Chapter 16
Chapter 16
ta fito dasu tana duba wanda zata sa, _lace_ din sunan Ummi ta dakko wani karamin _swiss_ da aka sashi siyanshi dan dole. Sunan na manya ne, dan haka sai da kure adaka. Ba koh shakku ta fice, yau tun dazu taji gidan su Maman Ummi t'sit kamar ruwa ya shanye su,halamar mai gidan yana nan kenan,amma tunda ta fara jiyo hayaniya tasan yai waje. Gidan suna kam ya kayatu, sun samu abinda ake so tuni aka baje a faranti ana ci ana kora wa gulmar wata. Kan ta farga har 5 da yan mintina. Haka kawai taji gabanta na fad'uwa hankalinta yayi gida. Tashi tai ana fad'in ta t'saya k'ulli ya kare a k'ulla mata tana a bawa Maman Ummi. Sauri take ta zubawa, dan da y'ar tazara a t'sakanin su. Adu'ar ta daya,Allah sa Ja'afar bai dawo ganin koh ta fitan ba. Ta rasa dalilin da ya sa hankalinta ya tashi,bayan ita ta zabi hakan. Lekawar da zatai shine taci ka'ro da Ja'afar suka had'a ido. *WAIWAYE*... *************** ************** Haka yai ta juyi har kusan k'arfe biyu. Washegari haka ta tashi sukuku, ga fargabar Abba yau zai dawo,ga wani mugun mak'on Ja'afar da yake taso mata. Kai in ma ba wai bata kula bane gani take zazzabi ne a jikinta. "Salma... Dagowa tayi ganin mama a kofa,da mamaki fal fuska ta karaso ciki. "Wai har yau kukan nan ki ke Salma?.. Mey yaron nan yai miki ne haka?.. Hannu ta kai kan fuskrta,sam ba tasan tana kuka ba, da sauri ta goge tana k'ak'alo murmushin dole. "Mama ina k'wana.. Kai kawai ta kada mata. "Haba Salma,kar fa ki rako mata duniyar nan...kar ki zamo mace mai kulafucin D'a namiji duk k'wa wulakancin da ya mata man... Ashe ni ina chan jiya nai baccin farin ciki da aka rabu lafiya ba rabo bare ya kawo cikas a zawarci ashe ke kina nan kina kukan an rabu? Haba Salma, karan nan ne fa ki ke da dama ta biyu,tunda har ya sallame ki. "Maza goge hawayenki ki biyoni daki yanzu. Kai ta kada,a gaskiya ta fara mamakin irin kiyayyar dasu mama suke ma Ja'afar, wato har ma godiya ake ta rabu da alakakai?... Allah yaga tafi jin haushin kanta sama da haushin Ja'afar, in ma taji haushin shi toh bai wuce yadda ya k'ulle mata gida ya kuma tafi koh ajikinshi. By Feenat Ja'afar. Like 路 1 路 Reply 路 Report 路 Jul 29 Feenat Ja'afar Novel's *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 22_"Toh wa ya jawo?... T'sam tai yayin da zuciya ta tambaye ta, "Ni ce... Tabbas ni najawo, amma ba laifi na bane. Kuka ta fashe dashi,tabbas anci k'arfinta,ta ko'ina an mata dabaibayi da huduba gur6atacciya. "Gashi na jawo wa kaina saki biyu ba tare da na samo kan ba(kan Ja'afar).. "Oh ni Salma.. Ina tunani na yake da har na aikata wannan wautar?.. Ina son da nake ikirarin ina ma Ja'afar?.. Ina ya je... "Salma... Mama ce ta kat'se mata tunanin gaskiya da kira. Hannu tasa ta share hawayen ta,ta daga kai tare da fitar da iska dan daidaita nut'suwar ta. "Na'am.. Ta amsa kan ta tashi tai waje. "Gani mama, Kan gado ta nuna mata kan tazo ta zauna. Ba musu ta karaso. Kafad'arta ta dafa kan ta numfasa, "Kina ji koh Salma? Kai ta daga mata. "Baban ki yau nasan zai dawo,tabbas ya rit'saki nasan zai cid'a ki ne a banza. "Yanzu abinda nake so kiyi shine,ki je gidan A'i,dan mijinta baya gari ya tafi sari,ki barni in na gama lalla6a shi sai ki dawo,dan karan nan kam sai dai ai wacce za ayi, amma aure