Chapter 40
Chapter 40
da kallon mamaki! lallai al'amarin yarinyar ya fi karfin tunaninsu. *An fara biyan kudin littafin masoya* *Hanyar da za a biya kudin mai sauki ce #500 Vip 1k 0542382124...Binta umar gtbank. idan kati za a tura sai ayi mini magana ta WhatsApp 07084653262* *MAJANUNI!* (The Unknown Rich Man) NA *BINTA UMAR ABBALE🍒* MANAZARTA WRITES ASSO.. _____ *Dubbun Godiya zuwa ga:* *Hajiya Hadija Marad'i (Nijar) Ina godiya da abin alheri Hajjaju🥰🙏🏻* 49&50 'Yan Allah ya sanya alhari da 'yan gulma sai shige da fice suke a gidan, ita dai Baba Asabe kallonsu kawai ta ke yi saboda ta san mafi akasarinsu, ba alheri ne ya shigo dasu ba, domin da kunnanta ta ji wasu mata suna maganar cewa; ai auran kawai aka d'aura amma babu lefe babu komai, asali ma angon yana da matsalar k'wak'walwa sannan ba shi da wani cikakken asali. ire-iren wannan zantukan jama'a suka ke'be guri guda su na yi. Amarya kuwa sam ba ta sanya damuwar komai a cikin ranta ba, ta na ji ko babu lefe za ta iya zama da masoyinta burinta ya cika za su rayu cikin inuwa d'aya. Kitso akayi mata 'kananu irin na bare-bare sai k'unshin salatif da makociyarsu tayi mata, ta sanya sabuwar atamfa wacce ya kawo mata a din'ke da mayafi da takalmi, Rabi makociyarsu wacce tayi mata k'unshi itace tayi mata kwaliyya dai-dai gwargwado tayi kyau tana ta murmushi, mutane na ta'ba ta suna mata Allah ya sanya alheri. Saliha kuwa sai dariya take mata addua take a zuciyarta Allah yasa mahaukacin ya nuna mata tumasanci! Can gidan Hujaj kuwa Talatu kamar ta zuba ruwa a kasa tasha ganin yanda al'amarin auran ya kasance, babu lefe babu wata hidima da ango yake wa amarya. babban farin cikin ta da ta samun labari cewa ai angon ma bashi da hankali asalinsa mahaukaci ne kawai ya d'an samu sau'ki ne! wannan al'amari yayi mata dadi sosai, kawai sai ta kwantar da hankalinta ta cigaba da sabgoginta, ko gidan bikin ba ta je ba, Jamila ce kawai tayi wanka ta shirya ta tafi. ita da sauran yaran suna gida duk wanda ya shigo sai sun labarta masa abinda yake faruwa domin ita Hadiza ma yawon gantali ta tafi da saurayinta. Da magariba Hujaj ya shigo gidan; 'kalau dashi cikin sabuwar shadda babba riga da 'yar ciki, komai sabo ne a jikinsa sai walwala yake kamar bai ta'ba shiga wani rikici ba. A tsiyace! ta kalleshi kafin ta ce." 'Karya banza da wofi ina zaune labarin komai ya same ni da har kake wani fuffuka kana murna ka dauki 'yarka ka bawa mahaukaci wanda ba a san asalinsa ba." Ya ce." Ai gwara ita akan ke da 'ya'yanki, Talatu daf ki ke da ki bar gidan nan, ki rubuta wannan ki ajiye mutsiyaciya kawai duk kin tsiyata ni, zan dai auro wacce take dai-dai da arziki na." Ta buga cinya da fad'in" Ai wallahi 'karya kake Jamilu, ai na ci gida ko ka sake ni ba zan fita ba ina nan daram dam." Ya ce." Tunda gidan ubanki ne ai sai ki zauna sakarai shashasha! kawai." 