Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 36

Chapter 36

A Bakin Aurenki Book 1 Complete Hausa Novel – Salma’s Painful Return 1,267 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Ido kawai ta sa mata,kan tai kwafa tai d'aki,da gudu itama ta bita tana kukan bazata ba Salman ta rufe kofarta ta batta da bugun "Antee,Antee bata cho. Anan tai ta mitarta tanaji daga dakin tana "Ai sai kinje... Tuni ta kara jiniya, kuka harda shudewa amma tai burus da ita tana kwalliyarta. Zuwa chan taji shiru,sai tai murmushi, Miemie matsala. Fito wa tai dan ganin koh fita tayi,sai ta ganta kwance bakin kofa sai sauke ajiyar zuciya take tai bacci. Sunkuyawa tai ta leka,ido har ya kumbura, duk sai ta bata tausayi,batasan lokacin da ta d'akko abarta ba,batajin tunda Miemie take ta ta6a dukanta haka tai kuka. Kwantar ta tai a gado tana goge mata fuska da tissue,baki ta kai fuskarta, "am sorry kinji... kamar ta sa kukan itama,Miemie taurin kai toh,Alhaji hancini,ya suke so tayi da ranta ne? By Feenat Ja'afar. 9/29/16, 9:34 AM - Queen Safiyyert馃憫: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 40_Washegari bayan la'asar tace mishi zata maida Miemie gidan Mama dan Allah ya batta taje daga nan sai tai barkar Ummi data haihu cikin dare. Da har zai hana,ganin kayan Miemie a akwati yasa bai gardama ba ya batta,kwarai tasha mamaki,dan rabonta da fita har ta manta,amma dake wacce bai kauna za'a mayar ya batta. "Ga driver in kin gama ya kaiku,kar kuma ki dad'e.. Kai ta daga tace ta gode. Rayuwa kenan,da ya batta ma taji dad'i,koh ba komai zata leka gida yau. Gidan Ummi suka fara zuwa,sai ta6e baki take tana korafin yadda ta zama matar k'ulle. "Aure sama da shekara wannan ne zuwanki na biyu gidana,wannan wace iriyar rayuwa ce,mutum sai shegen kullen t'siya.. Tana jinta tai shiru,tana tunanin hali irin na dan Adam,mai wuyar gane hali,lokacin Ja'afar mai barinta fita haka ta gurza,yanzu kuma ta had'u da dai dai kowa,ga kud'i ga cima, amma ba fita ba haihuwa.. Zaman lafiya wai yafi zama Dan Sarki. Ita kanta Miemie murna take sun fita yau,sai dai suna zuwa gidan Mama taji Salman na maganar zamanta ta d'ane cinyarta ta riketa tam. Ban6are ta Mama take ajikinta tana ihun kiran Aunty,ita kuka Salma kuka, ga magriba ta sawo kai. Suna haka Abba ya shigo, duk ta rike gyalen Salma kam tana ihu. Dak'yar ta fizge tai hanyar fita da gudu tana kuka. "Subhanallah... Ta shid'e fa wannan... Chak ta tsaya jin daina kuka Miemien,da sauri ta juyo taga Abba na jijjiga ta. Ba shiri tai gun dai dai Miemien ta kawo wuta ta kar6e ta. Kuka na fitar hankali take tana bata hakuri, ''Ni bansan mey yarinyar nan zata tsare miki ba in ta zauna achan gunki ba,kullum sai da kuka koh jinya za'a rabu?.. Ki bar y'arki a kusa dake man tunda ita mai kulafuci ce... Kai ta daga tana share ma Miemien hawaye tana tai shiru toh.. Dole tana ji tana gani ta koma da Miemie, dan yau fir taki yadda tunda ta d'andana zama da ita. Kanta take shafawa,ita kam ta tasata gaba tana ta kallo ba koh kiftawa. A hankali tace "Miemie.. Idonta a kan Salman tace "Uhmm. Kwanto wa tai a gefenta tana g'yara mata kwanciya, kamar wata babba ta fara mata fad'an ta zama mai ji dan Allah. "Ban san matsala Miemie, ki rufan asiri ki daina halin nan naki na kumbura ma mijina baki,kinji?.. Kai ta daga mata kamar gaske. Sai tai murmushi tai kan tace ta taso suje suyi girki a kitchen. Shikam Alhaji da murnar yau Miemie ta tafi ya shigo gida,shi kanshi ya rasa mey