Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 19

Chapter 19

A Bakin Aurenki Book 1 Complete Hausa Novel – Salma’s Painful Return 1,265 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

hawaye taro a idonta. "Ki gane Salma, ba wai.. "Eh koh A'a?.. Amma nake son ji kawai. Ba koh shakku yace mata "eh.. Amma.. Hannu ta daga mishi tana hawaye, "Barni haka dan Allah,amma kasan Bintu k'awata ce da koh?.. Ya zaka min haka? Kai ya kada harda dariya, "A sani na banta6a ganin Bintu a gidan ki ba,asalima... Sallamar Aunty A'i ce ta kat'se mishi maganarshi,sai ya tashi dan dan bud'e mata kofar,da kallo ta bishi tana mamakin kalamanshi,sai kawai ta k'ada kai ta mike tana goge ido. "Bissmillah mana Auntyn mu.. Yana gaba ta biyoshi a baya, sosai suke dasawa da Aisha,dan tasan abinda take sosai,shi yasa baya 6oye mata komai. Bayan sun gaisa ya mike yana zai fita, kai kawai ta k'ada mishi,sai Aunty A'i ce tai mishi a dawo lafiya. Zama Aunty A'i ta g'yara tana ma Salman k'allon tuhuma. "Ashe Salma baki fara g'yara ba har yanzun?.. Da rashin fahimta ta k'allo ta tana hawaye, "Fita fa yayi jiyan nan dawowarki amma har kin fara nuna mishi baki sauya ba. "Aunty A'i ba abinda na mishi fa Allah.. Katseta tai da fad'in "Amma zai fita babu koh a dawo lafiya?.. Haba Salma,nan ki ka dinga rantsuwar kin shiryu, koh har kin leka makotar ne yau d'akko sabon darasi?.. Kuka ta sa mata tana girgiza kai, "Haba Aunty A'i,k'awata fa zai aura fa,taya bazanji zafinshi ba?.. Da mamaki tace "wacce kawar taki? Cikin kuka tace "Bintu,dalibar shi ce a Day school fa. Ita dai ta hanga bata gano wace Bintu bace a k'awayen,tasan sarai k'awayen Salma basu fi biyu ba wanda tasan su. "Wace Bintu kuma cikin k'awayen naki? Amma basan ta ba koh?.. Kai ta daga mata, "islamiya mukai tare fa.. "Mtsww, t'saki Aunty A'in tai tana k'auda kai, "har wata kawar islamiya K'awa ce?, bana jin ko hanyar gidan ku ta ta6a zuwa balle ta zama kawarki, koh ta halarci bikin ki?.. Kai ta kada mata tana goge hawaye. Cikin lallami ta fara lallashinta. "Kar fa ki bari tun kamin ta shigo taci galaba akanki Salma, yanzu ba lokacin t'sayawa kishi bane a gunki, lokacin g'yaran kuranki na baya ne Salma... Ki d'auka baki ma ta6a sanin wata Bintu ba rayuwa,dan ba gaminki da ita sam. "Ki kuma fidda zancen auren nan a ranki,dan koma meye ke ce sila Salma. Nasiha tai ta mata tana kuka har ta gamsu da bayaninta. Ta bata shawara masu k'yau, ta kuma d'auka. Da ya dawo ya ga chanji,sannan bata kara mishi maganar Bintu ba. Yau satin ta daya da dawo wa,amma banda Maman Abba ba wanda ya leko mata har Maman Ummin, Ga sai wani kama mata kai Ja'afar din yake bare tace zata leka,abu daya ta sani,shine ta daina zuwa gidan kowa sai in ta kama. Washegari har kofa ta rako shi zai fita tace zata leka gidan Maman Ummi.. Yana fita yace mata sai ta dawo kawai. Da k'allo ta bishi,sai ta ga kamar gat'se ya mata,dan haka ta koma ciki tai k'wanciyarta. Mukullin gidan da ake g'yara zai fitar musu dashi sai ya dawo. A k'wance ya sameta ido rufe a parlour,sai yai jim,ganin bata fita ba har ya dawo. "Har kin dawo ne?.. Kai ta girgiza mishi,sai yai d'aki yana tunaninta, haka ta saba mishi kan gaba ta fand'are mishi,shi dai yasan yai alkawarin mud'in ta tambaye shi fita ya d'aina hana ta,yasan duniya makaranta,da sannu zata gane abinda yake gujar mata. Koh da zai fita sai ya kara nanata mata kan taje kawai. Bai jima da fita ba ta fito,tana dan jin hayaniyar su