Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 12

Chapter 12

Majanuni Book 1 Complete Hausa Novel 1,205 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

fara tas da ita amma ba ta cika kyau a fuska ba dan Mariya ma ta fita kyawun fuska, to da yake yana da kudi a hannu bai sha wahala gurin siye zuciyar Talatu ba, dama ubanta talaka ne basu da komai koda yaje neman auranta basu wani tsananta binkice ba suka dauki 'yarsu suka bashi. Wannan karon ba'kin cikin da Mariya ta had'iya yafi wanda ta had'iya a lokacin da ya auri Hafsatu, Talatu fitinanniya ce ta ajin karshe gabad'aya ta kanainaiye shi ta hanashi gane fari da baki ita kadai yake gani a gabansa, iskanci iri - iri suke a gidan, Sai ya kasance Mariya ta zama 'yar kallo domin tunda Talatu ta shigo gidan shikkenan ta kar'be girki da mijin gabadaya tsayin wata shida itake juya gidan sai abinda take so za'ayi. Sai dai abinda Talatu bata sani ba shine duk ranar da ta tafi Unguwa shi kuma a lokacin yake samun damar shiga dakin Mariya yayi abinda yake bukata domin duk gigin da yake akanta ba wani cikakkiyar gamsuwa yake samu da ita ba, Yafi samun gamsuwar da yake bukata da Mariya. Cikin ikon Allah ciki ya samu kuma bai bayyana kanshi ba sai da yayi wata biyar, ita Mariyar ta san da zaman cikin a jikinta. kawai tayi masa shuru ne saboda tana gudun ta fada masa ya zubar dashi tunda tana ganin irin k'wayoyin da yake dubgawa matayensa. Aikuwa bala'i ne ya tashi a lokacin da Talatu ta farga da cikin tana kuka tana fadin." Ashe dama yaudararta yake yana kusantar Mariya gashinan har yayi mata ciki amma ita saboda mugunta duk sanda ta samu ciki sai ya bata magani cikin ya zube to dan haka wallahi ba zata yarda ba sai an zubar da cikin Mariya. Budar bakinsa sai yace."Ta kwantar da hankalinta shi wannan ciki ba nasa bane domin shi rabon da ya hada shimfida da Mariya har ya manta. Mariya tana share hawaye ta fito daga dakinta tana kallonsu a tsaye a tsakar gidan sai rarrashinta yake, Tace."Jamilu kaji tsoron Allah kaji tsoron ranar haduwar ka dashi, kai ka san wannan cikin na jikina kai ne ubansa amma ka ke shegenta shi. Ya nuna ta da yatsa da fadin." Rufe min baki munafurka Allah ta'ala har yaushe na kwanta dake da zanyi miki ciki ban yarda ba tun wuri kije ki nemi uban danki." Wani irin hawaye masu tsananin zafi suka shiga zuba a saman fuskata, ta dinga kokarin magana amma tsabar bacin rai ya hanata furta komai, a daddafe ta shiga dakinta, tasa hijabi ta fito. Ya kalleta ya watsar da fadin." Duk in da zaki tafi kije domin kuwa ba zan yarda da wannan cikin ba. Talatu zuciyarta tayi wasai dama babban burinta Mariya ta fita ta bar mata gidan ita kad'ai. Tsakanin Baba Asabe da Hujaj! rigima aka tafka ba kad'an ba! domin kuwa Baba Asabe cewa ita ba zata yarda da wannan 'kazafin ba sai ta maka! shi a kotu a maimako ya risina ya bata hakuri domin su samu daidaito a tsakaninsu, sai ya k'ara fusata yace idan kotun k'oli zata kai k'ararsa taje ta kai babu abunda ya dame shi. Baba Asabe kai tsaye kotun musulunci ta nufa ta d'auki lauya ya tsaya mata suka fara bugawa, da yake ita gaskiya duk inda take sai ta nuna kanta a take asirin Hujaj! ya tonu domin kuwa duk wanda zai bud'i baki a gurin ba zai fadi alkairinsa ba sai sharrinsa. Alk'ali ya tabbatar da shedu daga bakunan jama'a a take ya yanke hukunci kan cewa dole Hujaj! ya amince da wannan ciki domin