Chapter 12
Chapter 12
yi sai ke kad'ai ce bakki shi?.. Salma ki nemi mutuncinki da hannunki,a ganina zai fi mu.... "Ka ga malam,ba sai ka zage ni ba zan san dama kana kule dani ba,daga fita nan da nan din shine har zaka na cemin wata gantalalliya?... Haka kawai,in ma kayan ne naga kai zan sawa ba wani ba,toh meye abin zafi aciki?. Kai ya k'ada kan yace "babu... Amma wallahi kar gobe ki sake ki kara fita gun wata mai gumama,in ba haka ba zan mugun sa6a miki... Waje yai rai 6ace, "Ja'afar?... Ni zaka sa6awa?... Chak! Ya t'saya ya kasa gaba, a hankali ya juyo fuskarshi d'auke da mamaki. "Salma... Yau ni kike kama sunana garangatsai ba koh rufi?... K'ugu ta rike tana girgiza, "ai sunan ka ne naga.. Kuma muna kama sunan Allah ma bare wani chan... Na gaji ne da hancini. Kai ya k'ada yana murmushi, tabbas ba abinda yai saura da gantalin Salma bai gur6ata ba,ciki kuwa harda iya fit'sara. Sai ya k'ada kai ya fice,dan yasan komai zai iya faruwa in ya tanka. ~~~~~~ Washegari haka aka tashi kowa rai ba dad'i, yau ce ranar farko da har aka waye gari ba'a shirya ba. Ga yau week end,yana gida yaki fita shago. Har yamma ba bayani, sai dai yai bacci,ya je masallaci ya dawo. A sama take,dan gani take da gayya yaki fita dan ai ba ita gidan gumama. Ya dawo daga masallacin la'asar ya shiga wanka. Maman Ummi ta turo tazo suje kan a za6e,yana jin lokacin da tace dan aiken yace tana zuwa. Yazo fita ta biyo shi,dan tambaya a ganinta ta wanke lefin jiya ya barta. "Ya Ja'afar zamu gidan wannan mai kayan Maman Ummi na jirana. Ja yai ya t'saya, kan ya juyo ya koma parlour,ba musu ta bishi ai wacce za ai. "Tun jiya ai mun gama magana dake,babu fita... "A gaskiya sai na je, gashi nan ai kai ka ke jawo komai, da lallami na tambaya ba zaka barni ba,sai na fita cibi ya zama kari... Haka kurum yanzu haka jirana ake ka ce wani bazani ba..ta karasa tana kunkuni. "Sai kinje koh?.. Cikin fusata tace "eh.. Murmushi yai ya k'ada kai, "Bazan hanaki ba toh, sai dai wallahi ki sani, mud'in kika sa kafa kika fita,toh *A BAK'IN AURENKI*.... Bai jira komai ba yai waje,yana jiyota tana ai wallahi bazaka sani kaffara ba,fita kam nayi na gama. By Feenat Ja'afar. 庐NWA. Like 路 6 路 Reply 路 Report 路 Jul 25 Ummu Maryam Tahir Sannu da qoqari 6ter Like 路 Reply 路 Report 路 Jul 25 Kareema Wakeeli Tnx Like 路 Reply 路 Report 路 Jul 25 Feenat Ja'afar Novel's *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 18 _Kitchen_ kawai ta leka,ta d'aura guntun ruwa a tukunyar silver a _hot plate_ nata karama nepa suka d'auke wuta. Kamar zata kashe,kawai ta bari,a ganinta ba komai. Kan su kai gidan gumama kuwa 5 tayi,fatansu Allah sa ba'a za6e ba. Kaya kam gasu masu k'yau, tuni ta fara daddagawa tana ware na wara. "NEPA"... Cewar yaran gidan, sai dai da halamun su Salma hankali yayi kan gumama. Suna nan a gidan har kusan k'arfe 6,amma basu gama da mai kaya ba. Kamar ance daga kai sama,sai ga nan dan hayaki na yin sama halamar daga nesa ana gobara a wani gu. "Ina ga wutar dazu tai ma wasu aiki,hayakin nan gobara ce duk yadda akayi.. Kai Salma ta k'ada, "koh taya ake konawa ba... Sai dai kan su farga ihun gobara har kusan layin da suke. Maman Ummi tace suzo su je,in yaso daga baya sa dawo suyi bayanin. Da sauri Salma ta tare, "A'a Manan Ummi,nasan yanzu Ya Ja'afar na hanya 6 saura. "Muje dai koh gobe tunda