Chapter 17
Chapter 17
jajir hawaye na zuba. "Wallahi tunda nake akan fita unguwa ban ta6a sa'inasa da Abban Aslam ba,kar kara in naja,ya ja,hakura nake na barshi,wani sa'in sai kiga har ya fita,amma sai ya dawo yace in shirya ya sauke ni,ina fara'a za'a gama komai ba bacin rai, duk wanda zai fad'a miki ana tank'wasa namiji ta fad'a da bala'i wallahi karya yake miki,sai dai ma kullum yai ta baud'e ga uwa uba sane mishi da ki ke. "Zuciya nason d'ukkan mai k'yautata mata Salma,sannan a kullum tana kara nisa ga wanda ke munana mata... Ki gane wannan, tunda dama taki,shine ya koma miki ta hagu, ki fita a bakin aurenki Salma, tun da kuruciyar ki wai har kin zama bazawarar k'arfi da yaji? Ranar da kanshi Ja'afar din yazo gidan nan,akan irin yadda ba k'ya jin maganarshi,nai mishi alkawarin zanje har gida na miki fad'a sai gashi Allah ya kawo wannan. Sosai tai mamakin Aunty A'i,da yau ta zauna fed'e mata biri har wut'siya.. Tai imani duk maganganunta ba wanda ba ita ke da laifi ba tabbas. Wata muguwar nadama ce ta sakko mata,kuka kam ba kama hannun yaro, har sai da taji ba dad'i. Bataki koh yanzu ta nemi gafarar Ja'afar ba kan ya maidata aurenshi,tai alkawarin d'auwama acikin dakinta har sai yace Salma fito. Aiya Salma, Ja'afar baya tataki,yanzu ta Bintu yake.. By Feenat Ja'afar. Like 路 1 路 Reply 路 Report 路 Jul 29 Feenat Ja'afar Novel's *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 23_Zazzabi harda amai take,duk zatan Aunty A'i akan kukan da taki dainawa ne. Washegari ba zato ba t'sammani Aunty A'i ta t'sinkayi sallamar Abba a t'sakar gida. Lokacin dawowarta daga band'aki kenan ta gama zuba ma Salma ruwa a amai na tun jiya da yaki t'sayawa,sai dai tana jin Abba ne ta mike tare da yin waje da sauri. Hannu Aunty A'i ta d'aura aka,ganin zabga- zabgan bulalin da Abban ya shigo dasu gidan, fad'i yake "Ina take Aisha?.. Tuni idonta ya raina fata,fatan ta Salma taji ta buya. Cikin in'ina tace "Abba wa d'in?.. Hannu daya marar bulala ya nunota dashi, "Kinci gidan ku... "Bani hanya na wuce,yau mai rabani da Salma sai Allah a gidan nan.. Da k'arfi Aunty A'i tace ta gudu,hayaniyar ce ta fiddota a band'aki ta had'a uban zufa dan azabar amai, har bata danji sosai, lekawa tai ta labule jin an ambaci sunanta... Ido waje ta koma da baya tana neman ma6oya,tuni ta ware tai bayan kujera tana rufe baki da duk hannunta biyu jin Abba a parlourn. "Dan Allah Abba kai hakuri,wallahi bata da l... "Aisha,koh ki fito min da ita koh bulalinnan su kare a kanki... Ido Salma ta rint'se da sauri,kirjinta sai d'ukan tara tara yake. Sai dai mey? Kamshi turaren kayan Abba ne ta busu hancinta,take taji amai ya taho tai kokarin ta mat'se sai dai ta kasa,tuni k'ak'arin aman ya taho sai dai ciki ba komai. Bata zata ba sai jin magiyar Aunty A'i tai tana dan Allah yai hakuri... K'wak'waran mot'si batai ba taji saukar bulali tai ajiki ta ko'ina. Ihu take da iya guntun k'arfin daya rage mata tana Abba zan mutu, ina,kawai lafta mata yake,da Aunty A'i ta rike sai ya cika ya hau zuba mata wata. Makogaro ba ruwa,duk ya tafi a amai,tuni har muryarta ta dashe,sai k'ak'arin amai da take. Kamar an hullo mama sai ganinta sukai a kid'ime,ganin yadda yake jibgar Salman ta bala'in tsorata, da sauri tai waje dan kara kiran yayanshi Ganin Abba zai kisa,yasa da sauri Aunty A'i tai ma Salman rumfa tana yai hakuri cikin kuka,ganan Salma koh k'wakkaran mot'si