Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 5

Chapter 5

A Bakin Aurenki Book 1 Complete Hausa Novel – Salma’s Painful Return 1,251 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

suka yi hanyar fita a shagon,a hankali ta dago mishi hannu halamar _bye_. Kai ya k'ada mata shima ya dago mata nashi. Tai k'walli da Ja'afar ta ji dad'i,har aka je gida bata umm ba um um,sai Ummi ke ta zuba kamar kanya, yadda zata zuba wanka a bikin Aunty A'i har ta kule. Da dare sai ga yaro wai ana kiran Salma. Rai had'e ta k'allo yaron, "je kace bana nan... Shiru tai ganin yadda mama ke mako mata harara, "anya yarinyar nan kalau kike kuwa? Wato sai dai ai ta min asarar hoda da kazal a banza ina tufka kina min warwara koh? "Farin jini Allah ya bayar kina ma kanki bak'in ciki? Haka zan ta barar miki ni baki ban bare na maida g'urbin abinda na fitar Salma?.. Maman ta k'allo da mamaki,toh rokon samari mama take so ta fara komai? Allah yaga ta t'sani fita zance. Amma ganin yadda mama ke wanke ta yasa ba shiri tace ma yaron "yace ma waye?.. Kai ya daga mata,"wai ince inji "Ja'afar in kin tambaya... Ai koh karasa wa nai ba ta mike,tuni murmushi ya maye g'urbin 6acin rai, da k'allo mama ta bita, kamar ba ita ce yanzu ba. Yau kam ga su Salma harda mit'sika hoda da _lips stick_ har ta d'au hijab ta kara k'allon madubi,kawai sai ta janyi g'yalen Ummi tai waje. Shine kuwa yana jingine da gidan,wani murmushi ta saka na farin cikin kara ganinshi a daren. Da sallama ta karasa d'uk da ba wani haske gun sosai,amma sai dan sinke kai take kamar rana. Bayan sun gaisa kowa yai shiru kamar basu abin fad'a. Chan dai ya nisa ya miko mata ledar hannunshi. Kamar mai neman ba'asi ta t'saya bata k'ar6a ba. "Ajiya na kawo kimin zuwa gobe ne,ba wani abun ba naga kina tsoro. Murmushi tai kan ta amsa tana k'allon Ummi zata wuce,koh ci kanku bata ce ba ta shige gida. D'uk sai Salman taji wani iri,Ummi sam taki jinin Ja'afar ta rasa dalili. Ba jimawa yai mata sallama dan ya rasa abin fad'i shima. Dama da Garba ne yau kam da zai iya fad'in komai ga Salma. *** Tunda daga lokacin Ja'afar ke zuwa gun Salma jefi-jefi,d'uk da har yanzun bai furta mata so ba,amma ita a ganinta d'uk acikin so ne. A k'wan a tashi gashi har ta kammala secondary, wannan itace tafiya mafi tsawo da Salma tai bata ga Ja'afar ba,kusan wata bakwai. Tun tana damuwa har ta hakura ta rungumi karatun ta na fita. Gasu yau sune a gida,d'uk an rame anyi baki. By Feenat Ja'afar. [7/21, 10:10 PM] Feenat Ja'afar: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 10_Babban tunaninta bai wuce d'uk t'sawan lokacin nan da aka diba ba Ja'afar ba labarin shi ba,tasan yakan je mata ziyara makaranta koh a t'satt'saye ne,ga ita ba waya ba balle ta neme shi koh lafiya? K'wana biyu da dawo wa yau d'ai ta kudiri niyar fita jin ba'asi,koh Garba in ta gani. Hijab d'in _mss_ d'inta har kasa ta sa harda nikaf. Sai d'ai har ta gama zagayen layin ba wanda ta gani ciki,kawai burinta ganin Ja'afar ne. Iyanzu kam tasan tai nisa kan sonshi ba kad'an ba,sai d'ai ita yanzu ta fara tantama. Har zata juya ta tuna da shago,d'uk da tasan yanzu ba kasafai yake zama ba tunda ya samu g'urbin koyarwa. Sai dai tai chan d'uk bata tunanin ganin nashi. Daga d'an nesa ta t'saya kusa da wata bishiya ta d'an kare ba mai ganinta, da sauri ta juya tare da dafe kirji,zuciyar ta sai bugawa take da k'arfi. Yanzu ta samo amsarta da kuma kokwantan