Chapter 6
Chapter 6
PM] Feenat Ja'afar: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 11_Kan safiya har ta gama tunanin abin da zai fisshe ta. Hakan yasa t'saf ta tashi kamar ba ita taci kukan nan ba. Aunty A'i yau za'a kaima wuni,tun (12) suka fice ita da Ummi. Chan suka yini har dare,a kafa ta ratso ita kad'ai sakamakon Ummi da ta biya kar6an _style_. Tunda tazo layin su Ja'afar d'in taji gabanta na fad'uwa, duk da bata koh k'alli hanyar gidan ba. "Abokina ina ka tafi ne daga lissafi kai shiru? "Ba kaga kamar Salma ba waccan mey tafiyar? Ido Garba ya k'wara, da mutum,amma a duhun nan bazai tantance ba,kawai sai ya k'ada mishi kai, "A cikin duhun daren nan ne har zaka gane wake tafi.... Shiru yai ganin Ja'afar d'in yai gaba,da sauri yace "wai mey ke damunka ne? Ina za ka?.. Binshi yake shi kuma yana bin mai tafiya a duhun. "Salma"... Chak! Ta t'saya dan jin kamar an kira ta,a hankali ta juya,da dan tazara a tsakanin su kad'an, amma hakan bazai sa ta kasa gane ya Ja'afar ba koh a cikin dubu,hakan yasa cikin sauri ta juya ta chigaba da tafiya,har dan gudu- gudu sauri-sauri take. "Mey zai fad'a min kuma? Ta fad'a cikin ranta. Har kusan layinsu ya bita, tsammanin shi koh tsorata tayi,amma tabbas wannan Salma ce,kawai sai ya t'saya a dai-dai layin nasu yadda bazata ganshi ba,da hasken inji a layin, yana gani ta t'saya ta waiga,kan da sauri ta shige gida. "Amma fa baka aiki sam Jaa, wai har nan ka biyota kage ma koh aljana ce a daren nan? Juyawa yai yana girgiza mishi kai,"Allah Salma ce,toh yaushe ta dawo?.. Baki sake Garba yace "hadda rantsuwa? In Aljana ce fa mai siffar ta?. Harara ya sakar mishi kan ya juya suka tafi. Ita kam tana zuwa gida Abba da Mama suna t'sakar gida ta shigo sai haki,tuni k'wa Abba fad'a ya karu, kan mey yasa sukai dare? Tuni tai zuru zuru,fad'a sosai tasha,saura Ummi,d'uk da laifin Ummin har sukai daren. Washegari kusan yamma sai ga nan yaro kan ana kiran Ummi da Salma inji su isma'il. Harara Salman ta k'wada ma Ummi, kan tace "yanzu sai da kika fad'i ma mutanan gidan mu kika huta koh? Allah ban san yayi6e ni. Hararar itama Ummin tai mata,"arziki na binki kina guduwa,kowa yazo kice bai miki ba,ki mayi karatun ta nut'su wallahi,dan aure zanyi ni ba jira.. "Keai Kowanne dan chaburos ma yazo Ummi a shirye kike, toh ba dani ba. Yankan farcen Ummin ta bari tai hanyar d'aki tana fad'in"sai kiyi ta zama kar kiyi aure,har mahadi ya baiyana. Cikin kuluwa zatai magana sai ga Mama ta fito a d'aki, ashe d'uk tana jin su, "toh k'wa maza ki wuce ki je tun kan na sa6a miki,daga yau na d'aina zuba miki ido ba fus bare ass Salma... Yarinya sai taurin kai,ace koh kishin yadda y'ar uwarki take shiga take fita da y'an k'wabai ba kiyi? Toh na gaji da gafara sa dan ban hangi kaho ba... Maza ki shiga daga ciki ki g'yara ki wuce... Kai kasa Salma tace "toh.. Ita kam tana mamakin halin Mama har kullum akan su,sai dai tana tuna Ja'afar tuni taji tana da muradin fita,tunda wanda take danshi bai ma san tana yi ba. G'walo Ummi tai mata,kan tai waje tana sai ta fito. Bata aune ba taji mama a d'akin nasu, bani waje ki ga,da kaina sai na g'yara ki... Baki sake take k'allon Maman,aikwa ta zage ta hau cha6a ma Salma k'walliya irin wacce bata ma san mama ta iya ba. Fad'i take "na rasa gane wace iri ce ke Salma,arziki na binmu kina zura da