Chapter 20
Chapter 20
BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 26_Kowa bin kofar dakinta yai da kallo, yana murna ba'a rikicin mata biyu a gidanshi yau gashi an fara,dole ne tun wuri yai ma tufkar hanci. Har yayi dakin Salman sai ya t'saya, dole ne ya nuna mata kuranta, in da tai mishi fitsara ya k'yale toh yanzu bazai d'auka ba,dan ba ita kadai bace a gidan,kawai sai ya juya dakin Bintu. Kuka take yana ta fadanshi taki kulashi, chan kuma sai ya sassauto, "Ni tashin hankali ne bana so a gidana ne,tun wuri ma in zaku had'a kai ku had'a, dan ba mai chazan hawan jini. Kai ta dago tana mishi k'allon tuhuma, "Au shine dalilin da yasa ka fad'a wa matarka baka so na?.. Ni nace ina son ka koh?.. A haka za ai zaman lafiyan?.. "Ke kinga bana son iyayi,dawa nai wannan zancen?.. Da sauri cikin kuka tace "da matarka man,wato harda fad'a mata kwantai nayi nai ma tallan kaina.. "Ban san anyi maganar nan ba Malama,ki ma cire zargin ni na fad'a mata, bari na je zata fad'a min yaushe muka fara y'ar sharri da ita... Waje yayi zuwa dakin Salman. Kai Bintu ta k'ada, "ashe munafuka karya take dan ta had'ani fad'a da Miji,toh karyarki taci karya,Allah sa ya k'wada mata mari tukuicin sharri. Ita kam tanajin bud'e kofarshi ta mike tare kama k'ugu ta k'ank'ance ido. "Salma yaushe muka fara y'ar sharri dake a gidan nan?.. Yaushe nace miki Bintu ce tai min tallar kanta na aura?.. Harara ta sakar mishi da k'allon kar ka rainan hankali. "Ka nad'e taburmar kunyar ka man ta haka,wato kayi amarya shine ka zabi ka tuzartani agunta,karafkaf abinda ya faru ta fad'a mini,toh da ka fad'a mata saura igiya daya ta aurenka a kaina sai mey?.. Baki ya saka cike da mamaki,lalle ya shiga tarkon kaidi na mata, wato kowacce sharri take neman k'ulla mishi a gun y'ar uwarta ashe?.. Bai da tace wa, kawai sai ya juya zai fice, da sauri tace "a ka fita man,dan nayi imani bazaka karyata cewar ba kai ka fad'i ba... "Idan kuma habaici da iyayi kake neman matarka ta dinga min dan ka huce haushinka na da toh bissmillah,dai dai nake dana sa kafar wando daya da kowa a gidan nan wallahi.. Juyowa yai yana kallonta, sai tai d'aki ta barshi t'saye baki sake. Titi ya fice ko ya samu sa'ida, lalle yau ya jinjinawa sharrin mata,amma kaf yafi jin haushin Salma,dan sam yanzu ya fuskanci fitsararta tafi ta da yawa. Tun daga ranar ba jituwa t'sakanin matan, daya in Bintu ta fad'awa Salma sai ta fad'a mata dubu,daga karshe ta bige da kukan bakin ciki, har mai gidan yazo ta kit'sa mai karya da gaskiya,wani sai dai ya bata hakuri, dan a ganinshi yanzu Salma tafi karfinshi,dan da ya mata magana ita y'ar dika take,daga shi har amaryar zata chake tass, sai dai yai abinda zaiyi. Shi yasa shi kuma ya t'siri mata t'siya,in dai zata kona mishi rai,toh shi kuma zai ta biyewa Bintu suna ta mata feleke a t'sakar gida, daga karshe kam sai yaci nasara,dan haka zata shiga d'aki tai ta kukan bakin ciki,a nan zai ta mata dariyar keta. ***** Sallama taji kamar ta Maman Ummi da Maman Abba,lekawa tai ta window, sune kuwa, "munafukan Allah ta'ala kawai... Ta fada tana kokarin ta fito rai 6ace,dan tai imani duk abinda take fuskanta yanzu da sa hannun su aciki... Chak! Taja ta t'saya rike da labule a hannu ganin Bintu ta fito da gudu danjin sallamar su. "Sai yau Aunty Ladi zaki zo min? Har nayi fushi ai.. Baki sake Salma take k'allonsu,tana