Chapter 38
Chapter 38
alakakai koh? Kai ta daga mata tana dariya.. Itama tana dariya ta fara mata chakulkuli su na k'yak'yata dariya har su Abba dake waje suna jiyo su. Mama ya kallo,itama shi take kallo, "kina jin mutananki koh?.. Kamar yau take Sallah.. Murmushi tai tana sadda kai kasa, sai ya girgiza kai yana tuna wani abu. ****** Tun daga wannan lokacin hankalinta ya koma kan makaranta, babban bakin cikinta bai wuce yadda Alhaji yai burus da maganarta ba,a ganinta in har da mutunci koh Abbanta ya samu da zancen.. Gashi a kalla yanzu ta kusa cinye kwanakin iddar ta. Duk suna waya da Maman su Nabila tace yana zuwar musu,sai dai ita baya samun ganinta. "Aunty!.. Aunty!!.. Da dan gudunta ta shigo gidan tana k'wada mata kira rike da leda tana ja,bakin nan har kusan kunnen Miemie. Kamar a mafarki taji kira ana ta6ata,a hankali ta bud'e ido dan bata jima ba da bacci ya debeta sakamakon ciwan period da take. "Uhmm Miemie.. Ya akai?.. Ledar hannunta ta hau bud'e mata tana mata magana duk a hard'e dan murna. Riguna ne y'an kanti masu kyau da tsada da takalma, sai teddy guda biyu da y'ar tsana mai feeder a baki. A zabure ta mike tana duben Miemien,tasan ba mai irin ma wa y'arta tsarabar nan sai Abbanta,yawu ta had'iye kamin tace "Miemie,ina kika samo kaya haka?.. Dagowa tayi kamin tace "Abba ne... Tsam tai tana kallon irin farin cikin da Miemien take,wato in zai shekara bata ganshi ba tasan Abbanta. K'allota tayi tana mata yake ganin yadda take cire feedern a bakin y'ar t'sanar tana fad'in Inya.. Inya. Da sauri ta tashi tare da zarar gyale tai waje. A kalla zataso ganinshi koh dan ganin yadda yake a t'sawan shekara guda da d'auri. Sai dai har ta gama leke bata koh hango mai kamar Ja'afar fa sai sawun mota. Zaure ta koma tana lumshe ido tare da dafe kirjinta. Babu makawa Ja'afar ya shigo zauren nan.. Dan ga nan kamshin turarenshi ciki tana iya shakarshi. Jiki a sanyaye ta juya ta koma cikin gida, a chan d'akin Mama ta jiyo karad'in Miemie na ba ma maman labari tana dariya. Da murmushi ta samu ta dan dosana tana kallonsu kamar ta sa kuka. "Na fuskanci yarinyar nan in dai tai arangma da Abbanta tana kwanan murna, haka kwanaki dak'yar na ban6areta jikinshi ashe bata manta shi ba tana kuka,shima harda y'ar kwalarshi yana daga mata hannu... Ido ta kurawa Maman ba koh kiftawa.. Ba dai Mama na nufin Ja'afar yana zuwa garin nan ba kuma har gidan nan?... Mama ce ta kat'se mata tunani da fad'in "Ban tunanin yaron nan koh a hanya ya ganni zai gaidani ba sam bayan aurenki, duba ga yadda na rika mishi fatattakar arziki.. Zuwan shi biyu gidan nan ashe makaranta ya koma kinji.. Murmushi tai Maman da iyakar shi le6e tare da daga kai. Tuni ta zurfafa tunani,har bata jin mey Mama da Miemie ke fad'a,kan ta farga har idonta ya cika da kwalla,da sauri ta juyar da kai tare da goge wa kamin su gani. Sakkowa tai tana taya Miemie rad'awa teddy suna suna dariya. Kallonsu kawai Mama take tana wani tunani, kai ta kad'a kamin ta tashi ta basu gu dan tasan Abba yana gaf da zuwa. Washegari da yamma tana kokarin shiga wanka akai mata sallama. Hijab ta zira harda shafa powder da zumudin Ja'afar ne ma,kila ya samu labarin tana gida. Turus tayi tare da chunno baki kamar Miemie ganin Alhaji da abokinshi. Baki ya washe mata yana fad'in ta karaso man kusa... Murmushin mugunta tai kan ta kalloshi "Dan bani minti biyar na fito a gida... Kai ya daga yana