Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 27

Chapter 27

A Bakin Aurenki Book 1 Complete Hausa Novel – Salma’s Painful Return 1,258 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Allah ya Ja'afar ka barni naje,nima dana haihu fa sau biyu tazo min har suna uku,kaga ba dad'i ace ni koh sau d'aya banje ba barka ba sai suna. "Sunan ma ki fidda a ranki,dan inda mu'amular dana fi tsana,toh mu'amular ki da y'an unguwar chan ne,kin gane ai?. Kasa tai da kai,sosai take d'aure irin halin da Ya Ja'afar ya tsiro mata,yanzu da ta kara tambaya zai ce tai gaban kanta,hakan yasa tai shiru. Shi kuma yadda yaga batai gardama ba yasa yai tunanin zancen bai shige ta ba ne. Miemie ya ajiye kusa da ita ya bar mata d'akin. A hankali ta zame ta kwanta,sai ga hawaye ya zubo mata. Zaman gidan nan ya fara isar ta,hakurinta ya fara karewa. Tana ji yai ma Bintu sallama ya fice,kawai sai ta sau kuka a hankali marar sauti. Wato a dake ka a hanaka kuka?. **** Tun bayan fitarshi bayan ta gama kukanta Miemie ta fara,kukan har ya wuce kima, komai tayi taki shiru,kawai sai ta goyata tasa hijab akai suka fita t'sakar gida dan sanyin magriba. Bintun na t'sakar gida tana saita abin fad'i kan Ja'afar ya dawo tambayar Salma koh ta fita,dan komai a k'unnenta ya wakana. Jijjiga ta take tana yawo daga t'sakar gida zuwa zaure da ita,tasan Miemie ba mai rigima bace, tabbas da abinda ke damunta yau,yawan kukan ji take kamar itama tasa kukan koh taji sa'ida. Dak'yar ta samu tai shiru,sai ajiyar zuciya take halamar tai bacci. Buta ta d'auka ta shiga band'aki kenan sai gashi kamar an hulloshi gidan,fatanshi yau ya rit'sata garin satar fita. Bintu ya kalla wacce ke murmushin ganinshi,sai taunar cingam take tana kas-kas,kai da ganinta da yanayinta kaga na mai shirin kulla wani sharrin. "Sannu da zuwa.. Kai ya daga mata, kamar kullum zai tambayi Salman sai yaji bud'e band'aki. A fusace ya kallo Bintu, "bayan fita ta Salma ta fita?.. Ki fad'an t'sakani da Allah. Kwai tayi kan ta fasa tare da yin kas dashi, "Eh ta fita,mey ya faru? Yanzun bud'e dakinta ta shiga band'aki ka shigo. Gadan-gadan Salma tayi kanta da butar data cika zatai alwala anjima,kansu farga ta rot'sa mata aka tana huci,bai isa ba ta rufeta da duka baji ba gani,fad'i take "Sharrin naki ya wuce bayan idona yanzu a gaban idona ma yi.. Mari ya d'auketa dashi shima yana fad'in ta sake ta. A fusace tace bazata saka ba,ita kam tamkar wawiya ta bari Salman na jibgarta,ganin da gaske take yasa da sauri ya finciko Bintun tare da kara mata wani marin. Kunci ta rike tana K'allonshi, "ki sani na gaji da halinki a gidan nan, karan nan zan d'au mummunan mataki akanki wall... "Ka sallame ni in ka gaji dani Ja'afar.. Dan ni tuni na gaji da zaman gidan ka, ka sallame ni ka huta toh.. "Haka ki ka ce?.. A fusace tace "eh haka nace.. Tuni shedan ya shiga cikin zuciyar kowa,musamman Ja'afar da ya rufe ido tamkar bashi ba. "Ki je gida sai na neme ki toh... Cikin kuka tace ''Ban isa zuwa musu ba sheda ba,dole ka bani sheda.. Ba tare da jin komai ba mugu(shedan) yasa ya rufe ido. "Kije na sake ki toh.. Chak! Taji kukan ya t'saya sai na Miemie data tashi dan hayaniya. Baki sake take k'allonshi fuska wanke da hawaye. "Ja'afar ka sakeni kace fa?.. Muryarta na ka'rkarwa ta tambaya. Da sauri ya bud'e ido ya dawo hankalinshi kanta. K'allon-k'allo suke ma juna cikin rashin sanin abin fad'a, musamman Ja'afar dashi ya furta. Ido ta rufe a hankali, sai ga hawayen da ya makale sun zubo. A hankali ta bud'e idon ta