Chapter 1
Chapter 1
BAK'IN AUREN KI... 漏Feenat Ja'afar. 1_Sauri take tamkar taci da k'a, kai daga ganinta ka ga marar gaskiya, a d'ai d'ai layin da zai sadata da gidanta ta t'saya tamkar munafuka ta d'an leka, da sauri ta komar da kai tare da dafe kirjinta mai barazanar fashe mata... "Na shigesu.. Ja'afar? Ta fad'a tana mai sake lekawa, sai karaf sukai ido hud'u dashi,tuni buguwar zuciyar ta ya k'aru, bata ta6a ganin shi a irin wannan yanayin ba. "Mey yasa kika fita bayan yace ka'rki fita?... Bak'in g'yalenta tasa tana t'sane gumin dake t'sat'safo mata, cikin jihadi ta fito daga inda ta boye harda d'aure fuskarta tamkar bata ganshi ba. Kanta na k'allon gefe tazo d'ai d'ai kofar gidan zata shige ba tare da ta k'alli yanayin nashi ba.. Turus taja ta t'saya, ganin yadda ya d'aura wani mukulli kan wanda ta rufe gidan dashi, cikin k'arfin hali fuskarta na gefe tace "ya haka? Wanda bai nan ma yafita,hakan yasa ta kara fad'in "Ya Ja'afar ya haka?.. Tamkar kububuwa yake cika, ji yake tamkar ya rufeta da duka dan takaici, Ashe d'uk uban rat'suwar Salma ta mai kan ta d'aina a fatar baki ya t'saya?.. Mota ya bud'e yana ko'k'arin shiga ta mot'so da sauri, "Ja'afar magana nake fa... A tunzure ya juyo da nufin kifa mata mari tai baya da sauri gabanta na fad'uwa. Lalle yau ta ta6o ran y'an maza, cikin bacin rai yai mata k'allon banza, "kin za6i gidan suna sama da sharad'i na koh? Toh mey kika dawo yi min gida? Koh kin manta da sharad'in da na baki na in kin fita toh kin fita "A BAK'IN AURENKI?... Ido ta zaro tana dubenshi, kawai sai ta dake, cikin k'arfin hali tace "A BAK'IN AURENA fa kace Ja'afar? Daga gidan sunan shine har kake wannan kumfar bak'in?.. Ta karasa tana y'atsine mishi fuska,kawai sai ya k'ada kai ya shige mota. Ganin da gaske tafiya zai yasa da sauri t ajiye t'siwar ta fara kiranshi, ina,tuni ya juya a kalar motarahi cikin zafin nama, da sauri ta mat'sa ganin sai ya iya bi ta kanta.. Tana ganin da gaske yake hakan yasa tuni ta t'sure, hannu ta aza bisa kanta cikin nadamar fitar da tai sunan da ba'a ma gaiyace ta ba, "na shiga uku ni Salma.. Na ja ma kaina wani bala'in.. "Yanzu igiyar Aure na biyu ta t'sinke kenan?.. Tuni zufa ta kara zubo mata dan tunawa da kalaman Babanta, "d'uk randa zaki kara maimaita haka Salma sai na 6alla kafarki in kin doso gidana.... Fad'uwar gabanta ta t'sananta,t'saf Baba zai aikata mata hakan, ta k'alli gabar,da yamma, ta ma rasa ta ina zata fara? Gefen dakalin gidan ta d'an dosana, da d'ukkan hannunta biyu ta dafe kai,tuni kalaman Ja'afar ya dawo mata, "in kin fita kin fita A BAK'IN AURENKI.... Ku biyoni Bayan sallah dan jin yadda zata kaya... By Feenat Ja'afar. 9/29/16, 8:46 AM - Queen Safiyyert馃憫: *A BAK'IN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. *3*- Kai ya k'ada mishi, _"aure ba shine mafita ba Ja'afar,ka g'yara wacce ke hannunka tukun,bana tunanin wannan shawara ce_. Murmushi yai tare da k'ada mishi kai _("I know)_.. _"Amma ka gane ba dan dad'i zanyi ba,nasan d'uk duniya ba abinda Salma taki jini irin nace zan kara aure,dole na d'andana mata mad'acin da ta d'andana min nima_. Murmushi Garba yai yana K'allonshi,wai yau Ja'afar ke maganar zai d'andanawa Salman sa mad'aci?.. Kai ya girgiza, lalle Salma tai wasa da damarta, dan yasan irin dimbin son da Ja'afar ke mata, sai dai gashi za a kaita a baro,dan ta fara sane ma abokinshi.. _"Bana tofa tawa ba nikam,nasan da kai da Salma sai Allah,ni d'ai kai tunani abokina,kar ka yanke hukunci cikin fushi