Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 9

Chapter 9

A Bakin Aurenki Book 1 Complete Hausa Novel – Salma’s Painful Return 1,264 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

d'aura ma kanshi abinda bazai iya ba,bare daga baya ya dame shi. Kawai sai ta toshe k'unnenta gun su mama,komai ta samu ta samu,wanda ta rasa tasan bai da hali. Mamaki kam Ja'afar ya bama su mama, dan ak'wati shidan nan y'ar yayi sai da aka bat'se ta da kaya, ga uban _cosmetics_ har a jakar Ghana must go. Aciki da swiss d'aya, holland biyu,engla biyu,sai su code dav'ior,sauran kam duk kana na ne su dangin material. Salma baki har k'unne jin ba wanda ya kushe a dangin sai d'ai ace na Ummi yafi t'sada. Anyi biki lafiya kowa ya wat'se an bar amare da halin su a gidan su. Kauna ziryarta taga gun Ja'afar mai t'sayawa a rai,sosai sukai amarcin su cikin kula da tarairayar juna,musamman ga Ja'afar d'in. _kitchen_ tare,wanki tare,shara tare,duk aiki in dai ba ya fita bane yana a makale da Salman sa, d'uk wata kulawa tana ganinta a gun Ja'afar,shi yasa sai abinda yace take aiwatarwa matukar bai sa6a Shari'a ba. Yadda ta fuskanta ma kamar bai kaunar tai nesa dashi,koh dan ganin har wata biyu kenan da bikinsu amma ba inda taje sai barkar Aunty A'i da makotansu da taje tun tana sati daya da zuwa. Sai dai tai ta jiyo shewar su ta katangar gidan halamar ana ta _chapter_. *Farin Bacin komai* Yau tun tashinta sallar asuba ta kasa komawa bacci,sakamakon tun dare da yace yau ta shirya da wuri zata gida. Dan farin ciki ji take kamar a wani garin zata je musu. Waya tai da Ummi kan zata fito yau gida. Gaban madubi take tana yi tana k'allon agogo har sha d'aya saura. Karar _machine_ d'in Ya Ja'afar taji a kofar gidan,sai ta cigaba da shiryawa. Sallamar shi taji,daga d'akin ta amsa tana fara'a. Yana shiga ya jingina da kofar d'akin yana mata murmushi,ta mudubin ta mishi tana d'auri. Kan ya tako gaban madubin ya t'saya ta bayanta. "Sannu da dawo wa.. Kai ya daga mata,sai kare mata k'allo yake, kayan sun mata k'yau, "Kinyi k'yau... Tashi tai da jin dad'in kalaman shi,sai ta dan ja mishi kumatu kan tace "na gode... Muje koh?.. Ta fara nad'a lifaya. Sai ya rike mata daya gefen tana nad'a dayan da murmushi. Da kanshi ya yafa mata akai ya rufe ko'ina ruf. "Ba dan kin nace sa abar nan ba da hijab d'inki za ki sa zai fi min k'wanciyar hankali.. Murmushi tayi kan ta lang'wa6e kai, "ai ba g'yale bane Ya Ja'afar, Allah ina son lifaya. Kai ya k'ada mata yana d'aukar mata jaka. "Toh naji,amma ni banga maraba ba. Murmushi kawai tai tana d'aukan mukulli. Machine d'in ya karkata mata kirar lifan,a hankali take ko'k'arin hawa sai ya dan girgiza machine din,da sauri k'wa ta dafa kafad'arshi suna dariya. In kagansu g'wanin k'yau suna ta nishad'i har suka zo gida. Tana g'yara lifaya tace "bazaka shiga ba?.. Kai ya girgiza mata da murmushi,"ki gaida su Mama, anjima in nazo d'aukan ki zan shiga, yanzun makaranta zan koma. Kai ta k'ada mishi,kan ta bashi hannu,sai ya bata suka gaisa suna dariya. "Abincin ka yana a kitchen a bisa faranti,na had'a komai, a dawo lafiya... Kai ya daga yana mata murmushi,jin yaki tafiya tace "kaje man.. Kafad'a ya make yana nuna mata gefen fuskanshi, kai ta k'ada mishi cikin kunya. "A layi muke fa... Shima sai ya kada kan tukun ya tada sukai sallama. Har ya kule tana daga mishi hannu,kan tai cikin gida. Da dan gudunta ta shiga tana kiran Mama. D'uk suna d'aki, Ummi an hakimce a kujera ana