ta da ya zama gaskiya... Bata aune ba sai jin hawaye tai na bin kuncinta cikin nikaf d'in. A hankali ta fito daga bayan bishiyar tare da kara k'allo shagon. Murmushi yake harda darawa, ita kuma budurwar sai washe mai baki take tana ta mai zuba,rike yake da hannun wata y'ar k'yak'yawar yarinya fara kamar yayarta. Ji tai wani abu ya tokare mata kirji,da sauri tasa hannu ta dafe gun,ga hawaye yaki ya d'aina malala. Lalle tai wautar kin kula kowa sai Ya Ja'afar da bai furta mata so ba. Ido ta rint'se ganin ya d'akko mata wani had'adan net purple yana bata,wato har kalar da yasha sanar mata yana so ya bata? Tai imani mai irin wannan zankadediyar budurwar fara ba abinda zai da ita Salma baka. Hannu tasa ta cikin nikaf d'in tana goge hawayen dake zuba mata. K'allo sun da zatai taga Ja'afar ya zuba ma inda take ido,har budurwar na k'allo itama,da sauri ta juya gabanta na fad'uwa, kar dai ace ya gane ta? Tab,da k'wa ta bada kanta wallahi. Juyo wa ta kara,sai karaf suka kara had'a ido da Ja'afar. Ba shiri ta tare mai adaidaita ta shige,tana k'allo ya bi napep d'in da k'allo yana girgiza ma budurwar kai. Kawai sai ta sa kuka mara sauti tare da cire nikaf d'in. Lalle tai wautar zurmuwa ga soyayyar Ja'afar, soyayyar da ba'a ma bayyana mata ita ba... Ya Ilahii. ************************** "Oh! Man Ja'afar, dama kana k'allon mata har haka? Bafa koh kiftawa? Murmushi yai mata tare da girgiza kai, "Hala tai kama da Salma ne? Danma da hijab ga kuma nikaf.. "Kusan hakan ne, jikina ya bani kamar Salman ce kam..amma nasan ba ita ba ce ma. Dariya ta danyi har hakorinta farare suka baiyana,kan tace "sannu _Romeo_ toh, ni sallameni kan Amal ta fara neman mamanta, amma ina mamakin yadda ka iya zaben kaya da color, halama kana son _purple_? Murmushi kawai yai mata,kan ya k'ada mata kai halamar eh. Ita kam Salma tana zuwa gida ta taho da yaro a kofa ya kaima mai Napep kud'in shi. Allah yaso ba kowa t'sakar gidan mama na d'aki. A katifa kawai ta zube ta sau kuka,sai da tai mai isarta tai shiru tana maida numfashi. Chan kuma kamar wacce aka t'sikara ta mike zaune. Tabbas Ja'afar bai ta6a nuna yana sonta ba kam,d'uk zuciya ke yaudarar ta. Asalima da "K'anwata" yake kiranta, kila hakan ne tun da,ita kad'ai ke kidanta, gaba d'aya ta gama kore masu sonta ita a dole ta riki Ja'afar. Hawaye ne ya kara zubo mata tunawa da yadda yake washe ma budurwar nan baki. Tasan yadda Ja'afar yake a gaban mata baya wargi,baya sake fuska ma bare har yai musu irin wannan tad'in. "Tabbas budurwar sa ce,nai wauta ni Salma... "Lafiyar ki kuwa kike maganganu ke kad'ai ya sabuwar kamu? Kai ta dago jin batun Ummi tana wannan y'atsine matan. Sai dai ganin irin yadda idon salman yadda yai ja,ga kuma hawaye yasa ta mat'so "Mey ya faru kike kuka haka?.. Ai kamar mai jira a ta6ota ta kara sa wani kukan mai sauti. Tuni kuma sai Ummin ta zauna tana lallashi da fad'in lafiya? Ita de sai kukanta take baji ba gani. Tashi Ummin tayi,"bari na fad'o ki da mama toh,kila k'ya fad'a mata ita... Da sauri ta rike mata riga, "ni ba komai.. Marata ke ciwo da bayana kawai. T'saki Ummin tayi, "Allah kina da aiki a gaban ki Salma,kukan jinya sai kace wata yarinya. Ita dai tana jinta ta karaci kardinta tai waje,a hankali ta zame ta k'wanta,sai sauke ajiyar zuciya take. *By* *Feenat Ja'afar* 庐*NWA* [7/22, 12:02

Table of Contents

Chapters

41 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});