Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 39

Chapter 39

A Bakin Aurenki Book 1 Complete Hausa Novel – Salma’s Painful Return 1,256 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

t'sare kai da tsare gida. Rayuwarshi ta sauya,dan ya dawo ainashin halaiyar shi ta da,koma yafi da din, Ja'afar kenan,namijin duniya. Dago kai yayi yana duba yanayin garin da yadda kowanne shago suke hadahadarsu,sai ya sauke kai kan Abdull mai tahowa dauke da baby a kafad'a tana ta washe baki tun kan ta karaso. Tuni fara'a ta maye g'urbin rashin walwalar shi,kashe wayar yayi tare da ajiye ta gefe dan tarar gudan jininshi,duk Abba dake gefe kad'an yana kallo. "Abbaaa... Miemien ta fad'a lokacin da yake k'ar6ar ta,murmushi yayi mata tare da shafo fuskarta "Na'am Miemien Abba.. Sai ta washe baki. Ciro changi ya mika ma Abdull, "Kan magriba kazo ka maidata kaji?... Kai ya kad'a tare da amsa yayi godiya. Zama yayi tare da d'aura ta cinyarshi, Tasha kwalliya da rigar da ya yo mata tsaraba cotton ja da pink,kan nan kamar an mata shampoo sai kyalli yake yasha ribbons.. Hannu yakai kan dan beauty point nata ya latsa sai ta sa mishi dariya. A hankali shima yayi har hakorinshi suka baiyana. Tashi yayi zuwa gun Abba dan mishi sallama,kai ya kad'a Miemie na mishi bye-bye tana dariya. Kamar kullum nai yai ta yawo da ita suka sai ice cream suka nufi gidan Garba nan suka yada zangon su. Miemien Garban ya kallo yadda take tsalle kan Abban nata shikam sai murmushi yake mata. "Abokina ina so yau dai daya ka saurare batu na,sama da wata hud'u dana fara ma magana zaka ce a'a kai baka so.. Kallonshi yake jin inda yake neman dosa,tuni ya fara sauya kama. Ba tare da yabi ta kanshi ba Garban yaci gaba "Salma fa au... Cikin t'sananin fushi ya rufe ido tare da daga mishi hannu. "Dan Allah ka d'aina dawo min da hannun agogo baya,ina a cikin farina yanzu,banson jin sunan wata Salma chan.. Gefe yayi da kai yana chunkune fuska,kai Garban ya kad'a kan yai y'ar dariya, "Karyar banza kenan,yanzu da zance Salma tana gida an sakota da nasan ba wanda zai farin ciki a yau,kaine fa.. Baki sake yake kallonshi, "kana sanin abinda zaka fad'a man malam.. Matar mutanace fa yanzun. Murmushi yayi yana mishi k'allon bakasan komai. "Toh auren Salma ya rabu tun wata hud'u da ya wuce,sai ka kurbi ruwan sanyi ka huce.. Baki sake yake kallonshi ba koh kiftawa. Baya Garban yayi da kai yana shafa ha6a tare da daga mishi gira,ya dan jima a kame kamin ya d'auke tare da wayance wa. "Wannan bazai sauya komai ba kama ji da wai,dan ban manta abinda ta dirka min ba a baya.. Kama d'aina wata dariya.. Kafad'a Garban ya make,kan yace "Daga baya kenan kuma,chan ta matse ma,dan nasan yau sai kafi kowa farin ciki a garin nan,karyar kawai. Tashi yayi yana daukan Miemie tare da hararar shi, "Kanka ake ji,ni nayi kaga tafiya ta.. Dariya yai kan ya mike dan sauke su, "Kaima an kusa jin naka soon. Harara ya sakar mishi kan suka fice yana ta mishi t'siya. ***** "Mama zan tafi,a min adu'a Allah yasa kar na samu mat'sala kamar yadda principal yace.. "Amin kam, in Allah ya taimaka zasu karbi uzirin.. Kai ta kad'a, ''Amin toh, na tafi kan wannan ta farka. Da sauri ta fice ganin zatai latti. Allah yasota tana zuwa wata Napep zata tashi ta d'au wani da dan sauri ta t'sayar ta shiga ba tare da ta dubi na ciki ba. "Dan Allah ka taimaka school of... Shiru tai jin wani kamshi da ya bigeta,turaren da koh ajikin wani taji,toh mutum daya ke zuwa ranta. A hankali ta waiwaya dan ganin waye masanyin turaren. K'yam tayi tana kallonshi da