Chapter 33
Chapter 33
har Salma ke mishi murmushi haka. A zuciya yace "Babu... Sai dai kud'i kawai da sa kaya masu t'sada. "Kai fa,daga ina ba koh sallama?.. Cike da haushi ya kallota, "baki sanarshi ko ni waye ba ne?.. Kan Alhaji ya dawo,ba shakku yace "matata ce ita,zaifi mana k'yau in ka daina zuwa gunta Alhaji. Murmushi yayi Alhajin,kan ya kallo Salman, "sai kinji ni kawai.. A takaice ya k'alli Ja'afar din,ba sai an fada mishi waye ba,halamu ya nuna tsohon mijinta ne,har zaga wa tai ta rufe mishi tana daga mishi hannu d'auke da murmushi, har ya kule tana daga mishi hannu kan ta d'au kayanta koh ta kanshi bata tai hanyar gida,da zafin nama. "Wato abinda ki ke kenan tun bayan tafiya ta shine yasa ki ka kashe waya? Salma mey yasa kike son ki 6ata min rai wai?.. Jibi fa shigar ki,ji gashi a waje,wace iriyar rayuwa ki ka za6a mana? Cike da fada tace "Wace iriyar ka za6arwa kanka dai Ja'afar.. Ya zaka zo kana fad'an wata iriyar magana mijin da zan aura?.. Karan nan bazan dau abinnan naka ba wallahi, aure zamuyi dashi nan da wata biyu... Sai kayi abinda zaka yi. By Feenat Ja'afar. [8/7, 11:07 AM] Feenat Ja'afar: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 36_Kan yai k'wak'waran mot'si ta shiga gida tare taru kofa harda sa sakata. Jiginna tai hawaye na neman zubo mata,daga yar bular dake jikin kofar ta leka waje,kofar gidan yake kallo jiki a sanyaye kamar yasa kuka,juyawa tayi hawayen dake makale mata ya zubo,dak'yar ta seta kanta ta shiga ciki rai cike da tausayin Ja'afar. Kusan kullum zai zo ba zuciya dan bata baki akan Alhaji tana mishi wulakanci,shi kam Alhajin har dariya yake bashi wani sa'in, dan baijin da abinda zai iya rabashi da Salma a dai dai lokacin nan,sai dai jin saki uku ne kawai sai ya bar jin komai,iyaka ma yai ta tusa ma Ja'afar din bakin ciki in ya gansu da kalamai ma Salman. Biki ya karato ga makaranta,amma haka duk week end daga Zaria zai zo kan batun Salma ta janye zancen bikin nan. Duk ya fita a hayyacinshi duk akan auren Salma. Da halamu ya fara hankalin daina zuwa gun Alhajin,sai dai in yazo ya tsaya chan gefe sai tazo shiga ya tare ta da magiya. Yau saura k'wana biyu biki, sai gashi shi da Garba,dawowarsu daga gidan g'yaran jiki kenan ita da Ummi. Turus ta ja ta t'saya ganin Ummi ta wuce ita ya tare mata hanya. "Ka ga yau bani da lokacin jin wannan mahaukatan zantukan naka,jibi iyanzu na d'aura aure, ya kamata kasan inda dare ya maka, sabuwar rayuwa zan fara,saboda haka kai yanzu ya rage ma,danni yanzu baka gabana... Kai ya kad'a mata, "Karan nan bazan hanaki aure ba Salma,sai dai ba da Alhaji ba. Baki sake take kallonshi, Garba ya nuna, "Garba zaki aura Salma,kimin wannan alfarmar. Kai ta dauke daga kallonshi ta k'alli Garban wanda shima ya cika da al'ajabin kan maganar Ja'afar. Sai ta girgiza kai da murmushin takaici. "Tanan kuma ka bullo min?.. Auren kisan wuta Ja'afar? Lalle kayi nisa ba zakaji kira ba. Bayab hannunta tasa tana goge hawayen idonta. "Wai ka zata ni din auren kisan wuta zanyi da wanda zan aura?.. Kai ta kara kadawa, "Kai kuskure toh,dan ni aure zanyi na tsakani da Allah,ba wai nayi na fito ba Ja'afar.. "A'a Salma,ba haka ne nufi na ba.. Da muryar kuka ta tareshi, "Hakane man,haka kake nufi,wato ka kawo min abokin ka na aura bayan wani lokaci ya sake ni sai ka halartawa kanka ni koh?.. Baki sake duk suke k'allonta,ganin yadda hawaye ke zubar mata. "Jahilcina bai kai nan ba Ja'afar, a