Chapter 35
Chapter 35
Ilham. "Kai Billy banda fa sharri.. Dariya tai tana "ba wani sharri, koh dai mun karu?.. Miemie tayi k'ani? Shiru tayi tana murmushin iya le6e. Bayan sun gaisa take ce mata ai daga wajen Miemie suke,tai ta kukan zata zo tana jin tace gun Auntyn ta zata. Murmushi tai tai kasa da kai,Allah sarki Mimi. "Yau Miemie aka kaima ziyara kenan?.. Murmushi Billy tai kan tace "ai duk sati sau biyu Abban Ahmad (Garba) ke zuwa dan dubo ma Abban Miemie lafiyarta. "Shine yau muka je tare,Miemie akwai wayo,kusan wata shida amma bata manta Abbanta ba,tana jin muryarshi a waya ta fara murna.. Shiru tai tana nazari,ba dai ace tun tafiyar Ja'afar ya zuciya ya bar garin nan ba?.. "Ja'afar kanar wasa,kinga wata shida muke nema yaki waiwayo mu,sai kulafucin a dubo mishi gudan jininshi... "Rayuwa kenan fa,kana naka Allah na nashi,in kai hakuri sai ka ga na Allahn ne dai dai a gare ka. "Amma Abban Miemie namijin duniya ne,mai ra'ayin kanshi,tunda ya jima haka nasan alhinin aurenki ne bai sake shi ba. Shiru tai tana jinta,a hankali ta fara jin nadamar wulakancin data kartawa Ja'afar, Abban y'arta. Yau Billy ta kawo fitina,dan har ta tafi bata da sukuni,har sai da ta tiki kuka son ranta taji dad'i,yanzu burinta Miemien ta dawo gare ta. Koh da maigidan yazo yaga yanayinta yasan tasha kuka,da ya tambaye ta sai tace Miemie take son gani ta d'akko ta. Anan ya tada mata bori,har sai da tai da na sanin maganar Miemie. Ba abinda yafi kona mata rai sama da yadda tanaji tana gani yai mata haramiyar makaranta,sannan Mama ta goya mishi baya,abu goma da ashirin sun had'e mata. Adaddafe akai shekara, lokacin tuni ta jima da d'akko y'arta,dan bazata iya da rashinta ba a irin yanayin da take na son yaran nan. Sai sai wani abu,fur Miemie taki jinin Alhaji, ko abu take in zai kwan dubu yana ta bari bazata koh k'alleshi ba,asalima har wani kumbura baki take in ta ganshi,Salma tai magana tasa mata kuka,ga bala'in Alhaji na wai yarinya tun kan ta girma ta rainashi shi da gidanshi, har harara wai take mishi... A tunaninta kamar Miemie wane harara ta sani bare wai kumbura mishi baki?.. Amma dan a zauna lafiya yasa kullum take kwa6ar ta. A gaban kowa har su Nabila zatai wasa harda k'yak'yatawa, amma fa koh a nan bangaren taci ka'ro da Alhaji zata d'unkume,tamkar ba ita ba,shima kwa da harara zai bita, wani sa'in harda t'saki.. By Feenat Ja'afar. 9/29/16, 9:33 AM - Queen Safiyyert馃憫: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 39_"Aunty A'i na rasa yadda zanyi ne,yadda yake nuna t'sanar Miemie karara yafi damuna,abu kadan tayi sai ya hantara,t'sawa, ga kullum yai ta surutun wai tana hararar shi,koh fa wai turo mishi baki,nawa take fisabilillahi?... "Allah bansan haka agolanci yake sai gun Miemie. Murmushi tayi "bari muga,ke dai sa ido... ta kallo Miemie dake chan gefe tana mota da motar wasa. Da k'arfi Aunty A'in tace "ke Miemie... Rai had'e, itama ta dago tare da 6ata rai tana kumbura ma Aunty A'in baki. Sai Aunty A'in tai mata murmushi tare da mika mata hannu, "zo Miemie naga kitso, waya miki?.. Kafad'a ta make halamar bazata zo ba kenan. Cikin wasa Aunty A'in tace "haba Miemie ta,zo zan baki sweet fa.. Da sauri ta taso har tana dariya ta d'are ta tana kiran sweet. Baki sake Salma take k'allonta,Allah yaga banda yau ta gani da idonta bazata yarda Miemie zatai haka ba. Gira ta daga ma Salman halamar ta gani ai. Miemien na fita tace "Ikon Allah Aunty A'i, ashe dai gaske