Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 50

Chapter 50

Majanuni Book 1 Complete Hausa Novel 679 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

haushin abinda yayi mata jiya. Sule ya risina tare da mi'ka gaisuwarsa, ya amsa hankalinsa na kan wayar dake hannunsa. Sule ya fara 'kokarin zuba masa abinci, sai ya dakatar dashi tare da bashi umarnin tafiya. Ya bi umarni cikin sauri ya kama hanya ya fita. Ta kai minti biyar a tsaye tana dawurwura! kafin ta yanke shawarar zuwa ta gaishe shi. Duk abinda take yana kallonta ta gefen idonsa. A nutse ta tsuguna da fadin." Yallabai ina kwana ka tashi lafiya?" Ya d'an saci kallonta da gefen ido kafin ya amsa a ciki, wanda yake da tabbacin ba lallai ne ta ji ba. Itama ganin bakinsa ya motsa yasa ta mi'ke tsaye zata tafi. Kawai ta ji sunanta rad'au! a bakinsa. Ta ja ta tsaya tana kallonsa gabanta na bugawa. Da hannu ya nuna mata gurin zama. ma'ana ta zauna cikin d'aya daga cikin kujerun dake gurin. Kasa zama tayi, domin tana ganin kamar hakan bai dace ba. Ya bud'e muryarsa yanda za ta ji sosai ya ce." Ki zauna nace ko bana son gardama." Ganin yayi maganar da yanayi na bacin rai! yasa taji wani iri kwata-kwata ba taso ta 'bata masa rai! Ido cike da ruwan hawaye ta ce" Kamar hakan bai dace ba. "Ni na baki umarni." yafad'a yana tsatstsare ta ido! A sanyaye ta ja kujera ta zauna amma ta gagara kallonsa, bayan kwarjinsa sai mugun 'kamshin turaransa da duk ya cika gurin. sai jikinta ya sake mutuwa ta dinga wasa da hannayenta. Muryarsa ya bud'e sosai tare da kiran sunanta. Ta amsa tana d'an kallonsa, kafin ta sunkuyar da kanta kasa tana sauraran abinda zai biyo ba. Ya ce." Ya hannun naki?" "Da sauki." tafada a ta'kaice! Gurin yayi shuru na minti uku. d'ago kanta tayi ta ritsa shi ya 'kura mata ido wannan karon ma idonsa ya sauya kala yayi ja! tare da 'kan'kancewa! sosai ta shiga rud'ani! sam bata 'kaunar wannan kallon da yake mata. Ta tsinkayi maganarsa yana cewa; 'Kin san kina da kyau kuwa ?" Shuru tayi ba ta iya magana ba, sai mugun mamaki! da yake kasheta. Ya sauke ajiyar zuciya mai zafi! kafin ya sake bude muryarsa yanda za ta ji ya ce." Zuba min abinci." A hankali ta fara zuba masa abincin tana Allah wadai da wannan hali nasa. shi kuma sai kallon hannunta yake, wannan dalilin yasa duk ta daburce amma dai yau ba ta zubar da komai ba. Bayan ta had'a masa sai ta kalleshi, as'usul ita d'in dai yake kallo! 'bata fuskarta tayi kafin ta ce." Zan tafi Yallabai. Kai tsaye ya ce." Zauna ki ta ya ni ci." Ta kalleshi da tsantsar mamaki a tare da ita lallai ma wannan mutumin da alama bashi da kamun kai Fita tayi daga tsakanin kujerun. Ya kira sunanta, ta kalle shi ba tare data amsa ba. Babu walwala a tattare dashi ya ce." Hau sama ki gyara min gado na. Taji wani irin miyau! ya tsinke a bakinta tsabar tashin hankali. Baki na rawa ta ce." Yallabai kamar hakan bai dace ba, kana yin wasu abubuwan da basu cancanta da kai ba. Ya ce" Na san ke matar aure ce, kuma matar yaro na, to ina so ki sani; shi mijin naki a 'karkashi na yake, dake dashi duk abin iko na ne, saboda haka kada ki sake yi min jayyaya akan umarni na. Jikinta yayi sanyi tana sake tuno jan kunnen da mijin nata yake mata akansa. Abincinsa ya fara ci ba tare da ya sake kallonta ba. Ta saci kallonsa ta gefen ido, sai ta ga babu walwala a fuskarsa. A hankali ta kama hanyar matattakalar bene tana addu'ar neman tsari a zuciyarta. Tsaruwar d'akin sam bashi ne a gabanta ba, babban burinta ta gama abinda take yi ta fita. Tana tsaka da gyara shimfid'ar gadon ya shigo dakin. Gabanta ya tsananta fad'uwa! duk sai ta rasa abinda za tayi, ta dinga sauri tana jere filo sam ta'ki kallonsa sai sanda ta ji kamar yana murzawa 'kofar mukulli (key) sannan ta zabura! ta kalle shi, lokacin ya rufe 'kofar ya nufi inda take.

Table of Contents

Chapters

50 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});