Chapter 25
Chapter 25
fara magana. "A lokacin chan baya ai bakaji zance na ba,dake idon ka a rufe yake,na sanarka baka san mey wani irin hali zaka jajubo ba,kace kai fa gaji ka gani sai Bintu.. "Malam ni shawara zaka bani,in babu zanyi gida. Dariya ya cigaba dayi,kawai sai ya zuciya yai gaba. "Ma had'u in ka gama,dan hankalina yai kan Salmatee. "Wash Allah bayana,Bintu!...Bintu!!.. Tamkar ba kowa a gidan ka ke ji sai karar fankar sama dake kadawa a parlourn wacce bata hana gumi t'satsafo mata ba. Rarrafo wa tai zuwa kofa,iya karfinta ta kwalawa Bintun kira,ji take tamkar zata mutu dan azabar ciwo,tuni ta fara kuka tana ambatan Allah,tasan koh zata mutu Bintu bazata taimake ta ba,fatan ta Allah ya hankad'o mata Ja'afar koh wani ya ceceta. "Wayyo Ya Ja'afar, Innalillahi.. Bintu.. A razane ya karaso cikin gidan dan jin ta ambaci Bintu cikin kuka. "Subhanallah.. Salma.. Ina Bintun toh?.. Da sauri ta dago,tana ganinshi ta kara fashewa da kuka tana cije le6e. gaba daya ya tallafota yana aikin sannu sannu. Waya ya ciro dan neman Garba ya kaisu asibiti, tana ta ringing shiru.. Da rigarshi ya goge mata gomin dake tsatsafo mata, "Bari na ga koh bacci waccan take na taso ta. Hannunshi ta rike gam tana girgiza mai kai, Kanta ya shafa, "ki d'aure Salma,bari na kirata kinji. Dak'yar ta cika shi yai dakin Bintun, dan ji take yana tafiya zata mutu. Bata parlourn, sai ya bankad'a daki,tana mike a kan gado taja rabin bargo tana dariya kasa-kasa tana charting hankalinta yai gaba. A sukwane yai kanta,bai wata-wata ya sinketa da mari mai rai da lafiya,a gigice ta mike tare da dafe kunci,wayar ya warce, "Lalle haukar nan taki karuwa take Bintu,yanzu dama kina cikin gidan nan Salma take ta kakarin kiranki kamar zata mutu?.. "Toh ki biyoni yanzun nan waje, tana turo baki ta sakko kan gadon tana gunguni. Nishi take ta dafe d'ukkan hannunta a kasa, sannu yake mata da tausayawa,da harara Bintu ta bita da jin haushin akanta an mare ta. "Ka kira min Iya Shatu dan Allah Ya Ja'afar kar na mutu.. Bintu ya kallo dake maka musu harara, "Kizo ki kamamin ita na kira Iya Shatun, kamar bata so ta matso kusa,yana fita ta mat'sa tana jan tsuka,"aikin banza,dan kina wata shegiyar nakudarki akan hakan kika ja aka mare ni, wallahi za... "Eh dan Allah kazo yanzu mukaita asibiti.. Shiru tai jin Ja'afar na kokarin shigowa tare da matsawa gun Salman da sauri zata ta6ata tana sannu. A hankali ta janye daga hannun Bintun tai dan ciki kad'an tana nishi, da sauri ya karaso dakin yana mata sannu. Nishi take iya karfinta sukaji sallamar Iya shatu,tana dubata tace ai haihuwa ce tazo gadan-gadan, ya basu waje, ya siyo reza da sauran abin bukata. Gam hannunta na cikin nashi,ji yake tana cikawa in ya tafi zata mutu. Kanta ya tallafo yana ta d'aure, iya shatu sai k'allon ikon Allah take. "Kai hakuri Jafaru,zata haihu lafiya dan ina jin kan D'a, yanzu bazata ji komai naka ba sai adu'a. Kai ya kada harda guntun hawayenshi yai waje,yana fita Bintu ta d'aura a bayanshi. Iya shatu tsuhuwar ingozoma ce mai ritaya, da guntun hand gulf din zuwa awunta ta karbi haihuwar Salman. Allah ya taimake tazo mata da sauki inji Iyan,sai shigowa yai shi da Garba yaji ihun jariri,baki wangale zai dakin iya shatu ta fito k'ar6ar reza. Ummanshi ya fara mawa albishir sai Aunty A'i,tuni ya fesa cikin gidan su,da ance mey ta samu? Sai yace bai gani ba. Har aka kintsa komai basu kara ganin keyar Bintu ba,sai da zasu