ce"Wuce muje." girgiza kanta tayi rai a b'ace tayi gaba Salihan ta rufa mata baya. Baba Asabe tana zaune a tsakiyar rumfa tana d'aura gishiri su ka yi sallama Saliha kai tsaye cikin uwar d'aki ta shige tabi lafiyar gado. Ita kuwa tsugunuwa tayi a gabanta cike da ladabi tace."Baba gani Saliha tace kina kira na." Ta ajiye d'aurin gishirin ta janyo jakarta dake gefe kudi ta dauko daure a leda ta kalleta da fadin." Bakin asibiti za ki je ki dauko min man gyda tun shekaran jiya ya k'are anata zuwa nema." bakinta kawai take kallo, nan ta fahimci abinda take nufi, tunda ba wai da 'karfi take maganar ba, shiyasa ta tsirawa bakinta ido, ta na ji amma ba sosai ba, shiyasa wani lokacin idan ana magana take bin bakin mutum. nan take fahimtar komai. Cikin saurin magana da yanayi na harshenta ta ce." Ban gama wanke kwanukan ba." Ta ce."Ki ajiye idan kin dawo ki k'arasa ai da sauran lokaci." Ta amsa da "To" Tare da mi'kewa. uwar dakin ta shiga domin dauko hijabi nan taga Saliha a kwance da waya a hannunta tana game. Girgiza kanta kawai tayi ta bude ma'ajiyar kayanta ta dau'ko hijabi tasa a wuyanta ta fito falon. Ta kalleta da fadin."Dubu arba'in da hud'u ne man gyada galan d'aya manja ma galan d'aya kafin ki isa zan kira Garba a waya na sheda masa zuwanki ya tari a daidaita sahu ya sanya komai a ciki. Tace."To shikkenan Baba sai na dawo." Tace." Ki kula sosai da kudin hannunki yau Juma'a akwai turmutsutsu na jama'a." Kud'in ta ri'ke da kyau da fadin." Zan kula insha Allah. Cikin nutsuwa take tafiya har ta fito bakin titi can tsallake ta hango mutumin ta zaune a 'karkashin tsohuwar motar da yake zama tare da tarkacen kayansa na mahaukata! Girgiza kai tayi tana me tsira masa ido yana kwance kan wani tattararran buhu ya takure jikinsa guri daya jikinsa duk yayi fururu! kasancewar lokacin sanyi ne shiyasa al'amarin ya tu'azzura. Ajiyar zuciya mai zafi ta sauke tana sake jin tausayinsa na bin ilahirin jikinta, hakika da tana da yadda za tayi da ta taimaka masa ya daina kwana 'kar:kashin mota duk yanayin da ake ciki na ruwa da iska anan yake wanzuwa tsayin watannin da yayi a cikin unguwar tasu. Cike da tsantsar tausayinsa ta d'auke kanta daga inda yake ta fara laluben abun hawa Juma'a ce shiyasa abubuwan hawa sukayi k'aranci a kan titin. Ihu! da hargowar yara ya sanya da sauri ta mai da kanta gurin, nan taga yara masu yawa sunyi masa rumfa suna tsokanarsa sai ihu! suke tare da fad'in "Baban- baba kazami! Baban -baba mai annakiya Baban-baba mai kashi a wando."! Shi kuma Yana zaune yana kallonsu fuskarsa a sake kamar koda yaushe idan yara suna tsokanarsa sai ya yi ta murmushi koda kuwa cikinsu za'a samu masu jifansa da duwatsu! ba zai yi 'ko'karin 'kare kansa ba. Ranta ya 'baci mutuk'a ganin yanda manya mutane ke wucewa wasu a kasa wasu abubuwan hawansu amma a cikinsu an rasa wanda zai tsawatarwa da yaran akan abinda suke. Ba tare da tayi tunanin komai ba ta tsallaka titin kai tsaye gurin ta nufa. Tana zuwa cikin 'bacin rai irin na kurame take musu fad'a tana korarsu........Sai suka kwashe mata da dariya suna nuna ta da hannu da fadin." Mu bama jin abinda kika cewa ke din kurma ce ko kuma bebiya?" Abun yayi mata ciwo sosai ta sake d'aga muryarta cikin yanayin saurin maganarta da yanayin hallitarta take gargadinsu da fadin." Ita din kurma ce kuma haka Allah ya halliceta idan da wanda ya isa ya sauya mata hallita a cikinsu sai ya d'aura aniya. Suka dinga kyalkyala mata dariya sunayi mata ihu! kawai sai ta durk'ushe a gurin ta fashe da kukan 'bakin ciki a wannan lokacin ledar kudin dake hannunta ta fad'i ba tare da 'bata lokaci ba wani matashi dake can tsallake yazo ya d'auke yayi gaggawar watsa yaran ya gudu da kudin a daure a leda. Ido kawai ya tsira mata tana tsugune a kusa da shi kanta a tsakanin kafafunta sai kuka take. Sosai yake jin zafin kukanta a cikin zuciyarsa to amma 'kudirin dake cikin zuciyarsa shi ya hana shi rarrashinta tun ba yau ba ya san da yarinyar a duk sanda zata gan shi a hanya ko a gurin zamanshi yana hankalce da irin kallon da take masa 'kwayar idonta kadai ita ke nuna masa da cewar ta damu da shi, duk da cewa wata magana bata ta'ba
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50