Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 13

Chapter 13

A Bakin Aurenki Book 1 Complete Hausa Novel – Salma’s Painful Return 1,252 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

dan sharad'in dazu yana kan ki.... Da sauri ta dago ta k'alleshi, tuni taji kukan ya kafe,sai ido da ta kafe shi dashi, shaf ta manta wani sharad'i ne ma? Tuni ta tafi duniyar tuna abinda ya afku ka ta fita. Garba ne ya katse mata tunani da fad'in "haba dai dan Allah? Wannan sharad'in bai k'yautu a gun ka ba Ja'afar.. Aure ya fice wasa fa.. Ka janye sharad'in nan tun kan kowa ya ji ku koma auren ku.... Da sauri ta k'allo Garba,duk ta kasa ta6uka komai, Mey Garba yake nufi da su koma auren su? Yaushe Ja'afar ya sake ta?.... Bai furta ba sai dai in yanzu.. Cikin muryar kuka tana ka'rkarwa tace "bai sake ni ba Garba, auren mu na nan... Koh yanzu ya furta?.. Banji ba Allah... Ni bai sake ni ba...bai sake ni ba.. Sai ta karasa tare da fashewa da wani kukan mai ban tausayi. Ido kawai suka zuba mata, tamkar zararriya haka take magana. Duk sai ta karya musu zuciya, barin gogan,har bai san ya je gareta ba,da zummar dago ta yaje ya lallashi abarshi,sai dai kamar wanda aka t'sayar ya d'auke hannunshi, baya ya koma yana rint'se ido... Tabbas yanzu saki ya gifta a tsakani,bai da _right_ na ta6ata,tabbas bai dashi. A hankali ya furta "Salma kin cuce mu... Kin fara dasa katanga a tsakanin mu... Ban san da abinda na rage ki ba Salma...ban sani ba, dazu a yadda nake jin zuciya ta,wallahi dan banzan doka naso na miki,Allah ya kareni da yin kuskure. Baya ya juya mata,kan ya k'allo Garba. "Dan Allah ka kaita gida gani nan zuwa... Waje yai ya barsu nan,Shikenan ta tabbata,ba makawa Ya Ja'afar ya sallama ta.. Ai tuni ta kara jiniyar kuka,dak'yar ta tashi sukai waje da Garban. Sai duba Yayan nata take koh zata ganshi. "Muje Salma,InshaAllah komai zai daidaita,.. Juyowa tai ta sadakar da yai nisa... Yana k'allon su har suka kule kan ya fito a inda ya 6oye a bayan bishiya. Harda goge y'ar k'walarshi... Salma kinyi aiki. By Feenat Ja'afar 9/29/16, 9:06 AM - Queen Safiyyert馃憫: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 19_"Toh a garin yaya haka ta faru? Fita kukai?... Tambayar da baba ya jeho musu kenan bayan Garba ya kawo ta ya dakko Jaafar shima. Kukanta kawai take,ita burinta ya kara maimaita sakin, kuma yaushe ya mata?. "Salma komai mukaddarine fa daga Allah,ba kuka zakiyi ba, kiyi adu'ar Allah maida muku alkairi kinji... Kai ta dago,ido duk yayi luhu-luhu, ta dubi Ja'afar, kanshi na kasa,cikin muryar kuka tace "Abba cewa yai fa ya sake ni... Wallahi ba dagangan na bari haka ta faru ba.... A zabure Mama tace "ya sake ki?.. Kai ta k'ada tana dan k'allon Abba da yai shiru yana k'allonta. "Ni dai banji lokacin da ya saken ba kuma.. Ta karasa da dan kukanta. Abban ta d'aure mai kai, chan ya k'allo Ja'afar, "Mey take fad'i ne Ja'afar?... Sam ban gane inda ta dosa ba.. Kai ya kara d'ukrawa,kan ya dago,mama in banda harara ba abinda take sakar mishi. Ya sani da dole su Abba suji. Cikin nut'suwa ya hau zayyanawa Abba halin da Salma ta t'sirar mishi,har zuwa kawo kararta gun Mama, kawo yau da abin ya faru.. Tsananin mamaki Abba kasa cewa komai yayi,wai Salman sa ce da wannan d'anyen aikin? Chan dai ya numfasa tare da fad'in "Innalillahi Wa'ina Ilaihirraji'un... Kuma kin fita d'in Salma?.. Baya ta fara ja tana k'ada kai, "Abba dan Allah kai hakuri,bazan kara ba... Murmushi Abban yai na takaici.. Ya