d'anna waya. "Har kun rigani ashe d'uk saurin nan nawa?.. K'allonta Ummi take ganin tana since lifaya,ga flasks da jaka an ajiye. "A ina zaki zo da wuri,ke dad'i miji ce ai.. Banza tai da ita tana gaida Mama, itama Maman a dan ciki ta amsa mata. D'uk sai taji ba dad'i, jikinta yai sanyi,da murnar ta tazo amma sun dakushe mata. "Sai ya barki ki waiwayo mu?.. Maman ta k'alla, kan tai kasa da kai, "ai na zata irin ta y'an da zai miki,sai kin shekara koh kin fito yawan arba'in.... Baki Ummi ta ta6e,kan tace "d'uk mai irin halin Ja'afar ai dole yai k'ulle Mama,in banda haka wata biyu wai sai yau za kizo gidan ku,ni nazo yafi a girga,wallahi tun wuri ki mawa tufkar hanci.. Dan in kika sabar mishi da haka zai mike. Dagowa tai da niyar yi wa Ummi magana Mama ta tari numfashinta. "Y'ar uwar ki ce,dole ta fad'a miki gaskiya, ke zaki nema mana mutunci a gun miji ki ma ji da k'yau. Kasa tai da kai tana murmushi, duk da a zuciyarta bataji dad'i ba sam. "Mama baza'a a sake ba inshaAllah. Da haka aka ware kuma zancen nawa ta tara a banki. "Ni fa ba'a ban kud'in cefane Mama, komai yana kawo min har katin waya,sai dai in ina da bukata yana cewa na mai magana... Baki Ummin ta ta6e,kan ta zuge jaka, sai ga nan kud'i tumi. "Kinga kud'in cefane na,nima ai ba abinda na rasa,ina ruwana da wani ni kud'in kati? Kawai naji dumus ni... Gashi nan na banki ne dana sa Mama ta sai min. Kai Maman ta k'ada, tabbas Ummi tasan ta kan maza,shi yasa take burgeta sosai. Itade Salma an sata duhu,dan sun raba hankalinta biyu. T'saka mai wuya kenan. By Feenat Ja'afar. 9/29/16, 9:00 AM - Queen Safiyyert馃憫: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 15_Sai dare yazo a dalilin yadda take fad'in bata gama ba,har cikin gidan ya shiga,kawai kuma sai yake ma Mama k'warjini, dan fuska sake ta amsa mishi,kan suka tattara suka tafi. Koh da Salma tazo k'wanciya maganganun su Ummi take ta tunawa. Ita babban haushinta ma yadda aka fa fad'in koh tsoron Ja'afar take. Washegari ma haka ya yakaita gidan su Abban shi,nan ya wuni suka biya gidan Garba. Yau tun (7:30) ya fita, sakamakon an fara jarabawa a makarantu. Sha d'aya ta gama aiki ta fara jiyo hayaniyar y'an unguwa a makotanta,halamun sun hallara za'a fara chapter. D'uk yau sai hankalinta yai gidan,duk da ba sabawa tai dasu ba. Waya ta d'auka,ta d'anna kiran Ja'afar _no answer_.. Ji take kamar ta zaga in ya dawo ta fad'a mishi,sai dai ta daure. Da yamma kam kamar kullum yazo fita shago tace zata leka makota. Jim yai ba amsa,sam tarbiyar matan unguwar bata mishi ba,baya so Salma tai sabo dasu a samu mishkila,amma kawai sai ya k'ada mata kai, "Sai kin dawo. Cike da murna ta rakoshi har bak'in kofa ta koma d'aki. Da sallamarta ta shiga,tun daga bak'in kofar gidan zaka fara jiyo karad'in matan. Da fara'ar su suka amsa,d'uk sun baje a tabarma, wasu ba koh dank'wali. A dan kunyace ta gaida su, dan ganin duk sun girme ta,sai wata mai kamar shekarunta da D'a a goye. Chan hira taci gaba, zabiyar ciki sai karanta musu makamin kama wuyan maza take. Salma tai shiru tana jin su,tabbas babban burinta shine Ja'afar ya so ta har karshen rayuwa. "Su amarya yanzu ai farin take gani kan a juya mata bak'in bayan.. K'allo matar tai,bata gane nufinta ba,sai dai bazata iya tambaya ba. Haka firar yau ta tashi kan makamin rike miji har Salma ta fito. Tunda ta zauna a gida take tariyo firar sun.

Table of Contents

Chapters

41 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});