Chapter 2
Chapter 2
ta kara sa ma sauran Burin da yafi na Aunty A'in.. Barin Salma dake doguwa ce cikin su. Ita kam Salma bata san ma ana yi ba. Kasantuwar shagonsu Baba ya zama biyu sai ya zamana aiki yai musu yawa, har bai samun damar dawo wa gida cin abinci sai d'ai Ummi koh Salma su kai mishi. Ranar kaiwar Salma ne,tai shirin Islamiya ta doshi shagon su Baba. Tunda ta ajiye abinci taki gaba taki baya,kamar dai da alamun an mata abu daga gida. Murmushi Baban yai kan yace tazo.. _"mey aka miki uwata?_ Hawaye ta dan matso halamar 6aci. _"Mama ce ta hana ni kud'in tara_. Kai Abban ya k'ada yana murmushi kan ya sa hannu a aljihu ba chanji,gudar naira dari ya fitar kan ya nuna mata shagon kusa dasu taje tai chanji. Da sallamarta ta shiga,ta gaida shi,shago ne na kayan k'yallin mata na sawa, attamfofi da laces,ga materials kala kala,d'uk zuwanta bata ta6a shiga shagon ba sai yau. _"Salamatu y'an mata,ina su Ummi?_ Murmushi tai mishi,dan tana ganin shi gun su Baba, dattijon na da kirki da fara'a, banda yaron shagon shi da koh k'allo bai mata ba, _"suna gida,Baba ne yace aban chanji_. Kai ya k'ada, kan ya k'allo na zaune a acikin shagon rike da littafi halamar yana dubawa. _"amm *Ja'afar*_.. Kai ya dago karon farko, _"Na'am Abba_,, sai lokacin ya kula da Salma, _"Ba wa Salma naira ashirin ta tafi kar tai latti_. Kai ya k'ada kan ya kara k'allo Salman wacce sai hange take koh za taga wani dan islamiyar su tana mika hannu. _"k'ar6i man_.. Juyo wa tai taga yana miko mata kud'i fuska ba fara'a, da sauri ta k'ar6a tana tafiya tana fad'in _"na gode Abba_. Da k'allo Ja'afar ya bita,yana ganin Ummi ce mai rawar kai ashe sauran ma haka suke. _customers_ ne suka tada shi ya shiga shagon. Washegari ma sai ga Salma,wannan karan koh shagon su Baba bata je ba tai shagon su Ja'afar. Da mutane da kusan d'uk y'an mata ne suna siyayya, yana ganin Salma ya had'e rai, sam yaki jinin a 6ata yaro da kud'i, ita kam Salma harda mishi murmushi tana dago mishi hannu da kamar abu aciki. T'saki yai,kan ya cigaba da abinda ya ke,sai da ya sallami kowa kan ya ganta tana gaida Abban shi da ya fita yana nuna mata cikin shagon. Da dan gudinta ta shigo,a tunanin shi kud'i Abban yace ta kara k'ar6a gun shi,dan da zumudinta ta gaida shi. _"dama Abba ne yace in_..... Cikin fad'a-fad'a ya katseta, _"bani da chanji nima yau,jiya an baki kinji dad'i shin_.... Shiru yai sakamakon idonta da yaga ya cika da k'walla tana k'allonshi. D'uk kuma sai jikinshi yai sanyi.. A hankali ta ajiye masa gudar naira ashirin akan benci ta juya tana goge hawaye. Ba dai kud'in shi ta biya shi ba dan ya mata fad'a? Da sauri ya d'auka da niyar k'wada mata kira ya mayar mata sai dai tuni tai nisa sosai. D'uk kuma sai yaji bai k'yauta ba. Yana nan zaune har Abba ya dawo, _"kaga Salamatu wai kud'in ka na jiya ya hau shine ta dawo ma dashi ba"_.. K'allon Abban yai da sauri, _"Abba kud'i kuma?_ K'allonshi yai kan ya k'ada mishi kai, _"sai da nace ta tafi wai A'a tana da wani,Salma ak'wai hankali, ashe batai ma magana ba?_ Shi dai Ja'afar yai shiru yana jin Abba,sai ya kara jin wani iri. *By* *Feenat Ja'afar*. 