yarinyar ta tsare mishi a gidan,duba ga su Ja'afar na gidan. Sai dai tun daga bud'e kofar parlourn farin cikin ya kau. Dariyar Miemie ya fara cin karo yana shigowa ta kitchen,dan haka da sababi ya isa. "Mey ya zaunarki har bayan magriba baki dawo ba?... Mey kuma ya dawo da wannan? Duk ido suka zuba mishi,mai hali kuwa Miemie tuni ta chunno baki gaba tana mishi wani irin kallo jin ya fara sababin nashi. "Wallahi har kusan suma tayi dan kuka yau,tausayi ta bani shine na dawo da ita,kai hakuri duk ita tasa muka kai magriba. K'allon Miemien yayi da kamar harara kamin ya kad'a kai dan takaici ya fice. Ajiyar zuciya ta saka,ta tsalake rijiya da baya da k'yar,kan ta dawo kan Miemie ita tuni har ta cigaba da sabgarta. Sai dai ana zuwa kwanciya yace daga yau Miemie zata bar kwana dakin su,koh ta koma kasa. Ya ta iya,dan a zauna lafiya ta sauke Miemie kasan,dan ba yadda za ai ta luluka yarinya chan wani waje ita tana wata jahar,a ganintq Miemie nawa take. ******* Fur yanzu ta daina ganin fuska gun Alhaji, in ya shigo ba wanda ya isheshi kallo,asalima ya daina zama bangarenta sai cin abinci koh bacci. Yau dai ta d'au damarar fara koyawa Miemie sabo da Alhaji. "Abba ki ne kinji Miemie nah?.. Ki dinga mishi oyoyo kina mishi dariya kinji?, banda harara,banda turo baki,kina ji na? Shiru tai tana binta da kallo kawai,chan sai ta yak'e mata hakori. Cikin farin ciki Salman tace "yauwa,koh ke fa,be a good girl ba? kai ta daga mata tana dariya. Alhaji yai wanka ya shirya yaje parlour yana duba abu a system nashi su kuma suna daki gun shirya Miemie. Daga parlourn ya kwada ma Salma kira wai ta fito mishi da agogon shi na kan mirrior. Murmushi tai ta k'alli Miemie,tasha parking da ribbon sanye da gown ja da baka iya g'wiwa, dake fara ce sai tai mata k'yau sosai. Agogon ta d'akko ta kamo hannun Miemie, "Kai ma Abba a maza yana parlour,ki nutsu dan Allah kinji Miemie nah.. Kai ta daga tana dariya ta karbi agogo tai parlour. Bayanta ta biyo dan ganin ya zata kaya, daga yau ne zata fara koya musu kusanci da juna shi da Miemie. A dunkume ta isa gunshi yana duba abu a laptop, mika mishi tayi ba koh magana, sai ya dago ganin itace,tai mishi kyau sosai,ga sai kamshi take,ba abinda ta bari na babanta a ganin shi har dacin ran,in baxai manta ba yanzu ne zata shiga shekara uku,amma duk ta tara dacin rai wai da fitsara. Kai ya d'auke ya cigaba da abinda yake, Salma har ta fara murna ganin bai mata dan halin ba yau. Ita kwa Miemie sai ta ajiye agogo kan hannun kujera ta juya tsautsayi agogo ya fad'o kasan tiles sai glass din ya fashe. Da azama ya juya,ganin agogon akasa a fashe Miemie ta juya ta mike ya fara sababi. "Duk wani mugun hali irin na ubanta yarinyar nan ta iya,agogon nawa zaki saka da gangan ki fasa min?.. Waje Salma ta fito ganin ya yo kan Miemien a sukwane, duk tana k'allon abinda ya faru. Kumatun Miemien ya ja tare da kai mata rangwashi akai yana sababi,tuni ta hau kuka jin zafin abin,da sauri Salman ta karaso dan bashi hakuri. "Shegiyar yarinya kawai,kin san kud'in agogon da kika fasa kuwa?.. Ja Salman tai ta tsaya tare da rintse ido. Ga ihun Miemie tana kiran Aunty,ga sai zagin y'arta yake harda sheganta mata ita? "Alhaji.. Cikin fusata ta kira shi tare da bud'e, Rai 6ace shima ya dago da niyar huce haushin shi kanta ta rigashi. "A gaskiya ka daina sheganta min yarinya, dan da ubanta gaskiya,haka kawai, ina

Table of Contents

Chapters

41 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});