Chapter 37
Chapter 37
fa kallo tana mika maka ka d'auke kai,ta ajiye ya fad'o kasa,toh meye lefinta aciki har irin wannan zagi?.. A'a toh gaskiya... Kai ta kawar ranta 6ace. Cika Miemien yayi yana kallonta, wannan ne karo na farko da ya fara ganin fitsarar Salma,shi zatai wa tsawa akan Miemie? By Feenat Ja'afar. 9/29/16, 9:37 AM - Queen Safiyyert馃憫: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 41_Da gudu ta karasa tana kama hannun Salman,d'aukarta tayi a ta sa6a a baya, "Yi shiru kinji.. Muje daki... "Kar ki kuskura ki shigar min d'aki da wannan yarinyar.. Chak taja ta tsaya tare da juyowa tana kallonshi. "Kema kar ki shigar min d'aki,ni zakiyi wa rashin mutunci kan y'arki?.. Toh baki isa ba,dan ba ayi macen da ta isa daga min murya ba ki sani. Cikin karfin hali tace "Toh mey ka ke nufi da hakan?.. Daga fad'in gaskiya?.. Haba Alhaji,Kullum ina fuskantar yadda ka ke tsagwamar yarinyar nan,shi yasa sam bata shiri da kai ai... "Ba wani nan,bakin halin yarki dai irin na tsohon mijinki dai,da kuma shegen taurin kanta irin nashi,koh kin zata na manta da waye shi zamanin neman aurenki? Da sauri ta tare mai numfashi harda sauke Miemie kasa da sauri, "Ba ruwan Ja'afar cikin maganar nan tamu,zai fi kyau in ka daina sakoshi ciki..kuma na fad'a maka y'ata bata da wani mugun hali,sai dai naka mugun halin rashin son yara, da kuma.. Shiru tai tare da ja da baya ganin ya zaburo kanta, "wallahi kar ma ka soma,dan ba yadda za ai in zuba ido kullum kana aibanta min yarinya wallahi, nawa Miemie take? Amma k'arfi da yaji so ake ta iya dan hali.. "Salma ni nake fad'a kina fad'a?.. Ashe baki da mutunci?.. Kai ta kad'a tare da juyar da kai, "Nikwa nake da mutunci tunda a cikin gidan ubana ka auro ni kuma... "Subhanallah,haba ku k'wa.. Juyawa tayi taga Maman su Nabila na shigowa dakin. "Tun ina shanya nake jiyo ihun Miemie da naku,bai dace ba Allah,kuna abu a gaban yarinya.. "Ba ruwanki cikin zancen nan,in ba so ki ke ya taso da kwantaccen naki ba ke ma.. Shiru taja bakinta tayi tuni idonta ya fara zubar da kwalla, ya cigaba "Yara nawa ma basa gabana bare ta wani, saboda haka akan yaro ba mai sani ciwan hawan jini,dole yau ki mayarta gun ubanta,koh ki san nayi da ita. Cikin kuka tace "Bazan iya rabuwa da y'ata ba,kai hakuri raina ne ya 6aci.. Malalacin murmushi yayi,kan yace "Daga baya kenan,amma dole ki za6a zaman dani koh da yarinyar ki... Maman Ja'afar ta kallo da itama ke hawaye tana kallonta,sai ta cije le6e da takaici. Juyawa tayi ta d'au Miemie, kan ta kalloshi ido na fidda kwalla. "Ni kam na kasance daga masu taya annabinmu kishin Al'ummar shi,dan haka ina son haihuwa,bi ma'ana zan iya rayuwa da Miemie kad'ai mud'in Annabin mu zai alfahari dani... Cikin zafin rai yace "Kimin hausar da zan gane Malama ni.. "Annabinmu yace kuyi aure dan ku hayaiyafa,domin go6e kiyama nai alfahari daku.. Kayi aure,amma baka fatan tara zuri'a, hakan yana nufin kana tarjiya a bisa umarnin manzon Allah.. A tunzure yai yo kanta, "Kimin shiru fitsararriyar kawai,koh yayarki bata isa ja ina ja ba wallahi, dole ne yau ki za6i d'aya.. Cigaba tai da batun ta ido rufe, "Nai ma biyayya ta t'sawan shekara guda ina bin yadda kaso,toh ka sani ni Sunnah na dauki aurena,kuma zan cikashi ne ta hanyar tara zuri'a, dan zanyi alfarhari idan na kasance a daya daga wanda Annabi zai alfari da ita... Mari ya de6eta dashi jiki na 6ari,da sauri ta dafe gun tare da bud'e ido,kuka Miemie tasa ganin an