Chapter 22
Chapter 22
ya zauna,Salma nuna mishi halin ko in kula take tun satin biki, sam bata koh kishinshi,sabgar gabanta kawai take. K'wafa yai ya kada kai,dan ba karamin haushi hakan yake bashi ba. Motsinta yaji a t'sakar gida,ta window ya dago yana k'allonta zata wuce band'aki da bokiti da kwandon wanka,watoh daga shi har amaryar shi basu isheta ma kallo ba?.. Dan wai koh hanyar d'akin bata kalla ba,k'wafa yai kan yai waje gun band'akin ya t'saya kamar maigadinta. Har ta gama wanka yana t'saye,tana bud'e kofa sai ganin mutum tai a t'saye ya bake hanya,kai ta k'auda da nufin ta wuce ya riko bokitin,yaja ta taja,kawai sai ta sau mishi,k'wandon sabulun yake neman k'ar6a tai baya dashi. "Wanka zanyi man Salma.. Wani k'allon ta watsa mishi kan ta had'e rai, "Bana _sharing_ din soso. Baki sake yake k'allonta, cikin fusata yace "da da wanne muke yi?.. Kanta gefe tace "toh yanzu na sake t'sari... A tunzure yace "Wai Salma meye haka?.. Bana.. "Kai Dear J,ga soso nan kai wankan. Juyawa sukai gun mai magana, Bintu ce daga ita sai y'ar yaloluwar rigar bacci ba koh zani balle dank'wali. T'saki Salma ta ja,kan tace ''Malam ban waje na wuce,tuni ya kara kuluwa, shi take ma tsakin?.. Yai mata k'yau,kawai sai ya dungurar mata da bokitinta ya shige band'aki,da sauri Bintu tai kitchen ta d'akko mishi nata,koh ta kansu bata kara bi ba ta zari bokitin ta kara mai,a ranta tana "karamar y'ar iska kawai. Sam Salma taki dad'i, dan fur taki bawa kowa fuska a gidan,dan taga da mugun falli amaryar ta shigo mata. Har girkin amarya ya kare ya dawo ga Salma amma ba sauki. Zata gaidashi tai komai,amma ba magana duguwa, sai ma haushin sa dake kara ziyartar ta. Tuni ya kai kara gun Aunty A'i,wai Salma taki sake masa fuska. A ranar tai mata waya ta kare mata tass,tuni ta hau kuka,wai ai dan ita bata kishiya ne,bazata gane lamarin ba,ga kusan kullum Bintu na chakalarta tana kaucewa. Shiru Aunty A'in tayi,dole wannan ba zancen waya bane, "Ki bari zan zo koh zuwa gobe ne. Ranar girkin Bintu ne,yau tun safe take fallin fararo a t'sakar gida,sai ya6a mata haibaici take ita kad'ai kamar sabon kamu. Salman tana zaune kan taburma a kofar ta tana yanke farce. Harara ta sakar mata,kan taja t'saki, "Wawiya kawai.. Shewa Bintun tayi harda guda. "Kece babbar wawiya wacce zaman gidanta ke mintsininta.. Ehee, naji komai ai,saki daya ya rage miki duk a dalilin gantali gardi. A masife ta tashi,sai dai nan da nan ta k'auda bacin rai dan ya6a ma Bintu magana dai-dai ita. "Ahaiyee,, naji,tunda banyi k'wantai a layi bare ina bi ina tallan kaina agun d'a namiji ba ehee, ke har kin isa ki ce kin san komai?. tunda dey ni ba matar tushe bace ba... Dan tuni akasan da matar tushe dai bata k'warjini... Karya uwar bin maza kawai... "Eh naji ki ce komai,igiya uku ce a kaina kinga na fiki matsayi a... "Ke... Bana son shashancin banza wallahi.. Juyawa sukai danjin mai gidan yai shigar bazata. "Ihu har titi mutanan unguwa ana jinku sai kace wasu karnika?... Harara Salma ta sau mishi da t'sabar tuhuma a k'allonta. "A ni ba karya bace, dan har gidan mu ka samo ni..chan ka nemi karya tun wuri.. Jiki ta kad'e tai dakinta ta barshi baki a sake. Ita kam Bintu lukwas tayi,tabbas Ja'afar kadai zai iya fad'a ma Salma cewa ita tace tana sonshi,da kuka tai d'aki dan bakin ciki. Itama haka take gun Salman,sosai taji zafin maganar Bintu,tasan kuma babu mai fad'a mata sai Ja'afar. Toh fa