murmushi ba koh kiftawa, shima hakan take,kan da sauri ya d'auke kai kamar ma bai ganeta ba yake nufi.. Dad'i ne..koh farin ciki a ranta a safiyar yau.. *Ja'afar* Wannan shine yaushe gamo. Kokarin mishi magana take yace da mai Napep ya t'saya. Ba musu yaja ya t'saya, da mamakinta taga yana kokarin sauka a Napep d'in, da sauri mai napep yace "Kazo gaba toh. Ba tare da ya kalle yace "Kai hakuri,bana shiga keke da mata... Gaba yai ya batta baki sake.. Kuturu,wa ya ga turnuku... Ji tai tamkar ta d'aura hannu a ka ta kurma ihu,wai ita Ja'afar zai haka?. By Feenat Ja'afar. 9/29/16, 9:44 AM - Queen Safiyyert馃憫: Feenat Ja'afar Novel's *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 45_Washegari kowa da farin ciki ya tashi kamar ma ance an shirya. Yau tana son ta koma Salmanta ta da ne. Yau shima yana son komawa Ja'afar d'inshi na Salmateen shi,dan haka tun wuri yaje yai g'yaran fuska,ya rage sumar kai,tuni ya hasko kamar zamanin angoncinshi da Salma. Gun Garba yaje yasha kwalliya kamar wani sabon ango. "Ya mutumina nayi kyau kuwa?鈥� banda shakiyanci pls. Daga sama har kasa yake kallonshi,yai kokakarin 6oye dariyar shi. "Kayi man,ina zuwa haka da sanyin yammacin nan haka?.. Da zumudi yace "gun Salmatee hayatee man. Da rashin fahimta yace mishi "wace haka?.. Harara ya sau mishi tare da fad'in "Ban sani ba, kaima ramawa zaka yin?.. Dan Allah ni taso muje.. Kai Garban ya juyar yana fad'in "ba inda zani bansan mace ba, haka kawai, Da zumudi yace "Salma ta fa,kar kace baka gane ba mana mun dinke.. Kunu yasha yace "ban gane ba,yaushe aka dinke?.. Koh ka manta kalamanka?.. Lallami ya fara yana kasa da kai,tuni Garban ya ware yana dillika mishi dariyar mugunta. Shi dai yau bata tashi yake ba,burinshi kawai su isa ga Salman shi. Yau d'aya ta zauna zaman kwalliya duk da bata da tabbas din ganinshi,har Mama na mata t'siyar ina zuwa?. Murmushi kawai tayi ta ciro wani arnan purple swiss tana kallo, shafashi tai tana tunano colorn da Ja'afar yafi kauna ya gani ajikinta. Riga da zani ne single, dinkin yai mata kyau tsam ya kama jikinta, da gaske yau ta fito a Salmanta. Tana daga d'aki ta jiyo yaro yazo wai Salma tazo,tana jin Mama na fad'in inji wa?.. Bataji amsar yaron ba taji Mama tace kace tana zuwa. G'yale ta rufa fari da ratsin flower purple tana k'allon kanta a mudubi,ina ma Ya Ja'afar ne man... "Ki fito ana kiranki a waje Ja'afar yanzu... 6ata rai tayi tana gunguni, "Ja'afar kuma Mama?.. Ni fa ba danshi zan fita ba fa.. Harara ta sakar mata,kan ta juya tana fad'in "magulmaciyar kawai,ni zakiyiwa alaye?.. Da gani shigar Ja'afar daban take gunki ai... Dariya ta kunshe kan ta kara k'allon kanta a madubi ta fita. Suna tsaye sun rike hannun Miemie da suka dakko chan gidan su jaafar suna mata y'ar dage tana dariya. Murmushi ta tsaya yi musu da sallamarta. Ido ya zira mata,yayinda itama take kallon sauyawarshi a yau kadai kamar sabon ango. Murmushi ya sakar mata yana daga mata hannu halamun tayi k'yau, da sauri ta d'auke kai a kallonshi tana cinkune fuska. Kai ya kad'a yana murmushi, karya kuma ai ta kare, tunda har shigarshi an mishi. Ha6a Garba yake shafawa yana kallon wani fulakon karya gun Salma da Ja'afar. "Kaganta ni dai ya kamata nayi fushi bisa abinda ta dibga min,amma kaga an dakeni an hanani kuka... Harara ta sau mishi,kan ta kau da kai, "lefinka ai dayawa,bar tunatune kawai. Kai Garba ya kad'a,kan ya kallo Salman. "Salma.. Kalloshi tai,bata tunani ta ta6a ganin Garba

Table of Contents

Chapters

41 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});