Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 30

Chapter 30

A Bakin Aurenki Book 1 Complete Hausa Novel – Salma’s Painful Return 1,261 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

kunu tana dauraye murfin feedern. "Sam baki da jimirin yunwa Miemie,kimin hakuri yanzun zan... Itama shirun tai dan jin sallamarshi. Da dan rarrafe da tafiyar da batayi kwari ba ta nufi gun Abban da murna. Ganin Miemien ne yasa shi dawo da hankalinshi kanta,sama yai da ita kamar kullum suna dariya. A hankali ta rufe idonta tanajin zuciyarta na bugawa da sauri,kusan wata 2 rabonta da ta sashi a idonta,jin takunshi na kusanto ta yasa ta juya da sauri tare da had'iye hawayenta. Ya sauya mata,duk ba g'yara, har wata kasumba ya had'a ta dole ta rashin g'yara fuska. Da t'sananin murnar ganinta ya karaso sai washe baki yake,da sauri tai baya ganin abinda yake shirin yi tai gun taburma ta d'akko,sai ya bita da kallo baki sake, tabbas Salma batai kewarshi kamar yadda ya mato a kewarta ba.. Koh irin d'aukin nan na ganinshi t'sawan lokaci haka bata yi. Dan dukan da Miemie take mishi ne yasa ya kallo ta,da hannu take nuna mishi kan feedern dake hannun Salman. Kan taburmar ya nufa tare da zama,so yake sai ya fassara yanayin Salman,shi yasa yake ta k'allonta. Feedern ta mika wa Miemie tana dan satar kallonshi kan ta kau da kai tace "Ina wuni.. Shiru yai mata,sai ta dan kalloshi cikin ido,shima ita yake kallo,bazata iya kallon kwayar idonshi ba,zata chaza mata matsala,da sauri ta kara dauke kai tana maimaita gaisuwar. "Mey yasa kwana biyu ba k'ya d'aukan kira na Salma?.. Ba k'ya ban amsa koh na miki text?.. Gefe ta kara yi da kanta tana kallon wani waje, kan tace "Ban gani ba ne.. Da mamaki yake kallon yadda tai maganar cikin nuna ko'in kula. "Salma kin daina so na yanzu koh?.. Yadda yai maganar yasa jin wani iri da dan tausayinshi,da jihadi ta juyo ido cike da kwalla. "Ya Ja'afar, ya dace mu fuskanci zahiri fa yanzu,mu daina yaudarar kan mu dan komai ya afku..Dole nai aure ka sani,ban maka alkawarin zama ba aure ba,bazan maka alkawarin kin kula wani ba.. Yanzu haka karatu zan koma,ka d'auka rayuwar da ta shud'e a mafarki muka yi ta, yanzu mun farka... Dole akwai cigaba a rayuwa.. Kai hakuri, amma bani da alaka da daukan kiran ka yanzu,ka manta Salma dan Allah,mu fuskanci rayuwar gaba.. Kai ta kautar tana goge hawaye, shi kam k'allonta kawai yake ba koh kiftawa. "Ke nan kina nufin son da nake miki karya ne?... Soyayyar mu hasashe ce Salma?.. Zaman mu da rayuwar auren mu wasa ne?.. Kina nufin Miemie ma mafarki ce?... Da fusata yake tambayarta,kai kawai take girgiza mishi tana hawaye. "Ba haka nake nufi ba.. "Toh mey ki ke nufi?.. Shiru tai tana cigaba da kukan ta,sai ya kada kai cikin takaici. "Salma kin d'aina so na kam.. Girgiza mishi kai tai "Ina sonka Ya Ja'afar, har karshen rayuwata.. Abu daya nake son ka gane,yanzu komai ya sauya,alakar Mimi ce kawai ta rike mu... Ka cire son zuciya aciki, dan bazan iya haramtawa abinda Allah ya halasta min ba.. "Assalam Alaikum, wannan akwatunan fa a zau... Tsaye tai ba tare da karasawa ba, kai kasa ta amsawa Mama sallama,ciki Maman ta karaso,ya gaida ta kai kasa,duk shiru sukai ba mai magana, sai muzurai Mama take ma Salman kan ta shiga daga ciki. Jiki a sanyaye ta tashi ta shiga ciki,a hankali ta sa kanta a kan katifa tana hawaye. Ba dan yaso ba ya tashi yai fita,tare da shigo mata da akwatunan ta. Har zauren Mama ta bishi ta sa sakata