mata murmushi, ashe bazai yi wahalar shawo kan Salma ba kamar Halima. Ruwan da ta zuba na wanka ta d'auka da wani a buta dan tsarkake kai in tai wankan t'sarki. Tana yi tana murmushi har ta gama. D'aki ta shiga ta tsane kanta da towel kan ta dan shirya a gaggauce ta fita. Yadda take murmushi ne yasa Mama tambayar waye yazo, a tunaninta koh Ja'afar ne,tana cewa Alhaji ne ta 6ata rai. "Ki dai kama kanki ki saiwa kanki mutunci,dan sam mutumin ba nagari bane,kinjini ai? Kai ta kad'a tana murmushi, lalle Mama, yau Alhajin guda?.. Sai ta kad'a kai, "adu'a bata fad'uwa kasa banza. Bayan sun gaisa yake zungurar abokin nashi sarkin iya t'sari, duk tana jinsu tana murmushi dan feleke harda tambayar Miemie,sai da suka gama tass tana jinsu tana kad'a kai. "Ai yanzu na fita sahun matarka Alhaji,sai dai kabi sahun zawarawa na..dan nayi iddah ni... Fuska ya g'imtse yana kallonta, "haba kar muyi haka dake man,ina fa lissafi,yau watanki biyu da kwana uku rabonki da gida na, kinga ai bakiyi wata uku bare ace kinyi iddah koh ba haka ba abokina? Kai ya jijjiga yana fad'in "kwarai kuwa,dan haka muka sani a al'adan ce. Kai ta kad'a tana murmushin takaici, wato ga babyn roba,a hular a lokacin da akaso a d'auka a randa aka ga dama.. 6aro-6aro tai mishi dalla-dalla kan ita ai duk bayan sati uku take period, kuma ya sani sai dai ya take. A fafur yace shi baisan zance ba,kawai ya maida ta dakinta. Juyawa tai ta koma gida,tana ji sai kwad'a mata kira yake tai mishi banza. Da farin ciki ta shiga har baya misaltuwa, dan da yanzu dabarar yin wanka ba tazo mata ba da tuni ansha da ita an gama. "Ba dai ya maidaki ba naga kina murna tun yanzu Salma?.. Yanzu ke bazakiyi kishin kanki ba har kin bada kai daga fita bori ya hau?.. Ina laifin ya samo Abbanki da maganar in dai da mutunci aciki... "Au dariya ma na baki koh Salma?.. Ga shash.. "Mama ni fa ba aure a t'sakanin mu da Alhaji yanzu,dan tau nai iddah ta.... Baki sake take kallonta,dariya tasa ta bata labari,sai ga Mama na tikar dariya. "Lalle yarinyar nan da wayo ki ke,kwarai kinyi dabara, dan sam mutumin ya sane min, dan ban fad'a miki bane,ba'a fi sati da dawowarki gida ba muka had'u da dan talikinnan,d'auke kai yai kamar bai ganni ba fa,bayan sarai mun had'a ido.. "Shi yasa yaron nan Ja'afar nake ganin kimarshi har kullum,dan koh bayan rabuwarku yana daraja mu,musamman zai sa azo har gida abokinshi yai mana goma ta arziki in sun d'au Miemie... Shiru tayi tana sauraran maganar Mama, wai Ja'afar take ma ya6o haka da kirari?.. Farin cikinta a yau bai misaltuwa,ina Miemie na nan ta rad'a mata itama suyi tare,tasan dai duk inda take yanzu tana neman gida,dan tun dazu tai mata kwalliya da kayan Abbanta kaninshi yazo ya d'auke ta. Murmushi tai tana jijjiga kai. Lalle ne *Duniya Labari ce* By Feenat Ja'afar. feenat-jafar.my wapblog.com Feenat Jaafar's Mobile Blog feenat-jafar.mywapblog.com Like 路 2 路 Reply 路 Report 路 Aug 9 Feenat Ja'afar Novel's *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 43_Waya yake d'annawa a nitse yana duba sakon waya kamar bayaso,kamili ne,da hasken shi,sajenshi a yanzu shine sirrin 6oye kyanshi na ainashi, sanye cikin kananan kaya da glass manne a idonshi,da gani yana ji da ajinshi a dai- dai lokacin nan,dan miskili ne yanzu na karfi da yaji. A yanzu ne yake tsone idon y'an mata musamman na jami'a, dan ya iya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41