azo daga baya ai nadama_... Baki ya ta6e, kan ya ciro mukulli a aljihunshi ya mika mishi, _"k'ar6i mukullin motarka,dan aure kam nayi na ma gama,kuma *Bintu* zan aura kasa ido_.. Ido waje Garba yake k'allonshi,kan ya k'yalk'yale da dariya, _"lalle ka d'ebo aiki..za kuma ka dasa ma Salma zargin ka cikin ranta tunda kasan komai_... T'saki yai kan yace _"zanso hakan ya kasance, dan zata fi jin haushi sosai_.. Kai Garban ya k'ada yana kunshe dariya, _"muje na sauke ka toh na Salma da Bintu,kai (scene) din nan zai dad'in k'allo wallahi_.. Ya karasa da dariyar keta. Murmushi kawai yai suka shiga mota,har suka isa gida Garba na mishi t'siya..da ya had'o shi da Salma zai kicin-kicin. ************************ A wajen Salma kuwa,sai da dare yai tana k'wance d'akinsu na da sai juyi take,wanda ita kanta ta rasa dalili,har yanzun haushin Ja'afar na kasan ranta na ya mata wulakanci, sai dai da ta tuna rabuwar igiyarta d'aya sai taji fad'uwar gaba. Yau gata a katifa ba ta ita da Ja'afar d'inta ba?..yau d'aya ta raba alakar matashin kanta(kafad'ar Ja'afar) sai pillow... Hannu takai kuncinta,da mamakinta hawaye take,kawai sai ta ida karasawa ta fashe da kuka.. Wanda kai da gani na k'ewar Jafaririn ta ne da t'sant'sar nadama,amma ina,zuciya taki amsar hakan.. Ga uban sauro da ya damu k'unnenta da ihu duk da da Katanga a t'sakaninta dasu(net), ga uban zafi ba wuta ba (Gen), d'uk t'siya tasan da a gidanta ne da yanzu tana shan iskar injin da Ja'afar ke k'unna mata d'uk dare ta k'wanta dan bata bidar zafi.. Ga mama tace ba mai tada mata inji Babanta baya gari, kuma bata kud'in mai... ***""* Shima hakan take ga Ja'afar, kusan a hali d'aya suke,sai dai shi kawai ya kura ma fankar d'akin da ke kad'awa a saman d'akin ido. Tabbas har yanzun baida sama da Salma koh a kasan zuciyarshi.. Yana sonta, so marar misali,duba ga yadda suka gina soyayyar tasu kamin aure.. Da za'a ce mishi a da Salma zata sauya hali gaba d'aya musamman akanshi da zai mu sa... Juyi yai ya jawo filo,d'uk t'siya tanan yai k'ewar Salma.. Dan karamin t'saki yai kamin ya tashi yai waje dan kashe inji. *By* *Feenat Ja'afar* 9/29/16, 8:48 AM - Queen Safiyyert馃憫: *A BAK'IN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 4- Salma Umar Y'a ce ta biyu gun Mama(Haj Rabi'a) da Baba(Malam Umar),y'an asalin Yobe ne,kasuwanci ya kawo kakansu Kano da rabon su Salma. Su biyu kawai ne a gun kakan su Malam Bukar Mai buhu,baban su Salma ne karami, sai yayanshi Baba Aji, yaranshi a kallah za suyi (16),yayin da Baban Salma ke da uku,Aisha (Aunty A'i)dan tafi Salma sosai,Salma,sai Ummi. Kasuwanci ne gadon su Baba,dan koh bayan rasuwar kakan su Salma sun cigaba da juya abinda ya rage musu. Suna taimakon juna sosai,hakan yasa kansu yake a had'e, duk da rufin asiri ne kawai na Allah. Sannan d'ai-d'ai iyawa sun bama yaran su karatu da tarbiya,suna da t'sanani musamman Baban su Salma. Sai dai fa ita Maman su gani take kakarsu ta yanke saka,tunda Allah ya hore mata yara mata uku setin samira ta zuba jari,shi yasa d'ukkan wani abu akan A'i yake karewa dan ita tasa a lokacin. Ba lefi,ak'wai dan k'yau irin na ainashin mutan kanuri,sai kuma Maman dake asalin Shuwa,ba farare bane,za dai mu iya kiransu da _"black beauties"_sirrin su kuwa,diri ne da yalwar gashin ka da _"beauty point"_ _(dimples)_.. Wanda tamkar kowa diga mata ake. Hakan yasa kasuwar Aunty A'i ta daga da sauri,tuni k'wa Mama abin nema sai ya samu,hakan yasa
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41