Chapter 4
Chapter 4
sam wallahi.. A y'atsine Ummi ta harare ta,"ka ga kunya manya,akan wannan mai dan uban d'acin ran kike wannan kumfar bak'in?...baki ta ta6e kan tace "Kin k'wa kama abga in dai Ja'afar ne.... "Ke Ummi... Bana son fit'sara fa,kullum ina sanarki Salma yayarki ce,dole ki bata girma, koh nai mugun sa6a miki.. Maza bata hakuri. Tana chunno baki ciki ciki ta bawa Salma hakuri,ita kam har ta fara hawayen bak'in ciki. "Toh fito ki biyoni.. Mama ta nuna ma ummin kofa da hannu.. *By* *Feenat Ja'afar* Like 路 1 路 Reply 路 Report 路 Jul 20 Feenat Ja'afar Novel's *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 7_Washegari ma ta fito zata makaranta sai gashi shi da abokinshi Garba suna tafiya. Ido ya kura mata ganin tai kasa da kai tana murmushi. Sai ya k'ada kai suka karasa,cikin sanyin murya ta gaida su,Garba kad'ai ya amsa,shikam Ja'afar k'allonta kawai yake yana murmushi, kamar mai son sai sun had'a ido. "Malama Salma fa kar tai latti a mata bulala abokina.. Kasa ta kara da kai tana dan dariya, shikam gogan sai binta yake kawai da k'allo,kan ya nuna mata hanya kan wai su rakata hanya. Ba musu ta wuce suka jera,Garba sai shakiyanci yake zuba musu,murmushi kad'ai ne nasu har suka zo bakin _gate_ d'in islamiyar. Ka'ro na farko suka k'alli juna cikin ido,da sauri ta K'awar da kanta tana murmushi, shikam harda k'ada kai, tuni Garba ya harbo jirgin nasu,sai ya hau shafa ha6a yana k'allonsu,musamman abokinshi da yace bai san so ba.. Hannu Ja'afar ya kai aljihu yana lalube,ita kam sai ta hau satar k'allon shi ganin mey zai yi. Da mamakinta k'wa sai gashi ya fito da naira ashirin yana mika mata. K'alloshi tai tana kunshe dariya,sai ta k'ada mishi kai, "Kud'in tara ne fa Salma, ki k'ar6a ki sai hambididi... Dariya Garba ya fara harda rike ciki,itama wacce take rikewa ta fito fili, sai ta sa hannu a baki dan rufe sautin ta.. Shikam Ja'afar kawai sai ya hard'e hannu yana K'allonsu, musamman Garba yadda yake k'yak'yata dariya. Shikam ba kasafai ya iya dariyar keta ba irin ta Garba,shi yasa wataran yakan kularshi a abu. "La Malam Ja'afar...... Gaba d'ayan su suka juya k'allon mey magana. Ja'afar take k'allo tana murmushi halamar jin dad'in ganin shi, shikam tuni ya had'e rai yana k'allon ina ma ya santa. Kamar tasan mey yake tunani tace *"Bintu*(Na Rufaida Omar) ce,dalibar ka a day... Salma ya k'alla wacce itama ke kallon Bintu,kan ya k'ada kai, "toh Bintu.. Salma Bintun ta k'alla jiki a sanyaye ganin ko in kulan da Ja'afar ya mata,"shiga za kiyi ne Salma? kai ta kada mata, jiki a sanyaye tai gaba Salma ta daga musu hannu halamar sai anjima tana murmushi. Da k'allo ya bita cikin wani yanayi, da ko shi kanshi bazai iya fassara wa ba. Kai ya k'ada kan ya k'allo Garba wanda k'wachokam ya maida K'allonshi kan abokin yana dariya kasa-kasa. Harara ya maka mishi kan ya juya,sai k'wa Garban ya kara sa dariya yabi bayanshi. "An fad'a tarko makal ana hura mana hanci,sai anyi magana kace wani "mey nene so? Ni ban sanshi ba.. Karyan kawai,koh makaho ya laluba yaji ka afka so ai yanzu kam. Chak! Ja'afar ya t'saya tare da juyo wa gun Garba. "Mey kenan haka ke nufi?.. Harara Garban ya k'wada mishi kan yace"kar ka maida ni yaro fa malam,kana nufin baka san kana son Salma ba ko mey?.. K'allonshi kawai Ja'afar ke yi cike da mamaki,a hankali ya furta *"SO"*?... Hararar shi Ja'afar ya kara,gani yake kamar ya raina mishi hankali ne. "Kaga Malam kawai kai saranda haka,tuni tun yadda ka ke ta