addinin musulunci ne ya amince da hakan, koda bashi yayi cikin ba tunda har ya kasance a gidanshi a ka sameshi dole ya dauki d'an da za'a haifa a matsayin d'ansa, bayan haka kuma dole ya cigaba da kula da matarsa da cikin da take dauke dashi, Ci da sha da kula da lafiyarsu duk yana rataye a wuyansa. Mai sharia ya gama yanke hukunci ya buga katako alamun hukuncin ya tabbata, ya mi'ke. kotu ta tashi kowa na fadin albarkacin bakinsa. Bayan kwana uku ya samu takarda da biro ba tare da tunani da tsinkaye ba ya rubuta saki har uku da kansa yaje ya har gidan ya bada takadar ya futo abunsa. Baba Asabe ba ta iya karatun hausa ba, ita Mariyar ita ta karanta takardar a take a lokacin ta fadi a gurin, hankalin Baba Asabe ya tashi a wahalce aka kaita asibiti taimakon gaggawa akayi a kanta domin kuwa jininta ya kai k'ololowa gurin hawa. Haka Baba Asabe ta dinga kai kawo ita kad'ai dan ma dai tana da kudi a ajiye shiyasa ta samu saukin wasu al'amuran. A takaice sai da Mariya tayi sati uku a kwance a asibiti ta samu sauki likita ya dora ta akan magani tare da sharad'ai masu tsauri domin kuwa. hawan jini ga mace mai ciki babban matsala ne. Baba Asabe ta sake yun'kurin shigar da kara kotu domin tun sanda alkali ya yanke hukunci Hujaj! bai ta'ba zuwa ya kawo naira biyar a cikin abunda alkali ya yanke masa ba. Kawu Musa d'anta shine ya hanata yace ta bar maganar kawai su barshi da Allah domun duk yanda take tunanin Hujaj! ya wuce haka shaid'anin mutum ne, Sharia dashi bata da amfani. Baba Asabe ta hakura ta bar maganar suka kyaleshi da mugun halinsa, Bangaran Mariya kuwa sai addua domin ita kadai ta san irin kuncin da take ciki bata ta'ba tsammanin Jamilu zai tozartata irin hakaba. Allah al-musauwiru wanda bashi da tamka, ya fara saukar da ishara akan Hujaj! kasuwancinsa ya tsaya duk abinda ya ta'ba sai ya lalace ta kai ta kawo idan ya fita kasuwa haka zai wuni babu wanda zai zo gurinsa da niyyar sayan kayansa, Idan zai tafi gida sai ya ci bashi domin kuwa idan yaje gida babu kudi a jikinsa zasu kwana suna tafka rigima da Talatu. Wani abokinsa ya jashi gurin wani malami domin yayi masa duba acikin al'amuransa yaga abunda yake kai kawo. Kai tsaye malamin yace."Matarsa da ya rabu da ita itace mahad'in arzikinsa saboda haka idan yana so arzikinsa ya dawo tilas yaje ya dawo da ita gidansa. Jin wannan magana sai hankalinsa ya tashi ya dinga share zufa yana tunanin yanda za'ayi ya cigaba da zaman aure da Mariya bayan yayi mata saki uku. A hanyarsu ta dawowa gida Alhaji Shu'aibu ya kalleshi da fadin." Ya hujaj! naga duk ka tashi hankalinka wannan al'amarin fa duk mai sauki ne." Ya kalleshi cikin damuwa yace."Alhaji Sha'aibu ya kake kiran wannan al'amari me sauki saki uku fa nayi mata ta yaya zan aureta dole sai ta auri wani sannan zata hallata a gareni." Alhaji Sha'aibu yayi murmushi da fadin." Yanzu dai mu bari ta haihu akwai shawarar da zan baka." Yace." Alhaji zama cikin kuncin talaucin nan ya isheni wallahi." Yace."To ya za kayi kaine kayi ganganci ai irin wannan ba'a yanke hukunci kai tsaye sai mahukunta sun duba maka abunda ya dace da rayuwarka gashinan ka saketa ba tare da ka san itace abokiyar arzikinka ba." Hujaj! ya girgiza kai da fadin." Wallahi sharrin zuciya ne amma nan gaba dole na kiyaye a yanzu dai burina ta dawo hannuna ko

Table of Contents

Chapters

50 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});