Chapter 36
Chapter 36
ta k'ok'arin ganin sun kori mutanan da sukeyi dafifi a jikin motar, da 'kyar suka matsa sannan ya samu ya shiga motar ya zauna amma duk da haka hannu yake daga musu cike da jin dadin adduarsu. Motar tana daf da fita ya hangi dattijuwar matar da ba zai ta'ba mance fuskarta ba. tana tsaye ita ce a kusan 'karshen layi. Baba Asabe ganin yana kallon gurin da suke da sauri ta d'aga masa hannu tana fadin." Alhaji Allah yayi maka albarka hakika kana aikata alheri muna rokon Allah ya kai mizani, Allah ya yi wa dukiyarka Albarka." Ya amsa da "Ameen ya rabbi." Ya kalli Laraban da fadin." Ka fita ka samu daya daga cikin yaran dake wannan aikin, cewa su ware Dattijawa maza da mata a sallame su duba da raunin da suke da shi." "An gama ranka ya d'ad'e." Da sauri ya fita daga motar ya je ya cika umarni ya dawo ya zauna a mazauninsa, Sule ya ja motar suka fita. Sai da suka hau titi sosai sannan ya ce." Ranka ya dad'e "Gadon 'kaya za mu nufa ne?" Ya ce." A'a Adakawa za mu je." Gabad'aya sukayi shuru babu wanda ya sake magana, sai dai Labaran da Sule cikin tunani suke! a duk lokacin da suka shigo garin KANO maigidan nasu sai ya je unguwar Adakawa kuma baya yarda su shiga dashi cikin unguwar a bakin titi yake sauka ya ce su tafi zai dawo gida da kansa. Wannan abu na nasu mamaki mutu'ka! *Tafiya tana kara nisa book1 yana daf da k'arewa! masu himma suna ta biya domin samun damar cigaba da karanta labarin. #500 ba zata gagara ba in sha Allahu. ga account din da za a tura kudin....0542382124...Binta umar gtbank.. idan kati za a turo sai ayi mini magana ta whsap 07084653262 mutan nan nijar za ku tura dala dari katin airtel ku tura mini ta WhatsApp* Allah ya yassare🙏🏻 *MAJANUNI!* (The Unknown Rich Man) NA *BINTA UMAR ABBALE🍒* MANAZARTA WRITES ASSO.. _____ [ 47&48 To a daran ranar Talatu dai da kyar ta iya rintsawa, domin ta jima tana tunani akan al'amarin, ka da fa tana zaune baki a sake yarinyar da ta tsana! tayi mata zarra! tunda gashi tun kafin aje ko'ina Hujaj ya fara yi mata habaici ita da 'ya'yanta, dole ta je ta bincika domin sanin ainihin mutumin da ya ke neman auran yarinyar. Shahida da 'kunci! da 'bacin rai ta tashi. tsakanin Baba da Saliha jira take wani ya ce mata kule tace cas! domin gabad'ayansu a ciki take dasu, saboda suna kiran masoyinta da mahaukaci. Ta shiga d'akin ta same ta a kudindine a cikin bargo amma ba bacci take ba. kawai ta tsirawa rufin dakin ido! Ta d'an bud'e muryarta ta ce." Shahida ki tashi ki karya kummalo mana kina kwance kina tunane tunane mara amfani ko?" Ta mike zaune tana kallonta ta ce." Baba ina neman alfarma a gurinki." Kallonta tayi tana ayyana wani abu, labarin gizo dai baya wuce na koki, amma sai ta ce." To Allah ya sa zan iya. Ta ce." Don girman Allah da darajarsa ki kar'bi wannan al'amari da zuciya d'aya! wallahi nayi imani da Allah cewa alheri ni, nayi istahara akan al'amarin, Baban Baba ba zai cutar dani ba, mutumin kirki ne kuma ba mahaukaci bane kamar yanda ku ke zato, yau ce kawai ta mayar dashi haka, amma tunda ya samu ubangida ya koma mutum kamar kowa, arziki da rashi duk daga Allah suke, kiyi min addua kawai Allah ya sa hakan alheri ne. Gabadaya ta gama kashe mata jiki da kalamanta, a yanda ta shirya ta kuma kudire