Ja'afar, ka shiga t'sakiya. By Feenat Ja'afar. 9/29/16, 9:16 AM - Queen Safiyyert馃憫: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 26_Kowa bin kofar dakinta yai da kallo, yana murna ba'a rikicin mata biyu a gidanshi yau gashi an fara,dole ne tun wuri yai ma tufkar hanci. Har yayi dakin Salman sai ya t'saya, dole ne ya nuna mata kuranta, in da tai mishi fitsara ya k'yale toh yanzu bazai d'auka ba,dan ba ita kadai bace a gidan,kawai sai ya juya dakin Bintu. Kuka take yana ta fadanshi taki kulashi, chan kuma sai ya sassauto, "Ni tashin hankali ne bana so a gidana ne,tun wuri ma in zaku had'a kai ku had'a, dan ba mai chazan hawan jini. Kai ta dago tana mishi k'allon tuhuma, "Au shine dalilin da yasa ka fad'a wa matarka baka so na?.. Ni nace ina son ka koh?.. A haka za ai zaman lafiyan?.. "Ke kinga bana son iyayi,dawa nai wannan zancen?.. Da sauri cikin kuka tace "da matarka man,wato harda fad'a mata kwantai nayi nai ma tallan kaina.. "Ban san anyi maganar nan ba Malama,ki ma cire zargin ni na fad'a mata, bari na je zata fad'a min yaushe muka fara y'ar sharri da ita... Waje yayi zuwa dakin Salman. Kai Bintu ta k'ada, "ashe munafuka karya take dan ta had'ani fad'a da Miji,toh karyarki taci karya,Allah sa ya k'wada mata mari tukuicin sharri. Ita kam tanajin bud'e kofarshi ta mike tare kama k'ugu ta k'ank'ance ido. "Salma yaushe muka fara y'ar sharri dake a gidan nan?.. Yaushe nace miki Bintu ce tai min tallar kanta na aura?.. Harara ta sakar mishi da k'allon kar ka rainan hankali. "Ka nad'e taburmar kunyar ka man ta haka,wato kayi amarya shine ka zabi ka tuzartani agunta,karafkaf abinda ya faru ta fad'a mini,toh da ka fad'a mata saura igiya daya ta aurenka a kaina sai mey?.. Baki ya saka cike da mamaki,lalle ya shiga tarkon kaidi na mata, wato kowacce sharri take neman k'ulla mishi a gun y'ar uwarta ashe?.. Bai da tace wa, kawai sai ya juya zai fice, da sauri tace "a ka fita man,dan nayi imani bazaka karyata cewar ba kai ka fad'i ba... "Idan kuma habaici da iyayi kake neman matarka ta dinga min dan ka huce haushinka na da toh bissmillah,dai dai nake dana sa kafar wando daya da kowa a gidan nan wallahi.. Juyowa yai yana kallonta, sai tai d'aki ta barshi t'saye baki sake. Titi ya fice ko ya samu sa'ida, lalle yau ya jinjinawa sharrin mata,amma kaf yafi jin haushin Salma,dan sam yanzu ya fuskanci fitsararta tafi ta da yawa. Tun daga ranar ba jituwa t'sakanin matan, daya in Bintu ta fad'awa Salma sai ta fad'a mata dubu,daga karshe ta bige da kukan bakin ciki, har mai gidan yazo ta kit'sa mai karya da gaskiya,wani sai dai ya bata hakuri, dan a ganinshi yanzu Salma tafi karfinshi,dan da ya mata magana ita y'ar dika take,daga shi har amaryar zata chake tass, sai dai yai abinda zaiyi. Shi yasa shi kuma ya t'siri mata t'siya,in dai zata kona mishi rai,toh shi kuma zai ta biyewa Bintu suna ta mata feleke a t'sakar gida, daga karshe kam sai yaci nasara,dan haka zata shiga d'aki tai ta kukan bakin ciki,a nan zai ta mata dariyar keta. ***** Sallama taji kamar ta Maman Ummi da Maman Abba,lekawa tai ta window, sune kuwa, "munafukan Allah ta'ala kawai... Ta fada tana kokarin ta fito rai 6ace,dan tai imani duk abinda take fuskanta yanzu da sa hannun su aciki... Chak! Taja ta t'saya rike da labule a hannu ganin Bintu ta fito da gudu danjin sallamar su. "Sai yau Aunty Ladi zaki
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41