Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 11

Chapter 11

A Bakin Aurenki Book 1 Complete Hausa Novel – Salma’s Painful Return 1,259 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

mishi,burinta ya fita ta fice, amma fur yaki. A jima kadan ta k'alli agogo,kafarta har kaikayi take,da ya k'allota ta sai ta sau mai murmushin dole. Kamar ya kula sai yace bari yai wanka,yau sha biyu yake son yaje shago. Ita dai ta samu ya fice,Allah koh satar hanya sai taje gidan sunan Maman Abba. Toh sai ma ya barta harda mika mata ledar riga ta barka. Abu kamar gaske Salma kamar anyi hankali, sai hali ya dawo sabo. Shiga makota kam Ja'afar har yai hakuri ya zuba ma Salma ido, Gashi yanzu su Salma har ketare ana t'sallakawa,kusan duk yanzu unguwar sun san da Salma,ga surutu da t'sabar manyance da ta koya zama cikin manya. Ranar Garba suka zo gidan a 6ame da mukull,sai ya d'au waya ya kira Ja'afar din. "Ba kowa fa a gidan nan Aboki,dan da mukulli a 6ame.. Daga chan Ja'afar yai t'sam, kan yace "oh,sorry pls,na manta tace zata je dubiya, ga wayanta ba chargy... Kai Garban ya kada "toh dai mun fita,dama ita ke mitar madam shiru,yanzu kam ma had'u suna. Murmushin dole ya k'akalo,yana cewa ace Billy tai hakuri. Bayan sun gama ya ajiye waya,Salma tasa ya tafka karya,dan da abin kunya ace yana mai gida amma bai san matar gida bata nan ba... Toh mey zai wa Salma ne?.. Ya mata d'ukkan nasiha,yayi fad'a, yai lallami,amma tamkar a iska yake zubawa. Sai tayi kamar ta d'aina, gobe ta fidda sabon hali. "Assalam Alaikum... Kai ya dago,ganin mey sallama yasa ya fad'ada murmushin shi, cikin girmamawa yace "a Abba,sannu, yana sunne kai, murmushi Abban yayi,kan yace ''yauwa Ja'afar,ka ga na dawo,zan dan zaga ne, baya,dayan shagon nan ba kowa ne, nazo arar Sadi minti biyu.. Kai kasa yace "Bari na zauna kan ka dawo nan bana komai. Yasan zai samu ma damar yau amar da abin da ke ranshi. Yana shagon Baban ya k'wance ya d'aure, ya fad'a ya je gida ya shiga uku gun Salma.. Shawara d'aya ya yanke, gun Mama, dan yaga ita batta zafin Baban. Tun yamma ya tashi,bayan sun gaisa da Maman faran faran yake sanarta halin da Salma ta t'suro mishi. Kamar abin kirki harda bashi hakuri,da fad'in zata t'sawatar mata. Sai d'ai tana fita Ummi da tun shigowarshi tai zamanta a d'aki ta fito. "Kai amma mama mutumin dan rainin hankali ne,wai kinji fitar Salma tai yawa? Matar da sai tai sati biyu wataran ba tazo gidan nan bama bare har fitar ta tai yawa.... K'wafa Maman tai,kan tace "ke lefin shi ki ka ga?.. Ai lefi na gun Salma da ta zauna yake juyata kamar waina... A zamanin y'ancin kai ake yanzu, bana tsawalawa dana.. Kaza kaza,har Abba ya shigo zaure ya dan t'sinci wani zancen,amma bai gane kanshi ba. Kullum Ja'afar na sa ran yaga Salma ta sauya,sai dai shiru,sai yai tunanin fad'an Maman ma bai shige ta ba. Ranar Garba yace a gidanshi zai magriba yace Salma tai musu irin gurasar nan tun tana amarya. A gabanshi ya kirata, a lokacin an zube ana ta firar kashe wando a makota bayan layinsu, Koh da ta sauke waya ta cigaba hirarta. Chan kusan magriba ta kusa ta tuna da zancen Ja'afar,kusan ma d'uk y'an firar an wat'se amma Salma matar gida ta riketa wai suna firar su zata tafi? Yaron gidan tasa yai gudu bayan layinsu ya siyo mata gurasa mai siga ta karbi kud'i gun matar gidan. Cikin nishad'i suka zo sai dai gida a 6ame,ga yau ta bar mukullin shi a ciki. Ranshi in yayi dubu ya 