Chapter 14
Chapter 14
"ya sake ki?.. Kai ta k'ada tana dan k'allon Abba da yai shiru yana k'allonta. "Ni dai banji lokacin da ya saken ba kuma.. Ta karasa da dan kukanta. Abban ta d'aure mai kai, chan ya k'allo Ja'afar, "Mey take fad'i ne Ja'afar?... Sam ban gane inda ta dosa ba.. Kai ya kara d'ukrawa,kan ya dago,mama in banda harara ba abinda take sakar mishi. Ya sani da dole su Abba suji. Cikin nut'suwa ya hau zayyanawa Abba halin da Salma ta t'sirar mishi,har zuwa kawo kararta gun Mama, kawo yau da abin ya faru.. Tsananin mamaki Abba kasa cewa komai yayi,wai Salman sa ce da wannan d'anyen aikin? Chan dai ya numfasa tare da fad'in "Innalillahi Wa'ina Ilaihirraji'un... Kuma kin fita d'in Salma?.. Baya ta fara ja tana k'ada kai, "Abba dan Allah kai hakuri,bazan kara ba... Murmushi Abban yai na takaici.. Ya ma rasa mey zai wa Salma ya ji dad'i.. Duka? Kai ya k'ada. "Ni meye nawa? Ba dai kin fanshi fita sama da aurenki ba?.. "Wannan shine sakin Salma... Tunda har kin fice bayan yace *A BAKIN AURENKI*.... Kai ta dago da sauri.. Saki kuma? Daga fad'in hakan?... Kawai sai ta sa musu kuka, "Dan Allah ya Ja'afar kai hakuri, Allah bazan kara ba,Abba kai hakuri... Cikin t'sawa yace "tashi ki bar wajen nan kamin nai miki lilis koh na huce... Kasa motsawa tai,ai da zafin nama Abba yai kanta da takalmi,Mama ta tare, amma duk da haka sai da mummuka mata. Dak'yar Ja'afar ya lallaso shi. "Kin wa kanki toh Salma,dan dole kizo ki bar gidana, wallahi ba zaki k'wanar min ba... "Haba wai Malam dan Allah.. Waye baya kuskure a rayu.... "Kimin shiru kema, dan duk laifinki ne,tunda kinsan irin shegantakar da take aikatawa, amma wai ki kasa sanar ni na d'au mataki.. Jan Salman tai d'aki tana bashi hakuri,dan sai ya iya had'awa da ita. Sai da ya gama sababinshi kamin Ja'afar ya hau bashi hakuri, "InshaAllah bazata kara ba Abba, nima na rasa abin yi ne shi yasa nai hakan.... "Ni fa banga lefinka ba Ja'afar, kamin dai dai.. Gaba nasan bazata kara ba. Shi dai kawai hakuri yake bama Abba. Abba ya tambaye shi kan saki nawa ne? Yace daya. Tashi yai yace ya jira shi,sai yace bari yaje gida shima ya d'au machine sannan ya sanar musu. D'aki Abban ya shiga bayan Ja'afar din ya fita. "Amma kin bani mamaki Allah Rabi... Ashe ba zaki zama mai g'yara wa ba sai dai kiyi shiru? T'sawan lokaci yaro yana hakuri da halin yarinya amma kina sane?... Shiru tai,sai da ya gama chake ta ta hau bashi hakuri. "Ke kuma tun yanzu har har kin kone tun kamin ki tafasa koh Salma?... Kai ta k'ada tana yai hakuri, "A'a, ni ai nawa mai sauki ne,koh dai ki g'yara halin ki,koh ki shiga hannu na... Bansan lokacin da kika sauya k'yak'yawar dabi'ar ki ba Salma?.. Sosai yai mata fad'a cikin zafi zafi kan ya kara da ta shirya,dan ya rantse bazata k'wanar mishi a gida ba... "Haba malam,ina zata toh?... Cikin fad'a yace "gidan mijinta... Koh da magana?.. Kai ta kada,kan tace "sakin fa?.. Sannan wane gida bayan ya kone?... "Eh a konan nan zata zauna akwai daki a waje yace da bai kone ba,sannan ki sani igiya d'aya babu a tsakanin ki da shi. "Ki gode Allah kin samu mai sanki,yau da wani ki kai wa haka sai ya tabbatar da ya miki shegen duka kan ya baki saki... Amma shi kok'ari yayi ma a take yace min ya mayarki. "Abu d'aya zan iya fad'a miki Salma... Wallahi, duk ranar da zaki maimaita haka,ki kuma k'waso kafa ki zo min gida sai na 6a66alla kafarki... Baki sake Mama ke K'allonshi, ita kam yau kad'ai