Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 34

Chapter 34

A Bakin Aurenki Book 1 Complete Hausa Novel – Salma’s Painful Return 1,264 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ya sunan shi? "Sunana Ja'afar".... Kallonshi take da mamakin jin sunanshi, koh dai bataji dakyau bane?... Kat'seta yai da fad'in "K'anwata kuma Nabila,Umman mu tace sai anjima zamu shigo kar mu tashe ki a bacci. Murmushi tai mishi yace ya tafi.. "Ja'afar... Ido ta rint'se jin maigidan ya kira sunan,ba shiri ta d'au abincin tai kitchen. Bayan sun gama komai yace suje bangaren uwar gida zai magana dasu. Batai zatan da kishiyoyi masu kaunar kishiyar su ta ra6e su sama da matar Alhaji ba,sosai tai mata bazata,tun tana d'ari-d'ari har ta saki jiki da ita da yaranta, musamman Ja'afar.. Yau Miemie ce tazo mata,sai murna take taga Auntyn ta. Duk babyn ta rame,yaye bai amsheta ba. ''Miemie, ga nan Abdul yazo ku tafi gun Mama koh?... Kafad'a ta make halamar taki tana neman kuka, "Yi hakuri gobe zanje gida mu taho koh?.. Kuka ta saka mata baji ba gani, sai mak'e kafad'a take tana ita "um-um. Sai ta sallami Abdullahi kan gobe yazo ya d'auke ta, har ya jima da tafiya Miemie bata bar kuka ba. Sai um-um kawai take fad'i, suna haka Alhaji ya shigo,duk yai kicin-kicin da fuska, cikin fad'a- fad'a yace ta lallasheta man,shi baison hayaniya bare ta yaro... Baki sake take kallonshi,kaya ya ajiye ya juya ya fice harda dan tsakinshi,toh mey yake nufi?... Y'arta ta d'auka ta sa6a a baya sukai kitchen tana fad'in tai shiru ba inda zata toh,kan aje ko'ina sai ga nan Miemie harda dariya tana bata labarin Mama cikin gwaranci. Har dare ba Alhaji ba duriyarshi,abinci ma sai Ja'afar ya turo ya d'auka. Suna k'wance Miemie sai k'allonta take,gani take kamar guduwa zata yi ta barta. Kanta ta shafo tana mata murmushi, "Yi baccinki my Miemie, ina nan fa tare da ke kinji?. Kai ta daga mata tana k'allonta. "Antee... Kai ta dago kan tace "Na'am Miemie nah... "Abba... Tsam tai tana k'allon Miemien,Abba? Ta nanata a ranta. Murmushin dole ta k'akalo tana fad'in Abba yana nan Miemie,bata aune ba taji ta kara fad'in Abba... Hawayen da take makalewa ne suka zubo mata,da halama yanzu Miemie ce matsalar ta,dan zata dawo mata da hannun agogo baya. Da dabara ta d'auke hankalinta daga tunanin Abban ta hau lalla6ata har tai bacci. Photocopyn Ja'afar ce Miemie,barin yanzu data kara girma, tunani take koh dai Ja'afar har yanzu baya zuwa gida, laifinta ya shafi Miemie? Dan tasan sai Miemie ta kwana biyu bata ganshi ba take nemanshi haka. Tana nan har maigidan ya shigo,sai wani k'allo yake aikama Miemie wanda ta kasa fassara shi. Tun daga ranar ya zamana in dai Miemie zata zo,toh fa zata rasa gane kan maigidan, ta rasa dalili, musamman in tai la'akari da hadithn hausawa na Duk mai son uwa toh yaso d'iyanta. Ranar har ta kasa d'aurewa tai mishi magana, amsar da ya bata ta jima tana sata hawaye. Ga Miemie da kulafuci bare tace kar a sake kawo ta,asalima duk randa tazo fara'arta karuwa take. Sa6anin in tazo mata,data gane sai take d'akko ta duk randa bata da girki su k'wana, ranar da maigidan yake da ita su wuni ai rabuwar kuka har uwar. Allah yaga Miemie kadai take gani taji sanyi a ranta. Ranar suna fira a bangaren uwar gida take mata korafi kan halin maigidan akan Miemie. Murmushi tayi kamin tace "Sai kinyi hakuri da halin Alhaji Salma,ba tone- tone ba,a'a kawai dai ya kamata ki sani, Alhaji sam baya son yara,musamman hayaniyar su,hakan yasa ya d'aurawa kansa kin haihuwar k'arfi da yaji, nayi ta zaman takaicin