6aci,basu jima ba sai gata tanan,duk tabi ta burkice, duk da koh k'allon inda take Ja'afar bai ba. Sai da Garba take magana tana ko'k'arin bude gida. By Feenat Ja'afar. Like 路 2 路 Reply 路 Report 路 Jul 25 Feenat Ja'afar Novel's *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 17_Shi dai Garba har suka shiga gida yana zungurar abokinshi kan ya saki fuska. D'aki ta shiga tana mai adu'ar Allah yasa a samu gurasar nan,in ba haka ba yau ta kad'e har ganyenta a gun Ja'afar. Suna t'sakar gida suna alwalar magriba sai ga yaro yai sallama rike da k'wano,da sauri ta fito ta amsa,har ta shiga Ja'afar na bin bayanta da ido,k'wafa yai kamin yai ciki, shi dai Garba duk ya gane da wata a kasa. Kitchen ta sameta tana jera su a faranti. Tasan shine amma fur taki daga ido ta k'alleshi. "Nagode Salma, kinji? Na gode,amma ba zanci gurasar titi ba ki sani... Kofar kitchen din ya rufo sukai waje. Ita kam koh a jikinta,tunda de ta t'sallake fad'a ai shikenan. Yau dai ya kasa d'aurewa, har sai da ya sanar da Garba halin Salma ba ragi. Sosai yai mamaki,wai Salma ce da halin nan? Sai dai kawai ya bawa abokinshi hakuri, da kuma ya rage saurin fushi... Haka ya wuce gida ba tare da shima yaci ba. Da dare ya d'au pillown shi ya koma parlour,baki ta ta6e tai k'wanciyar ta. Sai dai koh minti ashirin ba ai ba ta hau juyi,ta ture pillow,dan Allah yaga bata saba k'wanciya ba'a hakarkarin Ja'afar ba,duk fad'a kuwa. Ba shiri tazo bada hakuri dan tasan ya bala'in jin haushi. Shi kuma haushin shi d'aya da hakurin Salma,tunda ba wai zata g'yara bane. Kuka ta fara mishi harda shura kafa kan wai ya juya mata baya yaki kulata. Juyo wa yai yana k'allonta, duk da a kule yake da ita amma har kusan dariya yaso saka. "Ba nace kai hakuri ba,Allah kasan ban ta6a kin yi maka abinci ba da gangan... Tashi yai ya zauna a kusa da ita. "Toh naji na hakura,bar borin...ya sa hannu zai goge mata hawaye sai dai kamas... "Au kukan ma na karya ne ashe?... Dariya ta fara ta d'au mishi pillow sukai d'aki. "Ina a gidan nan Allah ba kai ba k'wanan parlour. Murmushi yai yana mai tausayin kanshi, ina ma Salman shi ta da ta dawo mishi... Ina ma zai yuwu ace kullum yaso ganin Salma zai sameta a gida haka?... Ya sani da yana son Salma,so ba na wasa ba,amma k'arfi da yaji so take tafi k'arfin shi,ga ko kadan bai kaunar yaga fushin ta. Ina ma itama haka take nannan da nasa fushin... Yasani da *Mai Hali Baya fasawa* **************************** Sauri take tayi,dan yau gidan mai gumama suka je,tasan kuma tabbas Ja'afar yana hanya. Aikwa tana zuwa ga nan machine d'inshi a kofa halamun yana ciki. Duk da tana jin dan shayin shiga su ar'ba, haka ta d'aure ta shiga. Takaddu yake nema, da sallama ta shiga, a chan ciki ya amsa yana cigaba da abinda yake. "Sannu da zuwa... "Uhmm.. Kawai yace, sai ta ta6e baki. "Gidan fa mai gumamar nan da na fad'a ma jiya ta aiko mana za'a kawo muka je..kaga zuwan banza mukai ma wai sai gobe. A dirare ya k'alleta lokacin da yake tashi, ganin yai banza yasa tace "ni fa nan kad'ai naje,sai gidan Maman Ummi dana biya mata muka tafi.. Kai ya k'ada, kan yace "yayi k'yau... Maman Ummin ce mijin ki koh mai gumamar?... Ido ta zaro,sai ya kada kai, "no ba wannan ba ma, wai d'uk inda kike azarbabin zuwan nan wa kike gani yana zuwa gidan ki yafi minti goma aciki?... Koh d'uk suna da aikin

Table of Contents

Chapters

41 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});