a ranta cewa sai bayan ranta wannan al'amari zai tabbata, amma wannan maganganun da tayi gabadaya gwiwarta tayi sanyi, babu shakka akwai wani abu da Allah ya rufe, kuma sha'anin aure irin wannan ba'a tsawwala wa domin idan ka tsananta sai ayi babu kai. Ta ce." Shikkenan Shahida na rabu dake da abinda ki ke so Allah ya sa hakan alheri ne dake damu baki daya. Cike da tsantsar farin ciki ta ce." Na gode sosai Baba insha Allahu za muyi farin ciki gabadayan mu, amma ki shirya an jima kadan yana tafe zai zo ku gaisa kafin ya tafi Abuja gurin sana'arsa. Ta na kokarin fita daga dakin ta ce." Shikkenan Allah ya kawo shi lafiya. Zama tayi kan kujera 'yar tsuguno jikinta duk a mace! Saliha ta ce." Baba Lafiya dai?" A sanyaye ta ce." Lafiya lou Saliha al'amarin Shahida da wannan mutumin ne yake ban tsoro. Ta ce." Tuntuni na ce miki ki daina damuwa amma kina kokarin janyowa kanki matsala! duk tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan doka." Ta ce." Na yi fatan alheri ai Allah ya ba su zaman lafiya." Shuru tayi ba ta amsa da ameen ba, kawai ta cigaba da feraye kabewar dake gabanta. ** To kamar yanda Talatu ta kudire a ranta cewa za ta je tayi tambaya a kan lamarin, da asubah zakara ya bata sa'a ta fita can wani 'karamin k'auye ta nufa gurin wani malami, wanda ya duba mata al'amarin ya kuma tabbatar mata da cewa shi bai ga komai ba face alheri domin kuwa babu da na sani ko bak'in ciki a cikin al'amarin, sai farin ciki. Jikinta a sa'bule ta dawo gida da tunanin yanda za tayi ta wargatsa auran. *** Cikin nutsuwa ta fito ta same shi a tsaye a soran gidan, sosai tayi farin cikin ganinsa tsaf dashi cikin shadda bulu mai duhu tazarce har k'asa da hula da takalmi ya dora rigar sanyi a sama saboda yanayin garin sanyi ya fara busawa, ta tsuguna har kasa tana gaishe shi, ya amsa a nutse yana mata wani irin kallo wanda ya sa ta jin kunyarsa ta kasa tashi tsaye. Ya ce." Kin yi min kyau fiye da tunaninki. Murmushi tayi ta ce." Ni ma haka idan na gan ka cikin suttura cike da kamala sai na yi ta mamaki kamar ba kai ba, wanda da yawa mutane suke maka kallon mahaukaci! lallai babu shakka wannan ubangida naka dole a jinjina masa domin ya taka muhimiyyar rawa a rayuwarka, ya sanya ni cikin farin ciki mara mislatuwa domin ni yayi wa tagomashi yayi wa bajinta ba zan gushe ba face na cigaba dayi masa addu'a har karshen rayuwata." Ya dinga jin wani irin farin ciki na kwarara a zuciyarsa, ya ce." Za ki gaisa da maigidana insha Allahu sai kiyi masa godiyar alherin da yayi miki, duk da cewa yana da labarinki amma lokaci kad'an ya rage ku gaisa da juna da ikon Allah." Ta mi'ke tsaye tana gyara mayafinta da ya sauka a kafadarta ta ce." Ina fatan zuwan wannan rana. Kawu Musa ne ya shigo da shirin zuwa kasuwa a tare dashi. Ya tsaya suna gaisawa babu yabo babu fallasa yake kallon mutumin, shima mamakin sauyawarsa yake, kamar bashi ne wannan mahaukacin ba mai yagaggun kaya da kwanciya cikin 'kazanta. Ya ce." Ai babu damuwa mu je ciki sai ku gaisa sosai tsayuwa a soron bashi da amfani." Cike da jin dadi ya ce." Na gode sosai Kawu." Ita kuwa Shahida babu wanda ya kai ta jin dadin ganin yanda Kawu Musa ya saki fuskarsa su gaisa da Masoyinta cikin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50