ta kara mugun tsoron Abba,tasan a yadda yau ya daketa tsaf zai iya 6alla tan. By Feenat Ja'afar. Like 路 1 路 Reply 路 Report 路 Jul 29 Feenat Ja'afar Novel's *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 20_Koh da Ja'afar din yazo haka ya kara bashi hakuri kan suka d'au hanya. Zaune take a d'akin da ya rage musu,duk ta dawo kalar tausayi. Waya yake amma yana k'allon yadda ya takure kanta tana K'allonshi. D'anna wayar ya cigaba bayan ya gama, cikin nut'suwa ta hau bashi hakuri, kan Allah bazata kara ba. Sannan bazata kara fita ba izinin shi ba. Shiru yayi,hakan yasa ta fara kuka tana rantsuwa kan haka. Sauka yayi akan 1sittern dake a d'akin ita kad'ai sai karamar katifa da filo daya da ledar t'sakar d'aki. Yasan dan so yana ma Salma,sannan yana matukar ganin darajar Abba cikin idonshi, sannan yana mutunta soyayyar da ta mishi a da chan baya. "Salma kin d'aina so na yanzu sam,shi yasa ki ke ganin damata a yanzu... Ki duba kiga abinda yawan ki ya wanzar mana...nayi imani a garin saurin ki fita ne har kika manta wani abu a k'unne a kitchen... Ki duba irin kinjin magana ta abinda ya jawo... Salma takadduna sun kone kaf...sai guntu, sanin kanki gobe muna da _verification_ da za'a gunar mana. "Ba wanda zan je ma hannu Rabbana ya k'alle ni... Kinga meyiwa na rasa aiki,dan zan shiga _miss call_... Kinga kin zaunar mu... Ba gida ba aiki.. Cikin kuka ta mat'so tana bashi hakuri, "kai hakuri banzan kara ba Allah.. Murmushi yayi kamin ya janyota da sigar lallashi. "Ina sonki Salma,kisa a ranki komai zanyi zanyi ne _for your own good_... Bazan ta6a miki abu dan tuzarci ba... _cos I love you_... Kank'ameshi ta kara cikin jin dad'i... Tabbas tana son mijinta, zata jure komai dan 6acin rana irin wannan. Koh da yazo k'wanciya ita tana gefe yaga bata niyar k'wanciyar tunda ta fito a bayan gidan waje. Daga k'wancen ya mika mata hannu halamar tazo. Har wata kunyarshi ce ta da tazo mata yanzu. Da rarrafe ta isa gareshi,sai ya nuna mata kafad'arshi kamar kullum,nufunshi ta sa kanta. Da murmushi ta g'yara, kan cikin nut'suwa ta zame ta k'wanta. Duk kusan tare suka sau ajiyar zuciya, bata ta6a saba bacci a kafad'ar Ya Ja'afar ba... Haka shima bai ta6a sa6a bacci,ba tare da Salma na hakarkarinshi ba. A daren ta tabbatar mishi da lalle har yanzu tana son nashi,har ma tai kok'arin mantarshi wasu abubuwan. *Hmmm..Allah sa da gaske ne Salma*... *************************** "Haba dai? Yaushe?.. T'salle ta doka lokacin da ta sauke wayar a k'unnenta... "Ya Ja'afar.... Da sauri ya katseta da "Ummi ta haihu... Yana murmushi. Hannunshi ta kamo,sosai tana a farin ciki. "Yaushe zamu ganin baby?.. Murmushi yayi,kan ya k'alli agogo, shida da rabi,harda wasu y'an mintuna. "Yanzu kam dare kinga ya gabato... Gobe da safe kan ma an sallamota sai kije koh?.. Kai ta k'ada tana wani tunani... Jin ya kai hannu cikinshi yasa ta dan murmusa.. Gira ya daga mata,kamin yace "saura mu koh?... Murmushi tai mishi ta k'ada kai. "Mun kusa ai...k'wantar da hankalin ka sarkin son yara... Dariya sukai,kan yace "sosai ina son su kam...in naje yaron Garba kamar nace su bamu aro... Kai ta k'ada, "lalle a gaishe ka.. Ni kam nafi son mu shekara kan na haihu da... Murmushi yai yana kada kai kawai. ~~~~~~~~~~~~~~~~~~ "MashaAllah, ganshi kamar dan larabawa... Ta g'yara mishi hular kanshi... Dagowa tai cikin wasa tana"um um,su Ummi an
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41