Chapter 40
Chapter 40
ya zama serious haka, hakan yasa ta bashi hankalinta gaba daya. "Nasan nima har yanzu kina ganin baki na sakamakon zuwanmu na karshe gunki. Rantsuwa ya mata,kan yace "Ja'afar baizo ranar gunki da neman auren kisa wuta ba sam,asalima yazo ne danya sadaukar miki da farin cikinshi gare ki sakamakon sanin waye Alhaji Usman.. Kai ta dago tana kallonshi. Sai ya kad'a mata kai, Ja'afar din ta kalla,shima itan yake kallo. Yacigaba, "yana son ki samu farin ciki ne Salma,wanda yasan a gidan Alhaji dak'yar ki sameshi,dan kaf halin Alhaji ba wanda ba'a karanto mana ba,hakan yasa ya gwammaci ya baki ni,duk nai imani sai ya fi mishi ciwo sama da auranki a waje.. Ya kallo Ja'afar da murmushi, "nasan abuna. Murmushi sukai ma juna,tabbas hakane,dan da Garba ya auri Salma,da yana gani bashi ba sake ganinshi bare hulda da gidanshi. "Dan haka banajin da wanda ya kai Ja'afar son farin cikin ki,ki d'aure ki bawa abokina second chance a zamanku kamar yadda bukaci haka. Nan yai ta musu fad'an rayuwa sai y'ar hakuri ce,da sanya tsoron Allah a lamari,gashi sunji dad'in tawakallin tunda suna fatan in Allah yaso su maida aurensu. Kan Garba ya tafi sai da ya tabbatar kowa ya yafe. Zaure suka koma ta sa musu taburma. Kallonta yake suna ma juna murmishin so cikin kauna. Sai wani dan sinke kai take halamar kunya. Hatta Miemie ta gane iyayen sun dinke, sai kallonsu take tana murmushi. "Assalam Alaikum.. Kai suka dago,Ja'afar ya amsa. "Aunty Salma wai ana kiranki a waje.. Kallon Ja'afar d'in tayi, Shima ita yake kallo,sai yai mata murmushi. "Tashi muje naga wane tsageren ne wannan... Miemie ya d'auka itama ta tashi tana murmushi suka fita. Alhaji ne yasha gayu da babar riga da wata katuwar mota yana murmushin ganinta. Fuska ya tsuke ganin fitowar Miemie da Abbanta suna wasan su. Tana ganin Alhaji Miemie ta g'imtse fuska,murmushi Ja'afar ya mata tare da shafo fuskarta suka karasa. Hannu ya bashi dan su gaisa Alhaji ya juyar da fuska gefe. "Gunki nazo fa. Kallonshi tayi tana murmushi, "toh Alhaji,gamu ai.. Da halamar tambaya ya k'alleta. "Ban gane ga ku ba?.. Kina nufin dashi zan ganki?.. Ja'afar d'in ta kallo tare da Miemie dake kallon Alhajin duk rai had'e daga shi har y'ar. Murmushi tayi tare da matsawa kusansu suka jeru mishi a gaba. "Alhaji, kai hakuri, kai hakuri,ka daina zuwa,InshaAllah aurenmu zamu mayar da Abban Miemie.. Ka d'auka zaman mu yazo karsh.. ka d'auka rabuwar aure na da kai da auran duk had'i ne na Allah... Ja'afar ta kalla tai mai murmushi tare da shafo fuskar Miemie. "Kai hakuri na na zauna da iyalina, ka yarda sune farin cikina, ni ce tasu,kai hakuri pls... Kai ya kad'a,tare da kallonsu,duk daga gani suna a farin ciki.. Tabbas yasan yai sake,gashi ya tashi a tutar babu,ba Halima ba Salma,ba su Nabila ba Miemie... Wa zai gane a jiya yayi nadama?.. Ya zasu gane yasan dad'in jin motsin D'a kusanshi a yanzu?.. Wa zai gane ya hakura yanzu kam yana son zuri'a?.. Murmushi yayi yana d'auke kai,kila haduwarshi da Salma sanadin shiryuwarshi ne,koh yanzu ya gode Allah. Kai ya kad'a tare da masu fatan alkairi, k'warai tai mamakin jin harda mata godiya a bisa gaskiya da take tsage mata. Hannu ya mikawa Miemie fuska d'auke da murmushi. Kafad'a ta mak'e tare da lafewa a kafad'ar Abbanta. Mota ya shiga tare da fitowa da leda cike da shopping na chocolate da ice cream.. Alawa daya ya fito dashi tare da fad'in "Zan baki sweet fa,zo mu gaisa mana Miemie.. Salma ta kalla kamar mai jiran