'Kwallah ta ciko idonta tana rawar murya ta ce. " Shashasha ba, ai ka santa. A sukwane ya gaura mata mari! wanda sai da ta ga gilmawar taurari! ya nuna ta da yatsa da fadin." Wallahi ki ka sake wata magana a bakin auranki domin dama na ga ji da zama da ke mahaukaciya kawai." D'aki ta shige tana wani irin kuka mai tsuma zuciya! Bayan sallar isha'i Hujaj ya dira a gidan, Baba Asabe. ta shimfid'a masa tabarma suka gaisa kamar abin arziki. Shahida ta fito ta gaishe shi, ya amsa kafin ya ce ta nemi guri ta zauna. Gurin yayi shuru na minti biyu yayi gyaran murya da fad'in." To Alhamdulillhi, bu'katata ta biya gurin ganin na auran da yarinyar nan a in da ya da ce! wannnan mutumin ya fitar dani kunya saboda haka ko da yana tsince-tsince ne akan bola zan iya bashi auran 'ya ta saboda yayi min abinda ba zan mance ba. Shahida 'ya tace, ni ne ubanta ni nake da iko a kanta, saboda haka babu wani mahalukin da ya isa yace ga yanda zan yi da abinda nake da iko a kansa. Ta ce." Dakata! Jamilu." Ya kalle ta ido cikin ido. Ta cigaba da cewa." Ai na dauka arziki ne ya kawo ka gidan nan ashe rashin kunya ka zo kayi min." Ya ce." A'a ba nufi na kenan ba. Ta ce." Idan ba nufinka kenan ba mai zai sanya ka dunga wasu maganganu masu kama da jirwaye." Ya ce." Surutai nake ji a gari cewa wai na d'auki 'yata na bawa mahaukaci wanda ba a san daga ina ya fito ba, naga dai ni na hai fi abata, kuma wannan maganar nasan daga gidanan ta fito." Ta tsira masa ido kawai tana kallonsa, ya cigaba da cewa."Kamar yanda na fada da farko cewa." Mutumin nan sanadiyarsa na fita daga cikin rud'ani, to wallahi ko doke-doke yake yana tsince-tsince a bola hakan ba zai hana ni na bashi yarinyar nan ba, dalili ya rufa min asiri na a lokacin da yake daf da tonuwa". Jiki a sanyaye ta ce Allah ya sanya alheri. Ya amsa da "Ameen ya cigaba da cewa." Gobe da sassafe zai zo ya d'auke ta su tafi can abujan inda yake aiki, yayi alkawarin cewa bayan an kwana biyu, zai zo ya dauke ni domin na je naga mazauninsu, na amince da maganarsa dari bisa dari! ke Shahida wannan mutumin daga yau shine uwarki shine ubanki! kuma mijinki, yi nayi bari na bari, ke ki ka ganshi kina so ki ka amince da auransa, saboda haka kada naji wata magana ta biyo baya wannan shine abinda zan fad'a miki." Ta d'aga kanta da fadin." Insha Allahu zanyi kokarin yi masa biyayya Baba a cigaba da yi mana addua'a." Ya kalli Baba Asabe da fad'in." Ko akwai nasihar da za kiyi mata domin tafiya nake so nayi da ita can gidana da wuri za su wuce." Ta ce."Ai ka riga ka gama yi mata nasiha Jamilu ni kuma a suwa! a matsayinka na ubanta ai ka gama komai.'' Ko a jikinsa, ya kalli Shahidan da fad'in " Ki shiryo ki fito ina waje ina jiranki." Ya mi'ke tsaye tare da zura hannu cikin aljihu, dubu uku ya d'auko ya ajiye a gabanta da fadin " Allah ya ba mu alheri.'' Cike da rashin kuzari ta bishi da kallo tana Allah wadai da mugun halinsa. Ta juya ta kalle ta tana zaune ta kasa tashi ballantana ta shirya kamar yanda ya umarce ta. Ta d'an bud'e muryarta da fad'in." Ki tashi ki sanyo mayafi ki bishi Shahida ai magana ta 'kare, ni dai nayi iyakar bakin kokari na akan lamarin, ba zanyi miki baki ba sai dai adduar Allah ya tabbatar da alheri." Wani irin kuka ya kufce mata sai kawai ta rungume ta a jikinta tana fadin." Baba don Allah ki yafe min kada ki k'ulla ce ni, ki cigaba da yi min addua." Tana kuka sosai ta ce " Shahida addua a kanki ai yanzu na fara, ba zan daina ba har sai ranar da Allah ya dauki raina, amma har a cikin raina
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50