batai,bai bi takanta ba ya hau zuba musu tare, "Abba ciki ne da ita,wallahi zai zube.... Chak ya t'saya da bulala a hannu sai zufa yake, yai dai dai da shigar Mama tai katari da zancen Aunty A'in. Bulala ya yarda yana haki,tamkar yasa kuka dan bakin ciki,tunda yake basshi da fadanshi amma bai ta6a sa hannu ya dakesu ba sai akan Salma,wannan shine karo na biyu gareta. So take tafi k'arfin kowa a ganin shi,toh shi bazata fi karfinshi ba. "Ba mai fin karfina a gidana ban maganin shi ba... Yau kin t'sira a dalilin zancen A'i,da na lahira ya fiki jin dad'i.. Duk da laifin nafi daura ma uwarku data zuba ido kuna abinda kuke so... "Mun shiga uku... Da sauri Maman tai kan Aunty A'i mai magana. Jijjiga salman take tana kira. "Salma!... Salma!!.. Mama bata mot'si wallahi... Tuni suka hau jijjigata Aunty A'i na kuka. "Shikenan Malam ka kashe min Y'a ka huta... Babu yadda banyi da kai ba akan kai hakuri kar kazo,kar kaje,ga nan irinta ka... "Ki rufe mana baki, koma meye ke kika jawo, ruwan k'anin Aslam ya gani a jarka da sauri kuma ya dakko wai su mat'sa agun,ido duk hawaye suka mat'sa. A hankali ya dagota tare da yayyafa mata, a hankali ta kawo numfashi sai dai ido a rufe. "K'unnen k'ashi gare ki ne Salma,shi yasa baza mu shirya ba sam sai kin g'yara hali. Kuka ta fara kad'an kadan lokacin da suke dagata, sosai ta lillisu,duk jiki ciwo. Wayar Aunty A'i,da Ja'afar suke magana wai yaji Abban su yace Mama ta bugo kan Abba zai kashe Salma... Cikin kuka tace "Kazo gidana suna nan. Duk ya kuma kid'ime, tabbas ba d'ukkan wasa yasan Abba yake ma Salma ba,tunda Aunty A'i take kuka. Garba ya kalla,"dan Allah kaini gidan Aisha yayar Salma. Da mamaki yake K'allonshi, "amma dai kasan yanzu _chairman_ zai zo yama signing koh?.. "In bazaka kaini ba na fita na hau abin hawa. Kafad'a ya daga, "a muje, ni meye nawa. Mijin Aunty A'in ya kira koh yana gidan,yace su shiga kawai,Abba ya sanarshi komai tun dazun. Abba ya fita lokacin da suka zo,mama ta tafi nemo abin hawa. Aunty A'in ce ta shiga dasu,ganin bulalin wajen duk sun kakkarye ji yai kamar yasa kuka,yanzu duk bulalin nan a jikin Salman sa ta kare? Jiki a sanyaye suka je parlourn,duk ta kudindina tana rawar sanyi,da sauri ya karasa gunta yana kira,tana jinshi ta kara rushewa da wani kukan. Hijabin ya yaye mata,yana ko'k'arin cicci6ota ya tuna da sakin dake t'sakanin su,sai ya zame hannu tare da zama. Bai san wani irin so yake ma Salma ba,wanda har yake rawar jiki akanta duk da abinda ta mishi, gashi har taja jiya ya bada kai gun Bintu bori ya hau. "Mey yasa Salma?.. Mey yasa ki ka zabar mana irin rayuwar nan?.. Gashi yanzu kin dasa min son kara aure koh na samu maslaha aciki... A zabure ta tashi,duk da yadda take jin jiki tana cije le6e dan azaba. "Mey kace Ya Ja'afar?.. Aure?.. Da sauri ya k'allo ta,sam bai tunanin zancen ba a ciki yai ba. Ganin bai bata amsa ba yasa ta yarda da abinda taji,hannu tasa duka biyu ta dafa kan ta zamo kasa tana cije baki,g'wiwa biyu ta durkusa duk tai kalar tausayi. "Ka rufamin asiri Ya Ja'afar dan Allah,wallahi, na rantse bazan kara ba..Dan Allah kar kamin kishiya.. Dan Allah, wallahi bana sonta.. Allah zan g'yara..nai alkawari,.. Ido ya rint'se, had'i da cije le6e,ba yau Salma ta fara mai magiya da rantsuwa kan ta d'aina ba,amma ba abinda ya sauya zani.. Yanzu komai ya kare musu,aure gareshi ya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41