umarninta. Murmushi tai mata tare da daga mata kai,abin kai sai taje ba musu,yau sai ga Miemie harda ma Alhaji dariya. Da zai tafi hannu ta daga mishi tana mishi bye-bye tana dariya. Duk sai Alhajin ya bata tausayi Alhajin,har Ja'afar na daga mata gira halamar tambaya. Marairaicewa tayi tare da shagwa6e fuska. "Y'arka ta rabani da Alhajina shikenan kunji dad'i.. Harara ya sakar mata kamin yace "toh bishi, Allah yai ma y'ata albarka yarinya mai kishin Abbanta koh? Kai ta daga mishi tana dariya,da murna ya shillata sama ya chafe suna dariya. Gwalo yai ma Salman,sai Miemie ma ta hau mata,tuni ta fara chunno musu baki suna cikin shagwa6a. By Feenat Ja'afar. Like 路 2 路 Reply 路 Report 路 Aug 11 Feenat Ja'afar Novel's *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 46_Ba sauran jira,dan karara suke nuna ma fitsara a gidan Mama, su Ja'afar abin nema ya samu,ba guntun fulako,ba shiri ta bama Abba shawarar ayi a mayar da auren nan. Wata daya aka sa suka sha biki kamar ba gobe.. Nan take jin labarin auren Bintu a gidan mai mata uku,tana chan ta zama bora. Su Maman Abba duk sun halarci bikin nata,nan take tsurkuta mata labarin Maman Ummi kan ranar ta fita gantali miji ya dawo,bayan ta dawo yace ta nemi inda dare ya mata,karshe dai akai saki. Murmushi tayi,tasan Allah ba azzalumin sarki bane,dole yadda taga tasku Maman Ummi tagani itama. Jingina yayi a jikin bango yana kare mata kallo,fuska rufe ruf da g'yale,murmushi yayi dan tunawa da daren farkonsu a wanchan gidan. Karasawa yayi tare da g'yaran murya kad'an yana leka fuskarta. Zama yayi tare da sauke ajiyar zuciya. A hankali ya kai hannunshi tare da daga mayafin da ta rufe fuskar. Tsam yayi yana kallonta ido cikin ido,tuni ya marairaice mata fuska,kuka fa?.. Hannu yasa yana share mata wani na zubowa,duka ya hayo gadon tare da janyota yana shafo bayanta halamun tai shiru. Sai da tai shiru kan ya dago kanta. Ido suka zuba ma juna ba koh kiftawa. Chan ya nisa cikin murya kamar mai jin bacci yace "Kin tuna kalaman da na ta6a turo miki na karshe cikin text message dina kuwa?.. Tunowa ta fara,sai yai murmushi tare da zamewa kan katifa da ita a kafad'arshi. Ajiyar zuciya suka sauke tare da kamo y'atsunta. "Na ce miki _" a heart dat truly loves never loses hope..but always believes in d promise of love,no matter how long d time and how far d distance,at d right time,love will fine a way".._ "Hope kin yarda da maganar ba wai soki burutsu Masoyinki bane?. Kai ta daga mishi halamar ta yadda,tunda ga nan K'ADDARAR wani zama ya kara had'a su waje daya. Yau kam ya gama gasa mata jiki da d'anyun kalaman da ya tanadesu kawai da Salmanshi,fatanshi Allah ya kare sa6ani a tsakani. Washegari da t'sant'sar farin ciki suka tashi,suna kitchen had'a break fast sai nannan yake da ita. Tashin Miemie suka ji tana kiran Aunty cikin kuka taga sabon waje. Ganin iyayen waje daya ita kanta sai binsu take da kallo, mot'si kad'an ta kallesu,kamar wacce bata so su rabu da juna suyi rayuwarsu tare. ********** Yau ziyara aka fito ta sallah ita dasu Ummi, Sun zaga duk inda ta tambaya saura gida 1 taga sun karkata zasu shiga gidan kawunsu wanda jiya sunje. Ja tai ta tsaya tare da ce musu su shiga su fito dan yau bata tambayi nan ba. Murmushi Aunty A'i tai tare da kad'a kai,a lalle kullum Salma hankali na kara zuwar mata. Tuni Ummi kam tai gaba tana t'saki. Tana nan tsaye kawunsu ya fito a gidan,bayan sun gaisa yace mata ya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41