k'allon suna nuno kofar dakin da baki suna ma Bintun kuskus tai baya da sauri. Ido ta rint'se tare da cije le6e,lalle mutum mugun ice ne,yanzu ta gane inda Bintu ta samo duk wasu _information_ na zaman aure nata ba agun Ja'afar ba,ido ta bud'e, ta d'au alhakin Ja'afar, har rantsuwa yai mata amma taki yadda. Karshe har raba shimfida tai dashi akan maganar har sai da ya gamo ta da Aunty A'i aka shirya. Zama tai tana jiyo shewarsu a dakin Bintun. Har kullum bazata daina nadama akan taraiyarta dasu Maman Ummi ba,tasan duk fushin Ja'afar ne da t'sinuwar mala'iku ke bibbiyarta. Har hawayen bakin ciki tayi yau,tai kuma alkawarin daina sa6awa mijinta ko da taji haushin shi. T'sakar gida ta fito bayan ta g'yara fuskarta, tai sa'a kuwa sun fito zasu tafi suna ta dariya. Ganinta a t'sakar gidan yai bala'in saita nutsuwar su,a t'saye take k'yam tamkar wata soja ta had'e rai tam,ido cikin ido take k'allonsu,tuni suka hau inda-inda, "dama kina ciki?.. Sannun ku da gida.. Harara ta sakar musu,ba shiri sukai hanyar waje,Bintu ce ta t'sayar su, "bari na raka ku hanya Aunty,ina zuwa na kira mai gida izinin fita. Duk tana k'allonsu,har tai ma Ja'afar waya wai za tai rakiya waje ya bata izinin fita. Bokiti ta zaburo da sauri tai hanyar fita,da sauri sukai waje sun zata kansu zata iyo,kawai sai ta ja t'saki ta shige band'aki. "A toh na zata koh rafka mana zatayi ai,g'wara muyi ta kai ta kai,dan wannan da gani zatai kishin hauka... Dariya suka sa tana jiyo su ta band'aki daga zauren sunki tafiya. Ruwanta na cika da ta tara ta bud'e band'akin a hankali tai zaure, basu nufa ba sai jin saukar ruwa sukai akansu har Bintun. Bokitin ta d'auka tai kansu dashi a sukwane, da ture ture suka fita waje da gudu. Tana haki ta leko kofar gidan ''Ashe karyar munafurci kuke, da ku t'saya na g'wada muku aikin mahaukaciya, shegu gadon na aiya,a haka zaki kare Maman Ummi wallahi, InshaAllah kema dubinki ta kusa cika. "Ke kuma yau mai rabani dake a gidan nan wallahi sai Allah, yau zaki ga karyar iskanci. Gida ta koma tana hakin daga ruwa bucket guda da tsohon ciki. A t'sakar gidan ta zauna tana maida numfashi a hankali, ta jima da zama kamin taji tafiyar Bintu cikin sand'a, kofar ta zubawa ido tana harara, kai ta leko dashi dan ganin koh Salman bata nan sai suka had'a ido. "Wallahi baki isa ki ce zaki hanani shiga ba, in gaske ne ki bari na shigo na shirya in fad'an ki ke nema dani ba hauka ba. Murmushi tai daga inda take, "Lalle kinyi kuskure in kina zatan zan iya had'a jiki da karya irin Bintu,haukar nake son sauke miki aka yau ai, gaba kin d'aina irin kuskuren nan ina zuba miki ido kawai,yau dole na fidda ki cikin gona ta. Like 路 1 路 Reply 路 Report 路 Jul 31 Feenat Ja'afar Novel's "Karya ki ke wallahi ki iya koyan hankali Salma,ai fad'a da makami tsoro ne,ki ajiye bokitin mu gabza da hannu in kin is... "Meye hakan ke kuma Bintu?.. Juyawa tai da sauri,tana ganin Ja'afar ta sau kukan munafurci harda kank'ame shi,wai Salma tace in ta shigo sai ta kashe ta da duka da bokiti bayan ta jika su ita da bakin da zata raka... Ciki yai gadan-gadan gun Salman,tana ganinshi ta mike t'saye rike da bokiti,bai watawataba kawai yai kanta da niyar mari tai baya. Kunci ta rike har tana halamar yin baya zata fad'i, "Kin haukace ne Salma ko mey?.. Gidan ki ne da har
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41