ta kirga wanda muka d'auka ma dawo ai sabon lissa... "Umma!..Umma!!... Da gudu yaron mai gumama ya shigo, matar tace "lafiya irin wannan gudu? Ince dai ba daga gun gobarar ka ke ba? Yana haki yace "a gidan Aunty Salma ne fa Umma.. Ana ta neman inda za'a shiga a k'ulle, yanzu aka kira Malam Jaaf... "Na shiga uku... Ni Salman koh wa?.. Kai yaron ya daga,ai ina,da gudu ta fice ta wat'sar da kayan a nan ta bar Maman Ummi da kira. Kamar wata sabuwar kamu haka ta iso wajen,kofar gidan cike da jama'a wasu na kok'arin sanya t'sani su haura. A ka ta d'aura hannayenta d'uk biyun,tama rasa ihu zata kurma koh kuka. Baban Ummi ne yace ina mukullin gidan?.. Nan ta fara tunanin mukulli?.. Innalillahi, ta barshi shima gidan gumama... Baya ta fara yi ganin Ja'afar da Garba sun faka mota a chan gefe, a gigice suka karaso, "Innalillahi Wa'ina Ilaihirraji'un"... Itace kalmar da Jaafar ya iya fad'i. Ina kan ta farga sai ga hawaye na zuba tana girgiza mishi kai,mukulli Garba ya tambaya, kan cikin azama ya lalubo a aljihu ya bashi. Salman ya k'allo cikin tausayin kanshi, har yanzu hannu na ka tana k'ada kai tana kuka. "Shikenan kin zaunar mu Salma... Burin ki ya cika sai ki zuba ruwa a kasa ki sha.... Tuni ta kara fashewa da kuka. Fad'in "A kashe meter... Ne yasa yai cikin gidan da sauri. Ba ka ganin koh ina sai dusu-dusu dan hayaki. Da taimakon Maman Ummi ta bar kofar suka shiga daga cikin gida. Sai dai har yanzu kuka take baji ba gani. Yau tasan ta kad'e har ganyenta. Motar kashe wuta ce ta iso,da taimakon dak'yar wuta ta mutu. Ilahirin kitchen da bedroom ya kone ya laso parlour ta silin Allah ya t'sayarta. Fito wa tai bayan taji komai ya dan lafa ta leka gidan,sai ga nan Ja'afar din sun fito rike da barbadin _documents_ nasa a hannu. Kamar munafuka ta dan ra6a ta shigo kai duk'e tana jan hanci. Sai da yazo dai dai ita ya t'saya. Kanta kasa tana sharar hawaye,a hankali ya saki burbudin takaddun ya fice jiki duk yayi sanyi. **************************** Zaune suke a bak'in masallaci shi da Garba bayan komai ya lafa yana tausarshi,yan unguwa sai jajanta mishi suke suna tafiya. "Dan Allah ka'r ka ce zaka d'au mummunan mataki akan Salma, kai hakuri,ubangiji ya mayar ma da alkairin da ka rasa. Shiru Ja'afar d'in yai,zuciyar shi sai tafasa take,dan ma yana ta kok'arin neman kariya daga zugar shedan. Zuwa chan dai ya nesa, "Babban ni takaici na Garba Takaddu na ne,tun jiya ake _verification_ gobe ne namu,ni bana ta Salma,dan a bakin aurenta ta fita... "Ni ga nan d'akin waje zan iya maleji. Kafad'arshi Garban ya dafa,lalle kowa da jarabawar shi a rayuwa,shi kuma abokinshi ta mata Allah ya bashi. "Yanzu toh ya za ai?... Murmushi Ja'afar d'in yai wanda yafi kuka ciwo... "Ya k'wa zanyi Garba?.. Kana sane da gamnatin nan tamu, wa zai k'ar6i uziri na gobe?.. Shiru yai mishi,dan tabbas yasan bai da abin fad'a ma abokin. Gida suka koma,tana nan inda suka barta a durkushe ta tasa takaddun a gaba tana shesshekar kuka. Ja yai ya t'saya yana k'allonta, muryar ta har ta dashe. Abin haushi wai kuma zuciyarshi ta fara tausayinta. Da sauri ya d'auke kai daga k'allonta dan jin zuciya na ingiza shi yaje ya lallaso ta, Salma ce fa... Dake wa yai ya daure tukun yace "toh meye ne na kuka kuma Salma?..ki tashi kawai kije gida
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41