Chapter 29
Chapter 29
ba abin a 6oye bane koh da za'a nemi sulhu,saki ya cike na uku abin yafi karfin zama anan Ayush.. Zamu tafi da Salman kai Ja'afar sai ku taho da abokin ka. Har kusan goman dare ana abu daya akan zancen saki. "Ka ce kayi saki,ita tace ya zama uku, sannan kana zancen ai sulhu koh? Kai ya daga da sauri, murmushi Abban yayi,abin yaso ma bashi dariya, "Wato Ja'afar... "Malam Umar wannan zancen ba zancen da za'ai wa sakwakwa bane,kan Ja'afar ya dawo. "Kai kuma in dan baka tashi mun wuce ba zan mugun sa6a maka yanzun nan.. "Kana hauka ne?.. A wane garin ka ta6a jin anyi saki d'ai daya har uku kuma ana neman sulhu?.. "Ai baka fara ganin komai ba Ja'afar, ba dai zuciya ba?.. Za ta sa ka dana sani, "Malam Umar ai hakuri bisa wannan K'ADDARAR da ta sakko mana,zamani ne yanzu muke ciki da yara basu dauki saki a bakin komai ba.. Tashi yayi yana bawa Abban Salman hannu,kan ya kallo Ja'afar,har yanzu sautin kukan su ke fita shi da Salman. "Muje koh?.. Salma ya dago ya kalla da sunkuyar da kai, "Salma dan Allah ki basu hakuri kar su rabamu,kin san bazan iya rayuwa ba ke ba,Abadan Salma...Please. Kuka ta kara saka mai karfi, t'saki Abba yayi ya karkade riga yana nuno shi cikin fad'a. "Hauka kenan wannan, dan koh a musulunce Salma ta haramta a gare ka..ta haramta har abada,dan kai kam ka nuna mana bazaka ta6a iya rike aure ba, saki tamkar wasan yara? Itama waccan wai ka mata saki uku?.. Toh koh aure Salma tayi na fad'a maka ta haramta a gare ka har abada,kaje kaci zuciya. Da gudu Salman ta tashi tai d'aki tana kuka.. "Haba Alhaji, abin bai kai haka ba,kuskure ne kowa yana iya tafkawa a rayuwa.. Anji bai k'yauta ba,amma kar hakan yasa kai mishi baki,kai hakuri. "Hakuri shine ya biyo ni yanzun nan.. Wace iriyar haukace wannan kamar a jahiliya?.. Wani yai mishi sakin?.. Haka Ja'afar naji na gani yai waje yana waiwayen dakin da Salma ta shige yana hawaye. Tun daga ranar duk suka zama sakwa- sakwa, barin Ja'afar da baida kuzari,ga Abba ya sako shi gaba ta ko'ina.. Dan har gida iyaye Bintu suka zo sukai ma Abba rashin k'yauta wa akan yadda bayan saki uku sai da aka kumburawa ya'rsu fuska,harda ikirarin koto,dak'yar aka basu hakuri kan suka debe kayanta, ranar Abba yayi takaici har yaji ina ma da ya barma Umman shi Ja'afar,kila da baici karo da bacin ranshi ba. Sai dai yace kayan Salma koh sama da kasa zasu had'e ba mai diba, ashe ma in ya bari aka diba sun rabun kenan... Ja'afar mat'sala. Anyi ban baki, Abba yayi fad'an ya dawo lallashin amma Ja'afar ba sauki,kawai sai Abban Salma yace a rabu dashi,dole in ta tashi aure zai bari a diba da kanshi. Kullum ta Allah yana kan jelar gidan su Salma,a wata guda har kama ya sauya,ba aski,ba g'yaran fuska,ya zama tamkar zararre. Sosai Abba yake tausaya mishi,Mama kadai ke shafawa idonta toka ta hana ya ga Salman,sai dai a bashi Miemie, haka zai gaji har ya tafi,sai dai tai ta ganin text na ban hakuri,gobe ma zuciya zai dawo. *************** *************** Rayuwa irin ta kunci kam sun ganta a wata hudu da ta gabata. Salma ta saduda sosai akan Ja'afar,dan har yanzu shi yana kan bakar shi. Sam in ka ga Salma ta sauya,ta dawo shiru shiru sosai,kullum zaka same ta a daki,koh ta dukufa tunani, koh tana k'allon Miemie tana hawaye. "Salma... Gefe tayi da sauri da kanta tana goge hawayen jin maganar Mama akanta. Dole yau ta kawo karshen matsalar nan. Zama