kasa-kasa. Har zatai Sallama sai ta ja ta t'saya jin wata gulmar da suke. "Ai yanzu ya zamarta mai gadinshi, tunda ta dawo ba inda taje tana d'aka,koh duk sururin zai kara auren ne?.. Tana jin Maman Ummi tace "oho mata,ba ita areni muje biki ba,mijina baya fad'a.. Muryar Maman Abba tajiyo tana fad'in ''ni tausayi ma take bani wallahi, ranar chan dana shiga duk ta rame tai baki,kana yaronka da kai an ma saki 2.... Baya tai cikin sanda danjin wani na shirin fitowa. Gida ta koma ta cire hijab tai dabar a kujera, tun yaushe haka take faruwa da ita?.. Ashe ita k'allon mara wayo suke mata acikinsu?.. Kai ta daga sama, lalle ta gane mey Ja'afar yake nufi da mutunci yake nemar mata.. Yau ta gane ashe in an yi gulmar wani da kai yau gobe da kai za'a kafa ai taka. "Allah na gode maka daka sa na ji na kuma gani. Tabbas Ya Ja'afar babban gata yai mata. Toh a ina ma suka samu labarin za ai mata kishiya?..har dare tana neman amsa. Ranar har kukan bakin ciki tai na taraiyarta dasu Maman Ummi. Tuni ta tattare kowa ta wat'sar shi,duk da ba duka aka taru aka zama daya ba. Ranar Maman Waleeda da suke kira uwar tsoron miji ita ta zo mata harda nasiha har gida,matar da koh gidanta sai tai fita ashirin bata leka ba,kuma makociya ta kusa,har misali tai mata da Maman Ummi. "A kaf unguwar nan bana tunanin da matar da take cikin takura irin na Maman Ummi Salma, ke shaida ce,in kinji gidan yai shiru ba koh tarin yaro kasan uban na gida. Sannan in zai shekara ba taje ko'ina ba shine dai dai a wajenshi,duk fita in zatai satar hanya take tasan in ya fita da yamma sai dare,amma a gun kuri tafi kowa iya dadin magana,da ina cikin su,daga baya na gane taraiyyata baza tai dasu ba,sai na zabi zaman gidana ya fiye min alkairi sama da yawan gulma. "Ka'rkara in abu ya faru in leka a tsatssaye in dawo, dan Allah ki iya kafarki Salma,dan zasu kai ki su baro ne kawai. Kai ta k'ada mata, "Na gode Maman Waleeda,Allah bar zumunci,kuma InshaAllah naji bayanin ki,duk da mun kusa tashi a unguwar ma duka InshaAllah. Anan ta sanarta za ai mata kishiya,k'warai ta jajanta mata kan ta kara da y'an shawarwari,tun daga ranar mutunci da Maman Waleeda suke,kusan duk yamma tana turo mata su Waleeda taya fira,har lokacin tashinsu yazo. ***************************** Cikinta yana da wata biyar lokacin auren Ja'afar saura sati. Sam bazaka zata Salma bace, dan tamkar bai dameta ba haka tai a auren. Har ranar Ja'afar yana fad'in wai ta daina sonshi gaba daya,koh kishi bata yi zai kara aure,murmushi kawai ta masa,dan tsaf ta kula da rawar kan da yake k'wana biyu. "Ba k'ya shirye-shiyen komai gashi lokaci ya taho fa... Tamkar ya choka mata abu makogwaro taji wani iri,kawai sai ta sa mishi ido tana k'allo. Tabbas rawar kan Ja'afar karuwa take akan auran nan,banda haka wani irin tambaya ce wannan?... Shikam tunani yake yadda Salman ta g'yaru har kullum,a ganinahi halin ko'in kula da yake nuna mata ne akan fita. "In da hali zan fita kar6o wasu kayana unguwar Ummi. Kafad'a ya daga mata,kan yace "sai kin dawo... Yai waje. Baki sake ta bishi,tun bayan dawowarta ta kasa gane inda Ja'afar ya dosa,abu yake mata tamkar ya kosa da zaman ta a gidan. Gashi tun kamin amarya ta tare har ya sallamata,wai ko'ina nan gaba in zata kawai taje,dan yanzu bai son 6acin rana irinta da. Toh mey yake nufi? By Feenat Ja'afar. 9/29/16, 9:11 AM - Queen Safiyyert馃憫: *A

Table of Contents

Chapters

41 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});