daki Auntyn ta, "Mutuniyar banza kawai,ni zaki mayar jahili?.. Murmushi tayi kan ta kad'a kai. "A'a,dan kuwa kafi jahili,danshi dama bai sani ba bare take,kai kuwa ka sani amma kana taya shedan rawa,dan baka kaunar.. Shiru tayi ganin zai kara mata wani,da sauri ta rintse ido tana hawaye,jin shiru bataji saukar mari ba yasa ta bud'e ido. Hannunshi rike a hannun Maman su Ja'afar, "Lalle lokaci yayi da ya kamata in tanka maka Alhaji,lokaci yayi da zan daina bin umarnin ka ina 6ata.. Ashe har alfahari ka ke cewar yaranka ma basa gabanka?.. Jiran amsa take tana kallonshi, da borin kunya yace "Cika min hannu... Ba musu ta cika, Salma ya nuno "Ke kuma ki tafi gidan ku,na sake ki saki daya,na koyan hankali,in kin koyo kofa a bud'e take ki dawo.. Ido ta rintse gabanta na fad'uwa, wai ya saketa?.. Daga fad'in gaskiya. Kan Maman su Ja'afar ya dawo, "Wato zuwan fitsararriyar yarinyar nan ta sa kin fara sauya hali Halima koh.. Kai ta daga da sauri.. "Kwarai kwa,dan yanzu na gane kuskuren dana tafka a zaman baya da nayi da kai, nima ina son zuri'a, ina son su Ja'afar sama da komai yanzu,kuma zanso wanda duk yake son su,zan kuma yi fad'a da duk mai kinsu, aciki kuwa harda kai usman... Baki ya saka yana mata k'allon mamaki "Usman?.. Babbar magana.. Halima yau ke kike kama sunana ba ma Abban Ja'afar bare Alhaji?.. Shiru tayi tana kallonshi,sai sababi yake daga karshe itama yace taje sai ya nemeta. T'saki sukai mai lokaci daya ita da Salma,duk da kallo ya bisu Salma tai d'aki. "Ai nima ka sallame ni kawai,dan bazan zauna da mutumin dake kyankyamin zuri'a ba,dole yau na barka,Allah ya yafen baya,amma yanzu kam ta kau,ka sake ni nima kawai... "Bazan saki ba,amma dole ki fuce min a gida,dan ba mai sa min hawan jini... Kuka Salman take tana jiyo sababin da Alhajin ke yi.. Hannu Miemie ta kai tana girgiza mata kai itama tana kukan,gaba daya ta rungumo y'arta tana kuka mai cin rai,ita kuma haka Allah yayi ta marar sa'a a zaman aure,gashi yau a dalilinta auren shekara sama da ashirin na neman tsinkewa bayan ta t'sinke nata. By Feenat Ja'afar. 9/29/16, 9:39 AM - Queen Safiyyert馃憫: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 42_Jugum Abba yai bayan jin bayanin Aunty A'i,ita dai Salma sai kuka take,dan tasan yau kam sai ta Allah,fad'a kam sai dai ta toshe kunnenta. Amma da mamakinta sai ji tai ya sauke ajiyar zuciya tare da fadin "Allah ya kyauta toh,dama tun farko ni mutumin nan ba wai ya mun ba ne. "Yadda naga kowa na yinshi a gidan musamman Babar taku yasa nabi yarima nasha kid'a, sai fatan Allah yasa haka shi yafi alkairi.. Mama ce ta riga kowa saurin fad'in "Amin,ni nasan naso shi,amma daga baya sam mutumin ya fice min akai,dan daga gani ba wai zaiyi wani mutunci bane,ga dankaran kulle,yanzu kuma an kara da rashin son haihuwa.. Dame yarinya zata ji?.. Kallon mamaki suke ma Maman musamman Salma, yau mama ke fad'in aibun Alhaji da bakinta?... Lalle abu ya 6aci. Da dare suna kwance ta tasa Miemie a gaba tana kallo,itama ido ta sa mata, tunaninta zancenta ya tabbata. A dalilin Miemie aure ya 6alle.. Murmushi tai kan ta gyara kwanciya. "Miemie.. Kai ta daga tare da fad'in "Uhmm.. Sai ta mirgino kusanta tai rub da ciki "Kina murna kuwa?.. Baki ta yage mata ba dan ta fahimci nufin Auntyn ba. Sai ta kad'a kai,ta rasa wane irin nishad'i ke shigarta da yamman nan zuwa daren yanzu.. "A k'ya kam yi murna,wato kin rabu da
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41