ma rasa mey zai wa Salma ya ji dad'i.. Duka? Kai ya k'ada. "Ni meye nawa? Ba dai kin fanshi fita sama da aurenki ba?.. "Wannan shine sakin Salma... Tunda har kin fice bayan yace *A BAKIN AURENKI*.... Kai ta dago da sauri.. Saki kuma? Daga fad'in hakan?... Kawai sai ta sa musu kuka, "Dan Allah ya Ja'afar kai hakuri, Allah bazan kara ba,Abba kai hakuri... Cikin t'sawa yace "tashi ki bar wajen nan kamin nai miki lilis koh na huce... Kasa motsawa tai,ai da zafin nama Abba yai kanta da takalmi,Mama ta tare, amma duk da haka sai da mummuka mata. Dak'yar Ja'afar ya lallaso shi. "Kin wa kanki toh Salma,dan dole kizo ki bar gidana, wallahi ba zaki k'wanar min ba... "Haba wai Malam dan Allah.. Waye baya kuskure a rayu.... "Kimin shiru kema, dan duk laifinki ne,tunda kinsan irin shegantakar da take aikatawa, amma wai ki kasa sanar ni na d'au mataki.. Jan Salman tai d'aki tana bashi hakuri,dan sai ya iya had'awa da ita. Sai da ya gama sababinshi kamin Ja'afar ya hau bashi hakuri, "InshaAllah bazata kara ba Abba, nima na rasa abin yi ne shi yasa nai hakan.... "Ni fa banga lefinka ba Ja'afar, kamin dai dai.. Gaba nasan bazata kara ba. Shi dai kawai hakuri yake bama Abba. Abba ya tambaye shi kan saki nawa ne? Yace daya. Tashi yai yace ya jira shi,sai yace bari yaje gida shima ya d'au machine sannan ya sanar musu. D'aki Abban ya shiga bayan Ja'afar din ya fita. "Amma kin bani mamaki Allah Rabi... Ashe ba zaki zama mai g'yara wa ba sai dai kiyi shiru? T'sawan lokaci yaro yana hakuri da halin yarinya amma kina sane?... Shiru tai,sai da ya gama chake ta ta hau bashi hakuri. "Ke kuma tun yanzu har har kin kone tun kamin ki tafasa koh Salma?... Kai ta k'ada tana yai hakuri, "A'a, ni ai nawa mai sauki ne,koh dai ki g'yara halin ki,koh ki shiga hannu na... Bansan lokacin da kika sauya k'yak'yawar dabi'ar ki ba Salma?.. Sosai yai mata fad'a cikin zafi zafi kan ya kara da ta shirya,dan ya rantse bazata k'wanar mishi a gida ba... "Haba malam,ina zata toh?... Cikin fad'a yace "gidan mijinta... Koh da magana?.. Kai ta kada,kan tace "sakin fa?.. Sannan wane gida bayan ya kone?... "Eh a konan nan zata zauna akwai daki a waje yace da bai kone ba,sannan ki sani igiya d'aya babu a tsakanin ki da shi. "Ki gode Allah kin samu mai sanki,yau da wani ki kai wa haka sai ya tabbatar da ya miki shegen duka kan ya baki saki... Amma shi kok'ari yayi ma a take yace min ya mayarki. "Abu d'aya zan iya fad'a miki Salma... Wallahi, duk ranar da zaki maimaita haka,ki kuma k'waso kafa ki zo min gida sai na 6a66alla kafarki... Baki sake Mama ke K'allonshi, ita kam yau kad'ai ta kara mugun tsoron Abba,tasan a yadda yau ya daketa tsaf zai iya 6alla tan. By Feenat Ja'afar. Like 路 1 路 Reply 路 Report 路 Jul 29 Zeenat Yakubu tnx 1st 2 cmmnt Like 路 Reply 路 Report 路 Jul 29 Feenat Ja'afar Novel's *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 19_"Toh a garin yaya haka ta faru? Fita kukai?... Tambayar da baba ya jeho musu kenan bayan Garba ya kawo ta ya dakko Jaafar shima. Kukanta kawai take,ita burinta ya kara maimaita sakin, kuma yaushe ya mata?. "Salma komai mukaddarine fa daga Allah,ba kuka zakiyi ba, kiyi adu'ar Allah maida muku alkairi kinji... Kai ta dago,ido duk yayi luhu-luhu, ta dubi Ja'afar, kanshi na kasa,cikin muryar kuka tace "Abba cewa yai fa ya sake ni... Wallahi ba dagangan na bari haka ta faru ba.... A zabure Mama tace

Table of Contents

Chapters

41 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});