yawan fad'in Salma nasan a rina,ka bar wani k'wane-k'wane. Shi dai Ja'afar ya t'sunduma tunani maganar Garba,wai So? Salma kuma?. *By* *Feenat Ja'afar* 庐NWA. 9/29/16, 8:56 AM - Queen Safiyyert馃憫: [7/21, 12:28 PM] Feenat Ja'afar: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 8-Har Ja'afar yazo k'wanciya yana tunanin kalaman Garba,tabbas biri yaso kama da mutum, dan yana jin sauyi tun ranar farko da ya dora idonshi a Salma bayan dawowar shi. "So"... Ya furta a hankali, murmushi yai kan ya k'ada kai,dan yana da aiki a gaba,dan bai san kom ba game da lamarin. Tun daga ranar ya zamto kusan kullum da yamma yakan raka Salma islamiya,koh da yana shago zai zo ya ganta kawai,hakan na sashi nishad'i, yau da gobe har ta fara sakin jiki dashi a karo na biyu. Sai ya zamana itama in bata ga Ya Ja'afar a ranar ba batajin dad'i sam,haka zata k'wana sukuku. Shirye-shiryen bikin Aunty A'i suke,duk sun shiga _busy_. Da yamma sun fito bak'in shagunan su Abba siyayyan kayan fitar biki, tasan kuma d'uk layin ba inda ya kai shagon su Ya Ja'afar kawo kayan k'yali, amma da tayi magana Ummi sai ta tanka. Kai duk'e yana duba takaddu,kamar _papers_,chak ya t'saya da abinda ya yake yana murmushi kai duk'e, ajikinshi ya ji kamar Salma na kusan shi,itama dai satar k'allon shi take,tana ganin zai dago tai sauri ta juyar da kai tana murmushi. Fara'ar shi ta karu dan hango Salman. A hankali ta dan kara K'alloshi,sai k'wa suka had'a ido,da azama tai kasa da kai tana murmushi har suka karaso. Tuni Ummi ta had'e rai ganin Ja'afar a shagon,a takaice ta dan harari Salman ganin sai wani munafukin murmushi suke sakar ma juna,baki ta ta6e kan a ciki ta gaidashi tai cikin shago ta barsu nan. _"My_ kanwa,.. Kai ta kara duk'ar wa tana gaidashi,sai ya k'ada kai,ya rasa irin kunyar Salma gare shi yanzu,abu kad'an duk'ar da kai. "Biki ya karato ba? Kai ta daga mishi tana dan k'allon _net_ d'in gefenshi da murmushi. Tashi yai zuwa gun inda take k'alla ya fara saukar mata dasu. A hankali ta tako gun dan zabi,d'uk sun mata k'yau. Sai ta dan kallo shi, "malam Garba fa? Murmushi yai yana k'allonta, "yaje inda aka tura shi _service_ nashi yaga gun,gobe zaki ganshi. Kai ta k'ada, d'uk sai taji ta kasa za6a ganinshi kusa da ita. Kamar ya sani ya kara s'akko mata da wasu. "Bari na tayaki za6a. Kai kawai ta k'ada mishi tana k'allon kayan,kan wani _purple_ idonta ya kai,a hankali ta kai hannu zata ja shima ya kai zai d'akko shi yana fad'in _"purple_ zai miki k'y... Shiru yai ganin itama shi ta rike,ya rike rabi ta rike rabi. D'uk sai suka k'alli juna ba koh kiftawa da wani yanayi... Tamkar wanda aka lika _poster_ a gun haka suka kame da k'allon juna. Ummi ce ta kat'se su da fad'in "Ga nan wasu materials y'an leda Salma masu kaman _lace_.... Shiru tai ganin wani ikon Allah,baki sake take k'allon su,tuni Salman ta sakar mishi tai baya tana sunke kai da murmushi tare da amsar kayan hannun Ummin tana sunyi k'yau ba dan ta gani ba. Murmushi ya sakar mata shima,har yanzu yana rike da _net_,ya rasa mey ke damun K'wak'walwar shi akan Salma. *By* *Feenat Ja'afar* [7/21, 8:05 PM] Feenat Ja'afar: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 9_Baki ta dan ta6e,kan a y'atsine tace ma Jafaar d'in "mun zabi wannan, zamu nuna ma Baba sai ya bada kud'in. Murmushi yai yana k'allon gun Salma,itama idonta na kusan hannunshi. "Koh na tafi ne Salma? K'allo Ummin tai,kan ta k'ada kan
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41