9/29/16, 8:50 AM - Queen Safiyyert馃憫: *A BAK'IN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. *5*- Washegari sai zuba ido yake yaga Salma shiru,dan d'uk jiya ji yake bai k'yauta mata ba. Sai d'ai Salma har k'wana biyu shiru ba koh kalar ta sai Ummi ke zuwa kawo abinci. Ranar Ummi ta kawo zata tafi ya t'sayar ta da tambayar ina Salma k'wana biyu? "tana gida Yace "ya bata kawo abinci sai ke?.. Tana zungura baki tace "sai gobe ne nata kawowar. Dan koh ita Ummi Ja'afar ke hanata zuwa gun Abba mai k'yautar naira biyar goma.. Sam baida fuska,shi yasa taki jinin shi. Washegari kuwa tun da ya ga lokacin kawo abinci yayi yake k'allon shagon su Baba,yau ga k'ananan shi a shagon baida mat'sala. Kamar ance ya dago,sai gata kuwa sanye da kayan islamiya,sai dai duk tai kicin kicin fuska ba walwala. Yana k'allon yadda ta t'suguna ta gaida su Abba kamar kullum, tana da nut'suwa ba kamar Ummi uwar bankaura ba. Tashi yai kamar mai tafiya wani gun,dai dai k'wanar da take bi gida ya t'saya,sai gata kuwa,har zata wuce ya kira ta,suna had'a ido ta had'e rai,sai ta bashi ma dariya. Hannu yasa ya ciro naira ashirin d'in ya mika mata yana murmushi, a dan sace ta k'allo shi kan ta kawar da kai tare da girgiza mishi kai. *"Salma*..K'all onshi ta kara,ganin yana murmushi sai abin ya bata mamaki,bata t'sinke da lamarin ba sai ji tai yace tai hakuri, kai ta kawar kawai, kin huce? tana wasa da hijab d'inta ta daga mishi kai, "toh ki k'ar6a in kin huce,na bar miki.. Kai ta kara girgiza mishi,kan tace "A'a ka barshi fa.. "baki hakura ba kenan Salma?.. Kai ta k'ada mishi, yace "toh ki k'alle ni ki amsa maza kar kiyi latti kinji K'anwata.. Da lallami yasa ta sakko harda dariya,har kusan makaranta ya rakata ya dawo,yana mai mamakin fara'ar shi yau ga yarinya Salma,sam shi baida sakin fuska musamman ga mace d'uk k'ank'antar ta k'wa. Tun daga ranar ya zamo in Salma ta kawo abinci sai Ja'afar ya rakata ya kuma bata ashirin d'uk bayan k'wana biyunta. Sosai sun saba,har in batazo ba baya jin dad'i, har su Abba suka kula da sabon kawancan Ja'afar da Salma,ana haka Baba yasa ya dinga ma wa su Salma _lesson_ tare da kannenshi tunda ya gama _secondary_ _admission_ yake jira. Koh a gun _lesson_ misalin Ja'afar a Salma yake t'sayawa, in k'wa duka ne koh t'sawa Salma bata ciki,sai dai yai ma k'annenshi, hakan yasa tun tana karama yaran suke ce mata Salma budurwar Ya Ja'afar. A lokacin takanyi bori kan bata so,har takai da ta kai kara gunshi,sai dai mamakinta dariya ma yai mata,yau da gobe har Salma ta saba da tsokanar k'annen Ja'afar . Karatu ake sosai za ai _coming interest_, sai dai ba Ja'afar dan ya tafi Zaria sakamakon _admission nashi da ya fito. Sosai Salma tai k'ewar shi,har hakan yasa ta d'aina kai abinci shago sai almajiri,a hankali har k'ewar ta sake ta suka gama jarabawa sai zaman jiran sakamako... Sai dai Ya Jaafar na chan k'wance kasan zuciyar ta. Yau ga Salma a _boarding_ babban burunta kenan makarntar k'wana. ************************** Lokaci ya shud'e, kamar wasa yau ga nan Salma an zana _J.S.C.E_, hutun mai dan nisa ne na yau. Mai nut'suwa ce a d'uk y'an gidan su,a layin su,dama unguwar gaba d'aya, Salma abar k'watance ce,musamman rashin yawanta,kullum kaje in tana hutu toh za ka samu Salma a gida. Batta k'warafniya irin ta y'an mata masu tashen tashi,asalima fitar ta in tai yawa toh islamiya ce ta yamma, sa6anin su Ummi da tuni tun kar ta far ta kone, dan wanka iya wanka Ummi ta iya,hakan yasa Mama ta kara d'aure mata gun siyan kayan k'arya. Dan a ganinta ta gama da kason Aunty
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41