gudu,d'uk wani buri da na sa kanki kin rushe shi, in banda haka a jiya kad'ai kina ga irin bajintar da Ummi ta shigo dashi daga gun isma'il yake ko wa? "Haba k'alle ki a madubi man,san kowa kin wanda ya rasa... Tana yi tana g'yara mata d'aurin dank'wali. "Maza ki fita kan Abban ku ya dawo ya hana ruwa gudu.. Kai ta daga zata d'au hijabi,da sauri Mama ta warce, "g'yale zaki sa matar Malam,koh a Shari'ar a haka ake son a ganki,ta ina za'a yaba in kin maka hijabin? Toh ba walima nace kije ba.. Kai ta k'ada, ta zama tamkar rakumi da akala,sai yadda mama tace. "A'a, ko ke fa,k'alli kanki a madubi ki ga man,ai da banbanci, maza je ki... Kai ta kara k'ada mata, har zatai waje da sauri Mama ta kara kiranta. Turare ta fesa mata,kamar tace ba k'yau mama,sai dai taja tai shiru. "Ki murmusa man Salma,haba..murmushi ma ado ne ga fuskar Y'a mace... A yadda maman take yi bata ma san sanda abin ya bata dariya ba. Allah ya gama su da uwa "LASHE MONEY", har ta fita kuwa tana murmushi, mama sai barta. Suna t'saye gaban wata jar _CRV_ tare da Ummi,d'uk dinsu sun zubo mata ido. Ita kanta tasan tayi ne, fari da manyan ido kawai budurwar Ja'afar zata fad'a mata tasan. Doguwa ce ita dai dai misali,farin jinin samarin zamani,fatarta a goge take mai launin Wankan Tarwada(black beauty), tana gashi ga gashin ido,gata fuska doguwa,gata tana da diri dai dai so,d'uk komai ya ji ba bau ba. Ya dace kam tai amfani da lokacinta tun yanzun. Cikin takun da ba irin na Salma ta da ba ta karasa gun su Ummi,ga murmushin nan dan _beauty point_ din nan sai lot'sa wa yake. Tuni ta kara tafiya da imanin Muzammil,har yake ji kamar ya taro ta kan ta iso. By Feenat Ja'afar. [7/22, 4:57 PM] Feenat Ja'afar: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 12_Ita kanta Ummi tai mamakin Salma da sakewar ta. Sun gaisa da isma'il saurayin Ummin su kuma suka zaga dayan bangaren motar, Kusan kawai d'aurewa take tana mishi yake, amma ita sam taki jinin saurayi mai shegen surutun t'siya. Hakan yasa d'uk taji ta gagu su k'auce, ga tasan Abba gaf yake da zuwa da magriba tayi. Kamar ance daga kanki, Ja'afar tagani kusan su kad'an, tamkar gunki yaja ya t'saya, ga nan wannan budurwar da ta ta6a ganin su itama tana k'allo su,sai ta k'alli Ja'afar, kawai sai ta d'auke kai kamar bata gansu ba. Harda kara bawa Muzammil wani _attention_ na daban tana murmushi. Cikin sanyin jiki ya juya,tana dan satar k'allon shi,a baya budurwar tabi shi tana waiwayen Salman,ji tai kamar ta k'wada mai kira,So ba k'arya bane Salma. Da k'allo Ummi ta bisu lokacin da suka zago ita da isma'il, sallama sukayi,suna kokarin jan mota sai ga wata bakar mota ta _parker_. Ganin su Garba yasa da sauri Salma ta daga ma muzammil hannu tana mishi murmushi. Ja'afar dake k'allonta ta glass din ya rint'se ido da sauri. Ganin zata juya yasa Garba fad'in "Salma" da sauri. Juyo wa tai lokacin da yake yafito Jafar da hannu halamar ya fito. Koh ta kansu Ummi bata bi ba tai gida. Yake tai mishi lokacin da suke karasowa,sai dai koh inda Ja'afar yake bata k'alla ba shi da budurwar shi. Cikin barkwanci Garba yace "duniya da alkawari kuwa Malama Salma?.. Murmushi tai mishi iya le6e, "ashe kin dawo amma koh mu sani.. Karon farko ta k'allo gun Ja'afar, idonshi k'wa a kanta girrr...ba koh kiftawa.
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41