asibiti ta fito,shi kam baiya ma ta ita. Suna fita su Aunty A'i suka zo da Ummi,lokacin Bintun na t'sakar gida tana yankar farce,ita dey Iya sai mamakin karfin hali irin na Bintu take. Sallama suke ta manna musu bajon hauka,tuni Ummi taja dogon t'saki, taki jinin Bintu a rayuwa. "Banza y'ar bakin ciki kawai,toh sai ki had'iyi zuciya ki mutu ai.. Hannu Aunty A'i ta daga mata halamar tai shiru,ita k'wa da harara tabi su har suka shige. Sun dawo an duba suna lafiya ita da babyn ta,Ja'afar baki har kusan k'unne dan murna,yana makale da yarshi. "Um,Baban baby ba koh dan karar nan ma ta manyan yayu.. Kai ya sosa yana ma Aunty A'in murmushi, ba dan yaso ba ya mika mata ita. Kan kace mey gida har ya cike da dangi yan barka da yan unguwa. Sai dare ta samu tasa hakarkarinta dan hutu. K'allon babyn take mey kama da Abbanta, gashi kadai da dan _beauty points_ (dimples) tai gadonta. Murmushi tayi tana kai hannu kan kumatun babyn, Allah mai halitta. Murmushi yake musu yayin da ya shigo d'akin, sai ta daga kai ta k'alleshi, kai ta girgiza tana dan murmushi. Sallama ta uku yana musu kenan yana dawo wa,ta rasa wani irin kulafuci yake musu musamman babyn. Zama yayi yana shafo sumar babyn da farin ciki. "Oh ni kam,koh zaka je da ita in tai kuka sai ka kawo ta. Murmushi yayi yana kai baki kan dimple din babyn yana kissing. "Ba kinki barina na k'wana anan ba?.. Da kalar tausayi yace "yau dai daya naji dumin y'ata kinji? Sai ya marairaice fuska. Dariya ta dan mishi,kan tai magana ta jiyo Babah mai zamar mata tana ya fito zata zo ta k'wanta,taga sallamar bata karewa. Dariya suka sa kamin ya tashi yai waje. "Maza ki rika biye mishi ki debo ma kanki magana da kazamin goyo ai. Da rashin fahimta ta k'allota tana neman karin bayani. ***** ***** Yau suna,baby taci sunan Mama tun ran huduba amma ya 6oye mata. Sosai yau daya Ja'afar ya biya mama,harda mishi waya tana kwarara mishi godiya ba iyaka. Maijego tai ras abinta da Baby Miemien ta,sun fito sunyi k'yau sosai. By Feenat Ja'afar. Ai hakuri da wannan dan zani gidan Suna Salma.. Zuwa yamma in na dawo zakujini Lol.. 9/29/16, 9:17 AM - Queen Safiyyert馃憫: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 29_Suna ya wat'se kalau,maijego tai goshi,ak'wati guda Mama ta mata na suna sai na baba,ga Umman Ja'afar nata daban da tazo suna,chan gidan su Ja'afar su ma sun mata karamci,sai son barka. Wankansu suke cikin g'yara na musamman da Mama ta zage yi ma y'arta, albarkacin Miemie mama ta sakko sosai. Shirya Miemie take tare da taimakon Ja'afar din suna ta nishad'in su yau za ai yawan arba'in. Ta chakare sosai kamar yau ne sunan ita da Miemie. Baya ta juya mishi yana goya mata ita, "D'aure ta dakyau,dan kinga machine zamu hau.. Kai ta kad'a tana murmushi, Sai da ya zaga ko'ina yaga yayi kan ya bata majanyi tana mishi dariya, "A'a toh in baki iya ba ni sai na goya abata kawai... Dariya tai kan tace "Da kwa kabar abin fad'i agari kuwa. Jakar ya d'au mata ta d'au mukulli sukai waje,shima yasha sabuwar shadda abinshi. Bintu na t'sakar gida tana d'anne-d'anne a wayar da dak'yar ya bata. Da harara ta bisu harda dan t'saki a hankali. "Toh mu zamu fita sarauniyar charting.. Sai kisa mana mukulli a gida dan gudun kar a dirko kina sana'ar taki koh.. Tuni ta kara k'uluwa kuwa,ita dai an mayarta borar karfi da yaji a cikin gida. Hannu Salman ta dago mata halamar sai sun
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41