k'alli Bintu. "Allah ya biya ki da dai-dai abinda ki kamin Bintu.. Ki sani,sharri kare ne,ko yayi nisa zai dawo gun maishi.. Jiki a sanyaye ta juya gun Ja'afar. "Shikenan abin nema ya same mu Ja'afar.. Aure ya kare a t'sakanin mu..igiya uku ka rusheta Ja'afar.. Ka rushe su.. Hannu tasa ta share idonta. "Ba ka da bukatar na t'saya maka bayani yanzu kam,dan ka zuba katanga a t'sakanin mu. Cikin nut'suwa tai hanyar waje ba tare da ta koh waiwayi d'aki ba. Da k'allo ya bita, ilahirin jikinshi ka'rkarwa yake,ya kasa tattara kalma daya da zai ambata, har Salma ta 6ace wa ganinshi. 'By Feenat Ja'afar. [8/2, 10:40 AM] Feenat Ja'afar: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 31_"Innalillahi Wa'ina Ilaihirraji'un.. Allahumma Ajurni fi Musibati,wakhluf li khayran minha... "Salma ki ce min ba gaskiya ki ke fad'a ba Salma?.. Dan Allah ki ce wasa ki ke.. Murmushi take,wanda da zatai kukan zai fi mata alkairi, amma ta kasa,tun zuwanta gidan Aunty A'i ido ya kafe,tunani ya t'saya.. Dabara ta ka re,sai kallo da ido da murmushi da yafi kuka ciwo. Waya Aunty A'in ta d'auka dan kiran Ja'afar, tayuwu koh shi ya mata bayanin da zata gamsu tunda Salma ta zama kurma. "Ja'afar.. "Bashi bane.. Tsam tayi dan tasan Bintu ce ta d'auka. Da karfin hali ta tambayi in yana kusa ta bashi man, t'saki tai mata kamin ta kashewar. Kasa tai da wayar tana mai tabbatar da kalaman Salma na aure babu,ya ka re. A hankali ta sakko ta t'suguna gaban Salman tare da dafa kafafunta. "Salma kimin magana ba shiru ba dan Allah.. A dunkule kika bani, dan Allah kiyi magana, shin da gaske ya sake ki cikon na ukun?.. K'allon Aunty A'in take cikin ido,tabbas wannan kalmar ita ta 6acewa tunaninta. Kan ta ankara ta sau mata wiwi,baji ba gani. "Bintu ce... Wallahi itace.. Ban mishi komai ba..ya raba aurenmu.. Allah banyi komai ba karan nan Aunty A'i,ki yarda dani dan Allah, koh su Abba baza su yarda ba... Kamar karatun yara haka take had'a kalaman cikin kuka. Jiki a sanyaye Aunty A'in ta tashi tazo kusa da ita,sosai ta gane sambatu take,cike da tausayin y'ar uwartata ta rungumo ta, ta abu daya take gane gaskiyar Salma tun a yarinta, shine fad'in abin da batai ba cikin kuka. "Na yarda Salma,na yarda dake karan nan.. Ki bar kukan haka, Allahu yasa shi yafi zama muku alkairi. Ita dai kukanta take. Ina Ja'afar ya gano abinda Aunty A'i ta sani game da rayuwar Salma, da bai bawa CID na fitar ta ba, da ya fuskanci ta sauya tun sa'ilin da in yace ta fita take kuka,da ba ayi hakan ba. ******************* "Innalillahi Wa'ina Ilaihirraji'una... Ja'afar mai ya kai ka wannan yanke d'anyen hukuncin kan ku?.. Mey ya kai ka?.. Abinda ya faru yake sanar mishi,gaba daya ya rasa abin yi. "Shin ka tambayi ta fitan koh bata fitan ba?.. Koh har yanzu kai baka hango hankalin Salma ba ne.. Kai ya k'ada mishi "Ba wannan ne karon farko ba,ni nasan Salma fiye da zaton ka.. "Ka kuma yarda da Bintu fiye da yarda ka bawa Salma yarda koh ka ke nufi?.. Murmushi yayi na takaici, "Ja'afar bakasan sharri irin na mata bane.. Da baka ba Bintu amanar aurenka sukutum ba Allah. Tayu ka tafka babban kuskure na fahimtar Salma karan nan.. Amma ka yi bincike, shine t'sarin Shari'a.. Ni na shiga gida. Da kallo yabi bayan Garban, duk maganar shi gaskiya ce,kuma ba daya daga ci da ya aiwatar kamin komai. Yau daya yaga fushin Garba karara kwance a fuska,tabbas haushin shi yake ji shima,kamar yadda shima yake jin haushin

Table of Contents

Chapters

41 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});