tana sababi kan tai gun Salman. "Wai ke baki da hankali ne Salma?.. Meye had'inki da wannan da har zai shigo cikin gida ki bashi taburma, har ki zauna a gabanshi kina wannan shashancin cin?.. Mey fa rabawa(K'ADDARA) ta raba ku har abada. Shiru tayi har Maman ta gama tana ta kok'arin shanye kukanta, ta sani da koh tayi bayani Mama bazata gane inda ta dosa ba. "Kiyi hakuri bazan sake ba. Kai ta k'ada tuni har tai laushi. "Ina kuje miki yaudara irin ta D'a namiji ne Salma,gaba in kina mishi haka sai ai abin kunya. Shiru tai tanajin wa'azin Maman kawai. G'yale ne kusan kala 5 had'add'u,tana washe baki ta fito dasu daga leda. "Ki zabi na za6a ki darje,dan zawarcin ki sai yafi y'an matanci a komai Salma, gobe kayan k'walliya zasu zo dan na bawa Hajiya Jidda kud'in kayan g'yaran jiki,ga wata yayi nisa da komai kin samu akan lokaci.. InshaAllah sai mun cike gurbin da muka rasa.. Ni da zakiji shawarata ma da an yaye Miemie a satin nan a mikata ga gidan su chan ya karata... Da sauri ta dago tana kallon Mama, Kat'seta tai da fadin "Eh man,bashi yake ikirarin yana kawo shi ba?.. Toh zamu mayar mishi da abarshi kawai. Kai ta hau girgiza ma Maman,Allah yaga ba mai rabata da Miemie sai aure. "Mama Miemie fa karama ce,kawai tai saurin tashi ne,koh fa wata tara bata cika ba.. Dan Allah kiyi hakuri,dan ba abinda zata t'sare min koh a makaranta. Harara ta aika mata, "Kina nufin da ita zakina fita?.. Kallonta take ta rasa amsar ba Maman. "Toh da sake wallahi, ba yadda za ai ina tufka kina bin bayana da warwara.. Zawarci da goyo?.. Toh da sake,dan ba mai gani ya kulaki alhalin kina sa6e da y'a. "Aikina fitarshi ta naga dama ce,in ma kince baza'a mayarta ba ni zan na miki renon,aje a dawo lafiya. Shiru tai tana jinta kawai. Washegari sai ga kayan k'walliya jibgi,su mascara, eye shadows,su sabulun g'yaran fata harda su man gashi,ga haddun man gyaran jiki,lalle Mama da gaske take. Shi kam tunda ya koma da yazo k'wanciya yake tuna dazu,lalle in Salma tasan wata toh bata san wata ba. Tazo k'wanciya taji karan wayanta,agogo ta duba, tasan ba mai mata haka sai mutum daya. Badan taso ba ta d'auka, sai dan jin dame yazo. "Naji kije makarantar, amma bisa sharad'i uku.. Baki ta bud'e cike da mamaki,wai koh ya manta bata karkashin ikon shi ne yanzun? Dan dai taji sharad'in tace tana ji. "Good. "Na daya kafarki toh kafar Miemie duk inda zaki shiga. "Na biyu ba zancen yaye sai Miemie ta cika shekara biyu kamin kiyi komai. "Na uku,fitar ki sai da nikaf da hijab,sannan ni zan sama miki mai kai ki a Napep ya d'akko ki in kin gama, dan ba ko wanne kato zai na d.. "Ka ga malam,ka bari ka fad'awa Miemie wannan dokar taka ba wai ni da nake Salma ba... Dan ba y'ar ka bace ni,ni nake da damar t'sara rayuwata yanzu ba kai ba. "Abu daya nasan na yarda zan iya shi,shima dan hakkin ka ne dole,shine yaye Miemie,zanyi yadda kace, sauran kuwa ba huruminka bane... Wayar yabi da kallo baki sake jin ta kashe kit.. Lalle Salma ba ta so zaman lafiya ba a garin nan, amma zata jidi mamakin shi. Dan shi tai mishi daidai ma da zata tafi makaranta. Tun daga ranar ya daina kiranta a ganinshi zata damu ta bashi hakuri ayi yadda yaso,sai dai ta daure ita. Ana haka ranar Abba yace ya batun makarantar da yace zai koma?.. Kanshi t'saye yace ya ma Abban ai ya fasa. Nan ya bud'e mishi wuta kan bai isa ba,duk haukar da yake ranar ya samu labari

Table of Contents

Chapters

41 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});