Chapter 7
Chapter 7
ya fita daga gidan. Ganin haka yasa Shahida shiga daki ta kwanta kan gado abu biyu suka dame ta irin rayuwar k'as'kancin da take a tsakanin 'bangare biyu da kuma al'amarin *Baban- baba* daya tsaya mata a cikin rai. Hawaye masu zafi suka dinga karakaina a saman fuskarta hakika maraici bala'i ne tabbas da uwarta tana raye a duniya ta san ba za tayi irin wannan rayuwar ba, Baba Asabe itace ta haifi mamanta itace kuma ta haifi Kawu Musa mahaifin Saliha kenan amma ba tasan me yasa take fifita Saliha a kanta ba, Gashi dai duk ita ta haifi iyayensu amma tafi son Saliha a kanta duk abinda Saliha za tayi daidai ne a gurinta amma ita abu kad'an idan tayi sai ya zama laifi. Ta shigo dakin ta sameta tana kuka, sai jikinta ya kara sanyi murya ta d'aga da karfi ta ce."Kukan me kuma kike bayan ubanki yazo ya fanshe ki ashe dama yana da kudi mugunta ce take sa baya zuwa ya bani wani abu duba da irin dawainiyar da nake dake ko tausayin tsufa na ba ya ji." Ta mi'ke zaune cikin 'bacin rai da masifa irin ta kurame! tace."Wai shin Baba ni d'in bare ce a gurinki? ko kuwa bake kika haifi uwata ba?" Ta rike baki tana kallonta da fadin." Ni kike wa tsawa yau kuma tambotsan naki a kaina zaki sauke shi?" Tace"Ni tambayarki nake ina so ki bani amsa? Tace."Ni ce na haifi Uwarki na kuma Haifi Musa su biyu kacal Allah ya ba ni sai me kike so kiji.? Tace."To me yasa kike 'bakin ciki don kin kula dani kin ciyar dani kin tufarta dani don kinyi min d'awainiya shine kike gorantawa ubana ai sai yana dashi zai zo ya baki." Cike da dumbun mamaki tace."Shahida yau ubanki kike fifitawa a kaina.? Tace."Kada kiyi min mummunar fahinta Baba ina so na nuna miki Kuskuran da kike aikatawa kada ki d'auka bana fahimtar komai duk abinda kike ina lure dake kin fi k'aunar Saliha a kaina meye dalili? ko don ita ubanta yana baki kudi ni kuwa uwata ta mutu bata raye babu abunda take tsinana miki shine kike gallaza min saboda kawai tsautsayi ya ratsa an sace kud'inki shine har zaki tattara min kayana ki watsa waje wai kin kore ni Haba Baba ke baki ji kunya ba." Baba Asabe bakinta ya mutu kallonta kawai take ta cigaba da cewa." Tunda kika dasa sayar da man gyada a gidan nan ni nake zuwa na saro miki kuma bant'ba zubar miki da kudi ba sai wannan karon amma saboda rashin tawakkali kika fita duniya kina zage-zage kowa yana kallonki ai wannan abun kunya ne." Baba Asabe ta fashe da kuka tasa gefen zaninta ta fyace hanci ta ce."Lallai Shahida wuyanki ya isa yanka ni kikewa rashin kunya ko kuma dai Jamilu da Talatu sunyi miki hud'uba akaina." Tace."Ni ina ruwana da Talatu itama ai ba k'aunata take ba kuma Abbanmu ba zai zuga ni nayi miki rashin kunya ba." Ta goge fuska da fadin." To babu laifi tunda a karan kanki ki kaga dacewar hakan na gode." Tana 'kare maganarta sai ta kama hanyar fita tana goge fuskarta. Komawa tayi ta kwanta tana jin wasai a cikin ranta dama abubuwan da ake mata a gidan yana damunta yau dai ta amayar da abunda yake cikinta ta samu sa'ida. Ta shigo d'akin ta tsaya a kanta cike da tsageranci ta d'aga murya da fadin." Shahida ke marakunyar ina ce da zaki dinga farfad'awa Baba magana kamar wata sa'arki." Dama a ciki take da ita sai ta zabura! ta mike tsaye jikinta har tsuma! yake cikin yanayin maganarta tace."Mara kunyar gidanku ce! nace mara kunyar gidanku ce idan kina da mataki ki dauka." Saliha ta tsorata domin ta san halinta idan tana cikin bacin rai! bata lank'wasuwa kuma idan fada ya ratsa a tsakaninsu da wuya take kai labari domin lilis! take mata. Sai taja baya, bata daddara ba tace."To mara kunya Da kika mike tsaye kina wani zabura! duka na za kiyi ne kin san dai ni ba sa'arki bace." Tace."Ki fita ki bani guri bana bukatar ganinki ni duk wanda ba zai ja girmanshi ba to zan hau kai na taka kuma ke baki cancanci na baki girma ba saboda kema baki da ladabi." Tace."Don Ubanki ni ce mara dalabi.'' Tace."Ubanki dai domin uba bai fi uba ba ehe.! Saliha ranta ya 'baci kawai sai ta fitar da hannu ta kai mata duka, ai kafin kice me! ta cukumeta ta matseta jikin bango! tana dukanta ta ko'ina." Saliha ta dinga ihu! tana kakari tare da kiran sunan Baba wai tazo ta ceceta. Ita kuwa Shahida dukanta kawai take sai kace wata mai iskokai. Hankali a tashe ta shigo dakin tana fadin." Sai da nace ki kyaleta saboda kinfi kowa sanin halinta idan tana irin wannan halin babu maganar wanda ta ke ji kuma 'karfi ku ba daya bane kin girmeta amma ta fiki 'karfi duka take miki." Saliha na ihu! take fadin." Ki janyeta ni ba surutu za ki yi ba ta matse min wuya zata kashe ni." Cikin rarrashi da kwantar da kai tace." Yarinyar kirki yi hakuri ki saketa ai ta daku kada kiji mata ciwo kinga k'arfinku ba daya bane kiyi hakuri ta daina yi miki katsalandan a cikin al'amuranki." Banza tayi mata ta cigaba da dukanta tana mintsininta! Baba ta cigaba da banbanki tana kwantar da kai da 'yar murya tace."Shahida kinga bani da lafiya kada wannan 'bacin ran yasa ciwona ya tashi yau da 'kyar zan iya bacci sakamakon wannan al'amari banji dadin maganganun da ki ka fad'a min ba." Ta fashe da kuka tana cigaba da maganar daso ta tabbatar mata da cewa abun yana ci mata towo a kwarya. Ganin yanda take kuka ne yasa ta saketa ta koma gefe tana mayar da numfashi, Saliha data samu kanta sai ta wawuri! wani gwangwani da Baba ke ajiye-ajiye a ciki ta kai mata duka dashi da fadin." Shegiya mayya 'yar mai dattin hula." Da yake 'kasa-'kasa tayi maganar yasa ba taji ba, Baba ta buga mata tsawa tare da nuna mata hanyar fita, tana numfarfashin wahala ta fita d'aga dakin. Baba ta rufa mata baya ba tare da ta sake wata magana ba. Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/K7QH4idftZS5fSw7m2Rueb Ku yi join domin samun damar karanta littafi na d'aya. *MAJANUNI!* (The Unknown Rich Man) NA *BINTA UMAR ABBALE🍒* MANAZARTA WRITES ASSO.. _____ *AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE* _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50