tayi a gefen gadon tana kare mata kallo. "Rayuwa fa kullum sauyi take Salma,amma banda taku, ni dai ban ta6a cin karo da kulafucin D'a namiji irin naki ba, wata hudu ba kwana hudu bane Salma.. "Lokaci yayi da za ki cigaba da rayuwarki ki manta da kashin Ja'afar.. Ki d'auka Rabon Miemie kawai ya had'a ku,ki manta da rayuwar da,dan ta wuce,ki fuskanci zahiri a rayuwar gaba Salma.. Fad'a Mama ke ta mata tana kuka, taya zata mance Ja'afar?.. Taya zata mance zaman su?..Soyayyar ta da Ja'afar had'i ne na Allah a ganinta ba wai wani rabon Miemie ba... In har Ja'afar na bata haushi bai wuce yadda ya dankara mata saki ba ba ji ba gani,amma bacin hakan,tabbas bata da sama da Ja'afar a zuciyarta kawo iyanzu.. "Nasan da kin gama iddar ki sarai... Da sauri ta k'allo Mama da t'sananin mamaki, kai Maman ta kad'a mata. "Tunda ki ka zo gidan nan ina fuskance dake Salma,kin gama iddah tun wata uku da suka wuce. Kasa tai da kai tana goge hawaye,tasan Mama gaskiya ta fad'a, dan shayarwa bai hanata period ba.. "Nasan ma hakan ne Salma,yanzu abinda nake so dake shine, "Dole ki fara fita,dan saki ba takaba bace, bazai yu kiyi ta zama a gida ba kamar matar kulle,tun yanzu zaki fara fuskantar cigaban rayuwa,bana son musu koh taurin kai Salma a zuwan nan daga gunki, dole komai nace kiyi kiyi, kina jina koh?. Shikenan kuma,ta faru ta kare,wai an ma mai dami daya sata.. Shikenan ta shiga sahu,yanzu sai jiran bazawari.. Kuka ta sa mai sauti,yi take ba kakkautawa,har ta kular da Mama ta bar lallashi ta hau sababi. Dole kam in dai ta yadda da K'ADDARA ta maida komai ba komai bane.. Dole ta daina yaudarar zuciyarta,tana biya zancen Ja'afar a kullum akan tashi ce shi kad'ai.. Hannu tasa ta share hawayenta,kan ta g'yara zama. "Na shirya bin umarnin ki Mama matukar bai sa6a shari'a ba.. Baki Maman ta washe, "Koh ke fa,yanzu naji batu,ko ke fa Salma. Kasa tai da kai tana murmushi, sosai taga farin cikin Mama. Washegari da dare bayan Abba ya dawo taje gunshi suna zaune da Mama,yai mamakin sauyawarta faradd daya,shima sai murmushi yake mata. "Abba.. Zama ya g'yara da murmushi ya amsa. "Abba makaranta nake son shiga dama... Da sauri Mama ta kallota, ji zata kwafsa musu kuma,wai makaranta? Baki ya washe dan murna. "Toh Salma,kinyi tunani mai k'yau, Allah yasa a shiga a sa'a. Kai kasa tace "Amin Abba... "Anjima ina son zan k'waso akwatina na a gidan Abban Miemie koh da y'ar makota ne.. Kai ya kad'a mata "A'a,ki bari zan ma shi Ja'afar din magana zai kawo miki har gida. Sosai sukai fira Mama na jinsu bata ce kala ba,tana shiga d'aki Maman ta bita. "Ya zaki min haka Salma?.. Wace makaranta kuma ana zaune lafiya?.. Shiru tai sai da ta gama kan tace ba abinda karatunta zai tsare mata,tai hakuri tasan zai mantar ta wasu abubuwan. Ba dan taso ba ta yarda. Ta gama da Mama, saura Ja'afar. By Feenat Ja'afar. 9/29/16, 9:25 AM - Queen Safiyyert馃憫: A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 33_Washegari Abba da kanshi ya samu Jafar din a shago,duk da yai jim,daga baya ya tuna da wannan ne damarshi na ganin Salma a yau dan tuna mata da alkawarin shi. Da yamma k'wa yasa Garba ya k'waso mata akwatinan ta da sauran sabbin kayanta marar dinki. Da sallama ya shigo gidan, ya k'wa taka babbar sa'a Mama bata nan. T'saye yayi ganin Salman t'saye a gaban famfo Miemie na mata kukan
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41