bazan ta6a abinda ka ke so ba, a gareni yanzu k'allon Yaya nake ma,da kuma uban yarinyar dana haifa, bayan haka.. Kai ta girgiza, kan tace "you mean nothing to me a yanzu kam.. Jin baice komai ba yasa taci gaba. "Banzaci haka daga gare ka ba Garba,a ganina in shi ya 6ata kai mey dawo dashi kan hanya ne, wallahi auren t'sakani da Allah zanyi, ku sani kuma auren so zanyi,wanda nake fatan mutu ka raba ne,dan Allah,dan kaunar ka da Allah ka bar bibiyata,dan Allah.. Shiru tai dan ganin shima idonshi ya taru da hawaye,da sauri ta shige gida tana goge hawaye.. Har ta shige yana binta da ido ba magana, sai hawayen da ya zubo mishi shar, da sauri yasa hannu ya share. Kafad'arshi Garba ya dafa, "kaji zancenta, tai mana fassara baibai,ya kamata kai hakuri ka bar kulata in har kana wa Allahn data had'a ka dashi. Kai ya daga, "InshaAllah.. ~~~~ Taro ne iya taro,taron shedar auren Salma da Alhaji Usman, daga inda yake t'saye a chan nesa da kofar gidan yana k'allon komai har aka shafa. Juyawa yai da jaka biyu hannunshi tare da sanya bakin glass dan 6oye sirrin dake idonshi. Yasan yanzu kam Salma ta mishi nisa. "Mama taki ta bud'e dakin fa,daga ina jiyo sautin kukanta Allah. Ta window Ummi ta leka,gata k'wance ta tasa tsohuwar wayarta a akan fuska tana razgar kuka, So ba karya bane Salma. By Feenat Ja'afar. [8/7, 11:08 AM] Feenat Ja'afar: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 37_Har aka kai amarya gidanta bata bar kuka ba,dayawa sun zata kukan na Mama ta cire Miemie ne, dan basa ji koh auren farkonta tayi haka. Kowa ya wat'se sai ita kad'ai, ko'ina take kallo a dirare, gida ne iya gida,tun bata fita ba ta zaga,yau gata a gidan da ba Ja'afar, ba kuma Miemie,tuni ido ya cika da kwallar tuna baya. Anya tai ma Ja'afar adalci kuwa?.. Anya bata ci amanar so ba kuwa?.. Ta sani da takai Ja'afar bango,hakan yasa bai kara waiwayarta ba,ta yuwu yai zuciya... Ido ta goge da sauri jin motsin za'a bud'e d'akin. Ango ne yasha babbar bunjima da rike da leda, bakin nan har kusan kunne,jan mayafinta ta kara yi ta rufe fuska. "Amarya! Amarya!!.. Ba k'ya laifi wai koh kin kashe dan maigida koh?.. Murmushi ta k'akalo mishi, zama yayi a gefenta tare da ajiye ledar a gefen bedside, bata aune ba taji ya yaye mata g'yale yana kallon fuskarta. Alwala yace ta d'auro suyi nafila,dan wai agareshi babbar kyauta ce ita daga Rabba. Sun gabatar da duk wani al'ada,sai dai har ango ya d'ane gado amarya tana t'saye a gaban madubi sai sininiki take,gabanta sai mugun fad'uwa yake tamkar wacce tai auren fari. Murmushi yayi da kanshi ya taso ya karaso har gaban madubin tare da kamo hannunta. "Muje ki kwanta haka dare nayi sosai.. Kamar yarinya ya kwantar ta gefen shi yana kallo da murmushi. Salon ya sauya,tuni ta fara digar da hawaye,shi kadai yake kid'anshi yana rawarshi,sai dan sautin kukanta dake fita kad'an-kadan,wanda a gareshi tamkar zigi take mishi. Kai ta juya ta kallo Alhajin dake bacci hankalinshi k'wance,abu uku sun hanata bacci,na farko kukan zamanta ta wani ba Ja'afar ba,na biyu tunawa da Miemie, na uku minsharin Alhaji.. Har gari ya waye bacci sai jefi-jefi-jefi ke dibanta,sam taki jinin minshari kusa da ita,tsaf yake hanata bacci. Shikam da farin ciki ya tashi irin na sabbin ango,ita kam da ido kawai take binshi. Tara sai ga yaron uwargida ya kawo abinci,da fara'a ya gaida ta,kanshi ta shafo kan tace
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41