kin gama... G'wara a chanja hannu,tunda wannan d'in ba fus, bare ass,sai dan banzan dacin rai ba koh gidan kai... Hawaye ne ya zubo mata,ba da ban suna matukar kama da Mama ba,da tayi shakkun akan haihuwar ta... Mama na da kamasho a ta6ar6arewar aurenta kashi 70 acikin dari... Tabbas uwa uwa ce, amma su kam tasu uwar sai g'yaran Allah.. "Au,au,kuka ki ke? Dan nace baida gidan kanshi?.. Koh shi ya siya ya gina da gumin ajin?.. Yarinya ki duba yadda ake harka,y'an uwanki na shiga ta alfarma amma ke kin zama y'ar k'allo.. Ki farka a bacci Salma,dan rayuwar nan ta zo mu fafata ce. Kai ta k'ada tana goge ido,sai ta mike tai hanyar waje, "Bari na shirya zuwa gidan Aunty A'in, naga 10 tayi. Kai Maman ta daga harda washe baki, "Yauwa,ko ke fa.. Maza aje a shirya,ga nan abincinki a kitchen. Kai ta k'ada kan tai waje, da kallo Maman ta bita, ba abinda y'arta ya gaza a gareta,wa ma zai ce ta ta6a aure in ta fito da ita gari?.. Dole kud'in da ba taci ba da yanzu taci gun Salma. *************** ************** A k'wance take kan _3sittern_ Aunty A'i,in banda ciwan kai ba abinda take, "Tashi ga maganin kisha... Kai ta dago,Aunty A'i rike da kofi da _paracetamol_. Bayan tasha ta g'yara zama,d'uk gidan bata jin da wanda bai ta6a kushe mata Ja'afar ba sai Abba da Aunty A'i. Hawaye ne ya zubo mata,kan kai duk'e tace "ban san mey Ya Ja'afar ya t'sarewa su Mama ba da sam basa kaunarshi... Yanzu ki duba Aunty A'i Mama yau tace murna take an sake ni.. Harda fad'in g'wara da bamu samu rabo ba... Kuka ne yaci k'arfinta,tuni ta hau yi ba kakkautawa. Taso wa Aunty A'in tayi zuwa kusa da ita ta hau lallashi,chan ta numfasa itama harda hawaye ta fara fad'in "Kinyi wauta Salma matuka,samun irin Ja'afar a yanzu wallahi sai kin tona,irin halin da kika dinga karta mishi duk na samu gun Abba,kinsan nima ba wai Mama nayi dani bane sosai,dan ban fiya shiga irin shirgin nan ba. "A gantali har gida sukutum ki ka kona mishi Salma.. Naji ance ya kuma shiga cikin y'an _missed call_..Bana tunanin har yau ya gama tattare takaddun da ya rasa kuma duk a dalilinki fa,amma dai dai da rana daya bai ta6a hanaki ci koh sha ba?.. Duk da baki san ta ina yake samu ba. "Maimakon ki zama mace ta gari mai k'wantar mishi da hankali har ya manta bakin cikin da yake ciki na rasa aikinshi,a'a sai ma kara hura mishi wutar masifa ki ke a gida. "Salma kina da ilimi fa,kinsan d'ukkan hukunci a game da matar da take sa6a umarnin mijinta, bare ke da kusan kullum cikin shi kike?.. Ina ki ka bar islamiyar taki Salma?.. Da har kika bari rudin su Ummi da chan wasu jahilan makotan suke hure miki k'unne,wanda in zaki titsiye su ba mai iya rashin mutuncin da ki ke Salma.. "Nayi imani zaman cikin gidan ki ya fiye miki alkairi sama da zaga makota yawan gulma da ki ke.. "Ya sanar ni shi sai a shafe wata nawa,baiga makotan naki na zirya gidan ki ba sai dai aiken bani taliya bani mai, shin sun fiki sanin ciwan kansu ne Salma? "K'wanaki haka har gida na samu yana fad'a kina fad'a, amma dana shiga nai miki fad'a, sai kika nunan wai maza sai da wuta.. "Kan kiyi aure Salma ni nayi da shekara hudu, ba zaki fad'an halin maza ba,amma a lokacin na biki da murmushi ne kawai. "Ki dube ni nan Salma... Dago tai ido
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41