ne Miemie na mishi hakan. Kai ta kad'a, ''amma in ya mata irin yadda na mata,kila koh wasa take yana mata ne,yaro kamar Miemie dan lallabi ne,shi yasa tun farko banso kin karbi yarinyar nan ba Salma,gudun irin matsalar nan.. Ba magiyar da Abbanta bai min ba shima a waya kan baison ya'rshi ta zama agola, Gashi in bakiyi wasa ba shi kenan ta gama raina miki miji. Cike da damuwa tace "Nikam ta rufan asiri karta kashen aure Allah.. Dariya Aunty A'i tayi,lalle ma Salma,wai karta kashe mata aure? "Haba dai ke kuma,sai kace wata babba,kawai dai ita tata salon fad'an ne haka,amma zata daina. Ajiyar zuciya ta sau,kan tace "Bazaki gane ba Aunty A'i,wallahi in Abban su Nabila zai kwana yana cewa Miemie bari koh kallonshi bata yi,wannan nasan tana dashi,shi kuma sai ya kule,baya duba yarintarta,sai ma ki ga ya hauni da sababi. "Toh ki dinga sata misali kai mishi abu haka,kina kuma kula d yanayinta in yana mata magana,sai kina sata a hanya. Har magriba suna abu daya,matsalar gida Alhaji har ta tafi. Washegari a ita ke da shi,tun wuri ta shirya Miemie ta d'auke duk kayan 6arna duk dan a zauna lafiya. Chankula chankoto take mata tana dariya,ta sunkuya tana mata "aci ladan gabe" tana dan mata duka yai sallama. Kallo daya ya musu ya d'auke kai, dagowa Miemie tayi,in ba idonta ke mata gezau ba kamar harara ma ta mishi,tuni ta gintse fuska ta daina dariya. Ya salam, Miemie tai nisa a tsanar Abban su Nabila. Yake tai kan ta tashi dan binshi d'aki, "Miemie tashi muje gun Abba koh?... Kafad'a ta mak'e tana turo baki, sai tai kamar bata gani ba ta kinkime ta,a ranta tana fad'in "sai nayi da gaske a kanki Miemie. Ihu ta fara tana zazzamewa,a dole ita bazata je ba,jin suna iyowa dakin yasa da sauri yace "Kar ki shigo min kina min wannan kukan dama.. Chak ta tsaya tare sauke ta,kafadar ta kara makewa tana kallon Salman,sai ma ta fita tayi bangaren su Ja'afar. Kai ta dafe tana mai mamaki ita kam,Miemie,toh mey take so da ita?. *DAN KUKA...* ************************** Dube yake zai k'alli news amma baiga d'ayan remote ba, ga Salman ta shiga wanka, Kamar ance diba hannun Miemie dake chan gefen corridor tana wasa sai ga shi kuwa,yau shine motar ta ma. Da zafin nama ya tashi ya nufi gunta.. "Jiyinnnn" take dashi cikin tsawa yace "Wannan ne abin yin motar?.. Dagowa tai tana t'sareshi da ido cikin had'e rai, "Bani nan ni labarai zai wuce ni sarauniyar 6arna. Kafad'a ta mak'e mishi tare da yi da remote din bayanta tana zunguro mishi da baki. Cikin zafin nama ya dagota, dai-dai fitowar Salma dan jin fad'anshi, binta yake daga zaunen tana matsawa taki bashi,kawai sai ya fizgota da niyar kwata ta tun karfi, kai cikin fushi ta kwada remote din a kasa tana kuma mishi ihun kukan ya hanata wasa.. Dagashi har Salman suka bi remote din da kallo wanda kowanne part yai nashi gun battery ya cire. Da sauri Salman ta karaso ta kwada mata mari,sauke ta yai kasa yana sababin ai wai ita tasa ta raina mutane yai waje,k'allon da baiyi ba kenan ya fice. Harara ta kwada mata kan ta kamo kunnenta ta murde tana kuka, "Baki isa ki chazan matsala ba ja'irar nan,wato bakin hali ki ke son kowa koh?. Kashen aure zakiyi ne?.. Kullum baza'a aji kanmu da mijina ba sai akanki?.. Cikata tai tare da dan rangwashenta, "Toh baki isa ba,dole kizo ki koma gurin Mama koh dangin Abbanki da zama... Bata karasa ba Miemie ta fad'i tana burburwar fad'in taki,ita bazata ba.
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41