halin nan na Alhaji har t'sawan shekara bakwai,a lokacin aka tada kayar baya kan sai ya kara aure tunda ni sun zuba ido shiru. "Hanna ta shigo itama ta shekara biyu shiru, ni dai nasan kusan kullum yakan tasa ni da Hanna dan shan maganin daukan ciki. Ana nan ranar wata kawar Hanna tazo suna jajanta ko dai matsalar gun mijin ce,toh a ranar dai asirin Alhaji ya tonu,dan kawar Hanna taga magani tace na hana d'aukar ciki ne. "Ranar muka mishi tawaye har Hanna,in takaice miki yace shi bai shirya haihuwa ba yanzun,anan sukai baram-baram da Hanna ya bata takardar ta. "Haka sauran mata biyun kowa tazo zai fad'a mata ra'ayinshi, da taga bazata iya ba zata fice, duk kuwa da tarin arzikin shi,a lokacin muna da shekara kusan sha uku da aure,koh mai zaiyi na daina shan magani, hakurina ya kare,nan na kai kara gun Hajiyarshi. "Ya saduda muka haifi Ja'afar, yace daga nan ta isa haka,wai incigaba shan magani,a gabanshi zanyi kamar nasha, daya kauce zan zubar. Koh shekara Ja'afar bai ba na samu cikin Nabila,cikin da a kullum sai naga tasku gun Alhaji,gar da gar zai nuna bai kaunar su,barin in Ja'afar na kuka,haka nai ta hakuri har na haifi Nabila. "Yanzu kam magani sai dai shi yai tasha,amma banda ni,kinga Nabila har ta shiga shekara ta biyar. Tsam tai tana tunani bayan kammala bata labarin waye Alhaji, ita ba kullen ne yafi damunta ba sama da rashin son haihuwa.. A kalla yanzu ta doshi wata na biyar a gidan nan amma ba bayani,sam bata kawo wani abin ba,ashe wannan ne dalili?.. Bazata iya tuna ranar fitarta ta karshe a gidan nan ba,tun kwa bayan aure sau daya taje gida sai dai aukin waya koh azo mata, lalle duniya labari. "Zaman hakuri kawai zamuyi Salma,sai adu'ar shirya in da rabon zai gane, amma shawarata gareki ki rike y'arki, dan kar kiyi sakiyar da babu ruwa tun kina yarinyar ki dake,shi ba ruwanshi. Kai ta kad'a mata,Allah sarki Ja'afar, ta tuno lokacin data fara period tana kukan samun ciki yana murna. Ta tuno da abinda yace mata "Allah sa Miemie ta samu k'ani a kusan nan... Ta tuna data hau bori ya hau lallashinta, harda alkawarin shi zai mata reno in bata shirya ba... "Ba kuka zakiyi ba Salma,muyi ta adu'a. Hannu takai fuskarta, ashe kuka take bata sani ba. By Feenat Ja'afar. [8/7, 11:08 AM] Feenat Ja'afar: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 38_Ranar sakwa-sakwa ta yini tana tuna halin Alhaji, bai da mugun hali koh daya sai na bakin kulle da kin yara,bayan nan baza tace ga mugun halinshi ba. Zataso sanin wane hali Ja'afar yake ciki a yanzu,dan tabbas tasan ya zuciya da ita,tunda gashi ance koh wajen Miemie baya zuwa sai aike?.. "Mey nai kenan?.. Mey nayi ni Salma?.. Mey yasa ban iya jure zama ba aure ba a rayuwa kamar yadda yaso muyi..mey yasa?.. Juyi tayi tana hawaye, Kila rabon Miemie kadai take dashi a duniya,tasan kuma aure dai ana yinshi ne dan abu biyu,samun zuri'a na daga ciki, gashi ita anan ana son a haramta mata. Tabbas d'aukar y'arta shine babban mafita a game da yadda take jin son ta haihuwa a yanzi.. Wayarta ce tai ruri, a hankali ta goge hawayenta ta tashi, "Billy" taga a rubuce. Da sauri ta saita kanta kamin ta daga. "Sarauniyar kirki kina gida ne?... Dariya ta danyi kan tace tana nan.. "Toh ina kofar gidan ki yanzu haka. Da sauri ta tashi dan g'yara fuska tana fadin gata nan zuwa. Sai da ta tabbatar da ba mai gane tai kuka kamin ta fita kofa shigo da Billy. "Matar nan kinganki kuwa?.. Kin zama big madam da gaske fa. Murmushi tayi tana kar6an

Table of Contents

Chapters

41 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});